← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 139

Sashe 67

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saura kusan shekara guda yarage min inkare karatuna, don haka ba bu kama hannu yaro, babban burina shine nagama da sakamako mai kyau
Danagama in wuce Nigeria wurin yan uwana da iyayye na ,
Don babu ranan da ban tunawa da inna a cikin rayuwata,
Karatun sai yazamamin biyu saboda salimat cikin ta ya tsufa sosai yai mata wani irin girma kamar cikin ta gwaye,
Duk zaman da takeyi agidan mu bata taba haduwa da sheriff ba sai yau , koda ya iso itace zaune dirsha afalon mu duk da sanyin A C dake ta aiki a falon ita sai zufa takeyi,
Duk kan mu munfito muna mai sannu da zuwa yazauna yana kokarin cire sock din dake kafar shi,
Drinks nahado mai a ture na zo na aje mai gap da shi,
Wani irin kamshi da sanyin A C suka hade suka canja launin shakar mutum
Yadda naji nashi kamshin shima haka yaji nawa kamshin cikin kasala ya dan kara dukowa yadauki cup da niyar zai zuba ma kanshi sai hannu mu suka hade wuri guda da sauri naga yaje hannu shi yana fadin
Subbahanallah, cikin lunshe idon shi duk wanda ke falon saida yadan waigo mu,
Na tsiyaya mai ahankali yakarba tare da fadin Shukuran,,,
Sock din kafan shi da yacire don ya dan sha iska na duka gefe ina tsincewa, mangashin da nai gyaran kaina na dashi ya kara shaka,
Tun lokacin yadan ritse idon shi cup din drink rike a hannun shi,
Salimat ce tayi kokarin tashi daga inda take zaune sai ta kasa dariyan da yaji na Amal yasashi dan bude idon shi daga zurfin tunanen da yashiga,
Abu kamar wasa sai salimat takasa cire kafar ta ga sheriff a falon duk mun rasa dabaran da zamuyi don ta samu ta tashi don tashi da kyat takeyi,
Dan tabur din da ke gaban sheriff nainiyar indan tura dakafa idan yaga haka zai maida hankalinshi ga tebur din har salimat tasamu ta daga don naga kunya take ji,
Sainai rashin sa,a nafada dani da tebur din duk saman jikin sheriff wanda ke zaune yana waya,
Ji kawai yayi nafado mai a jikin shi babu shiri gaba daya na,
Wani irin yarrrrrr gaba dayan mu muka, naso in mike sai dan kune na ya lake mai a aljihun rigar cort din shi tagaba,
Duk kamshi kaina yana shaka a hanncin shi,
Wanan karon bai samu kiran subbahanallah din ba
Rikeni ya dan yi gam ajikin shi yadda har muna iya jin hucin junan mu, yasa hannu shi guda yazagaye ni dashi, a hankali ya cire dan kunin a jikin rigan shi,,,
Duk wanan abin rabin Idon shi a lunshe yake,
Salimat har tasamu tadaga ,
ni ba,a sake ni ba,
Sai can yadan sakeni a hankali yace min are u, ok,
Kai kawai na iya kada mai tare da mikewa tsaye cikin sauri,
hannun shi na rike da ni har saida yaga na mike da kyau , ya sake ni a hankali,
Sai yace min b/careful
Daga haka sai, yamike zubur yadauki wayan shi dake saman hannun kujera yayi hanyar waje,
Alokacin ita kuma, Amal tasa min wani irin mugun dariya tace min daga zuwa taimakon salimat gashi nan natashi jin ciwo,
Inbadon a jikin yayan su nafada ba da tabur din yajin man ciwo abanza,,,
Duk maganan da takeyi ban fahintan ta saboda wani abu da na,ke jin yana , min yawo ahankali cikin jikina har kwakwalwana ,
Abinda bantaba sanin ana,jin shi a rayuwa ba yau shi ne naji ga jikin sheriff din,
Har takaraci dariyan ta tagama ban ce mata uffan ba
Saboda weak din da jikina yai min,

