← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 139

Sashe 58

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau dagani har Amal da mama su Umar agidan maman salimat mukayi ni don tayata aikin taron mijinta da zai kawo mata ziyara daga nageria
Saida mukaga komai yayi tsab mukayi mata sallama muka bar
Lokacin da muka iso namu gidan sai muka tarar da baki
Sheriff ne tare da wata mata fara sol da ita, saida bata da tsayi don ina iya cewa gajera ce,
Da murnan mu muka tare shi, wanda yaji dadin hakan har cikin ranshi,
Nice ma na kula da matar wace ke zaune gefe tana wani shan kamshi,
Nagaisheta nai mata sannu da zuwa, a yatsine ta ansa min,
Azuciya na nace taupa abin jiya yadawo ke nan,
Amal ma a gadarance tace mata sannu,
Wanda hakan ya nuna sheriff baiji dadin hakan ba shima,
Maman Umar takawo masu dan abin sha tana tambayar su komay za,a dafa masu,
Da hannu ta nuna adauke abin shan kamar wace aka aje ma kashi agabanta tace ita bazataci komai, ba sai sunje hotel,
A hankali na duka zaukwashe kayan sai sheriff yai min ahannu alamar indakata da shi,
A hankali yazuba lemon stwberry, a cup din wanda yai sanyi sosai sanan ya jawo wani dan gutun snack ya na ci,
Bansan lokacin da nai ajiyan zuciya ba wacce har takai mai akunen shi
Da sauri yadan kalloni yana mamakin ajiyar zuciyar nawa,
Wanda dama mamakin yadda yaga nakoma yakeyi , don a kulun yagani sai yaga na kara wani irin girma,
Hira sukeyi da salim inda na dan tashi a hankali na koma kan kujerar dake falon gefe guda na zauna
Saidai daga inda suke muna jin hirar komai, niko irin kallon da matar ke min ne yasani komawa gefe na zauna,
Don ina zaton ta san cewa ni yar aiki ce kuma gani ina watayawa kamar kowa,
Wayana ne yadauki tsuwa alamar kira ya shigo ,
Duk wanda ke falon saida yadan kalleni alkarayi ,,,,
Dan basarwa nayi har kiran ya katse, ido sheriff yadan zubo min ganin kiran ya katse ne yasa shi dan kauda kai
Kiran nawa aka karayi cikin rashin damuwa nadauki kiran tare da dan yin murmushi a fuska na
Bandamu da barin wurin ba don nasan babu mai jina a inda nake kuma nai tsabar keantar da muryana bamai jin abinda zan fada,
Bayan mun gaisai sanan na tambaye shi ya aiki, yace ba wani nadai gane inbani nakiraki ba watau ke baki iya kirana fadima,
A hankali nace natuba zan fara kiran,
Abin mamaki dariya naji ya kwashe dashi, sai nadan yi murmushi nima daga inda nake,
Sai yafara magana da dan saurisauri yake ce min jirgi zai shiga shine ya bugo min don muyi sallama zaije wani akine a paris,
Sau biyu muna hada ido da sherrif yayin da nake wayan, sai nadauke kaina daga gefen su nacigaba da wayana ,,
A hankali naimai fatan alheri tare da Allah tasa
adawo lafiya ina mai yin murmushi cikin kashe murya na,,,
Daidai lokacin da nakashe wayan nawa ne muka ido hudu da sheriff din mu wanda yazubo min idon shi da suka dan sauya daga fara,a zuwa fushi,
Sai naga ashe kusan kowa dake falon ni yake kallo ban sani ba
Mikewa nayi abina nawuce wurin maman Umar a kitchen,
Tundaga wanan lokacin sai hiran nasu yadan rage karfi sosai,
Nasamu ta hada masu abincin labawa mai saikin dahuwa ga dadi,
Najera a tire nadauko nakai masu har gaban su na aje,
Ina cewa ga abinci nan nasan zaku iya cin shi don ba mai nauyi ne ba,
Sai alokacin yadan sake fuska kadan yai ma matar da ko sunan ta bai gabatar muna ba balle yace muna ai matar shi ce,
Abincin suke ci hankali kwance har da ita matar sai salim da ke taya su cin abincin,
Amal tace wai yaya bakuwa ce kayi don bamu santa ba, kuma na ganku atare,
Yanajin dadin zama da kan nen shi sosai don yana son su saboda sune mafi kusanci da shi fiye da kowa,
Murmushi yayi kadan ya kalli salim tace baka fada mata tayi sabon anty bace,
Saida Amal ta dan kalli matar tace to, nida ke gefe ina kokarin jona tv na juyo da sauri ina fadin masha Allah,
Gaskiya munyi farin ciki kuma muna mata sannu da zuwa da fatan zaki kula muna da dan uwa fiye da komai a rayuwan ki,
Koba komai tadanji dadin hakan don tasan nafi Amal dama tunda har nai mata fatan alheri,
Sundan kai wani lokaci a tare da mu anata hira tsakanin shi da yan uwan shi,
Inda aziza ta fahinci cewa yana son yan uwan shi sosai saboda bataga abinda yake ba muhin manci ba kamar su,
Don ta kula ko awaya yake magana dasu zaidade suna hira yana nuna jindadin shi,
Saidai tasan cewa bata sami karbuwa ga Amal ba sam
Shakata guda ne ni saboda tace niba yar uwsn shi bace ta jini amma yada yake kula dani yana daure mata kai so sai,
Wayana yakara tsuwar kira again,
Wanan karon salimat ce ke kirana tana fada min mijin ta ya iso ko
Bansan lokacin da nadayi dan ihu murna ba nace mata tai mashi sannu da zuwa ,
Nan nake fada mata nace mata ai yayan mu yazo da amaryan shi mai kyau da ita,
Wanan magana yaiwa Aziza da sherrif dadi don na fahinci cewa yana son aziza sosai,
Nikuma duk abinda yake so ina son shi don yawan kaunar da ya nuna min tun farko,
Da murna nake fada ma Amal sakon salimat Amal din tayi dan dariya tace ashe yau anty amarya ce,
Basu wani dadewa ba sukai muna sallama zuwa masaukin su,

Acikin barci naji tsuwar waya na kamar kada in tashi sai dai nadaure na ansa kiran ,
Amma abin mamaki mai kiran ya boye nobar shi,
A cikin harshen turanci mai shi ke min magana,
Dafarko yace min sorry da damuna da yayi ina barci na,,
Sai na ce ba komai amma dan Allah dawa nake magana ne,
Shiru ne yadan biyo baya, jin danayi ba ansa yasa nace ma maikiran kada ya kara kirana ni matar aure ce ,
Idan yakara zan fada ma mijina,
Dan murmushi yayi yace good ina iya infada ma mijin nawa,
Ganin da nayi zai jani da dogon zance yasani kashe wayar gami da tsaki, nagyara kwancina,

Anashi bangaren jinda yayi nace zan fada ma mijina yasa shi dagaba yace kai wanan yarinyar,
Tashi yayi tsab yakoma cikin bedroom inda Aziza ke kwance tana jiran shigowar shi,
Ce mata yayi baki yi barci bane, saitace mai a,a,
Yana shirin kwancine ta jeho mai tambaya ,, dayasa shi yin tsit,
Tace mai wai Ahmad ya kuke da wanan yariyar fadima ne,
Batare da shakkunta ba ko jin wani dar yace mata yar uwatace itama,
Tace mai maman ku guda ne da ita din ma,
Atakaice yace mata aa, yar uwata ce kawai,
Saida tanisa sai ta dan juyo setin shi tace mai ke nan akwai aure a tsakanin ko ko,
Cikin firgita da jin kalminta yasa shi saurin waigo ta da karfi yace baki da hankali, aziza,
Sister dinace fa sai tace and so what,
Kallonta yakama yi a kufule,
Ita ko kodar bataji ba, irin halin nan na kasaitatun mata,
Daga haka baikara cemata komai ba ya kwanta zuciyar fam da wasiwasin,
Tunda safe muka hada masu break fast din su tsab ,
Amal takira shi tace mai ko salim ya kawo masu abincin su inda suke ne sai yace mai aa kawai sujirashi gayan zuwa suci tare,
Kowa ya zauna a table din don cin abincin sai ni kadaice ban zo ba,
Salim yace yafada min suna jirana,,,,
Salim na fada min duk saina rude don gaskiya ban taba cin abinci agaban shi ba,
Table din nazo na zauna kowa na cin abinci niko sai wasa da cibi dake hannu kawai nakeyi,
Aziza ta kalli sheriff takali fadima tace man kici abinci mana yar uwa
Dan murmushi nayi nadan dibi ruwan chayi dake gaba nadan kurba kadan sai naji gaskiya ban iya sake jikina a gaban shi hakan,inci abinci,,,
Tana kallon shi taga ya ture kayan abinci ya mike ya ce mata zai je yadawo ta zauna nan ta jirashi zai je yadawo,
Ido tabishi da shi don mamaki tabas akwai wani dan feeling da sheriff ke boye wanan yariyar amma koma dai maye zata bincika,,
Ga mamakin ta sai kuma taga yanafita nafara cin abincina nomal kaman bani bace nakasa ci dazun,,,,

🐎ZEEE MAKAWA
✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣0⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Ya Allah ka azurta muna dukkan Aluman Mususllumi da lafiya, arziki ilimi mai amfani a rayuwar duniya da lahira,
Jinjina da fatan alheri gare ku masoya na asali yan huguma groups gabadayan ku ina kara maku fatan alheri,
Banta mantawa da ku yan uwa na asali ,Anty,Hafsat yusuf, Anty,Mariya SB, Mama farida ,Anty Safiya mai huguma, Maman Rufaida, daduk wani wanda ya cancanci in rubuta sunan shi ban rubuta ba, nagode, nagode, nagode maku kwarai da karfin gwiwar da kuka bani, tun farko har yau gani ga shafi na sitin daidai cikin hikimar ubangiji,,,,,👏👏👏👏👏

Almost true life story ,,,,
Chapter 58 · 0% Book details