Yanafita waje cikin mota yashiga da niyar ya bar gidan ko yasamu dan relief a zuciyan shi,
Don tunda yake bai taba jin irin wanan yanayi ba,
Don dai da shi yadauka cewa duk mata iri daya ne ba banbanci,
Ama yau yafara shedawa cewa akwai banbanci sosai a tsakanin mata,
Shi bai tada motar ba kuma shi bai fito ba,
Ahaka salim yazo yasa may shi zuwan salim din ne har yadan yi kokarin saita kanshi,
Suka fita cikin gari da salim din, dole badon yaso ba yau salim din ne mai jansu a mota,
Don shi jin shi yakeyi kamar duk an zare mai lakkan jikin shi gabadaya
Barci daine barawo har ya iya dauka na don da na rintse idon abinda yafaru nida sheriff nake gani,
Duk na rasa sukuni sai juyi nakeyi kamar wacce, ake muntsula, ajiki
Da haka har barci ya sace ni cikin wanan yanayin,
Washegari tunda safe natashi nafada kitchen don in hadawa sheriff abin karin kumallo don idan yana garin ko in munje hutu makkah nice mai yi mai duk wani hidimar da ta shafe shi,
Don kowani yayi mai yakama korafi ke nan kamar zai tashi sama,
Amal bata so sam tasa hannu ga duk wani abinda yashafi aikin sheriff din,
Don gudun korafin shi,
Nasan cewa yanayin aikin su na madina tunda safe suke fita su dawo zuwa karfe dayan rana,
Shiyasa nake tashi da wuri in mai break fast,
Ina gamawa na fada dakin mu don indan watsa ruwa a jikina,
Salimat ce na iske cikin wani irin yanayi, naban tausayi,
Gurin da take na nufa cikin sarsarfa, tana kasa kusa da hanyar shiga bayin mu
Ta dan zauna tayi dai,dai da ita tana maida nunfashi guda guda,
Dasuri nakarasa gurin ta ina mata sannu,
Kai kawai tadan daga min alamar ansawa ta na cizon bakin ta da kyat sai gumi dake ta zubu mata kamar an,tsa mata ruwa,
Duk sai na firgice na duka saitin ta ina mata sannu,
Tace min cikin karfin hali fadima kila haihuwa zan yi,
Ido waje nace mata what cikin karfin hali ta daga min kai,
Nace to barin kira maman umar tazo muje asibiti ko,
Har nakai kofa sai naji tayi wani irin nishi gami da salati mai karfi,
Aida sauri nayo kanta ina fadin sannu salimat
Wanan karon bata karba min ba ido kawai ta zuba min duk sun firfito waje,
Sai naga tafar wani irin nishi makarfi
Da sauri na rungumay ta ina kokarin daga ta sai naji duk taimin wani irin nauyi, kamar ba salimat ba,
Kafin in kifta ido har ta sullubo yar baby ta tana fama calara ihu irin na jarirai,
Wani irin mugun tsoro naji yakamani, don bans an abinda zan iya taimaka mata dashi ba,
Idonta a lunshe tana hamdala tace min fadima kira maman umar da sauri tazo
Aiko aguje na kwasa da gudu na manta sam banda wani rigan kirki ajiki,
Sai falo ina ihun kiran maman umar,
Suna falo suna break sukaji ihu na kowa sai ya watso min ido don jin komai yafaru hankalinsu tashe,
Da sauri maman umar tafito kitchen din cikin rikecewa,
Mu kaci karo a kofar kitchen din da ita,
Ina haki nace salimat ta haihu,
Duk a rude suka tashi tsaye cikin mamaki suna kallo na,
Maman umar da sauri ta shiga dakinta ashe ita dama da shirinta take,
Muka bita diiiii abaya sai dai wanan karon akofa na tsaya munajin baby nata tsala ihu duk ta karade gidan ,
Sai da tagama gyara su sanan ta miko muna yar baby fara sol da ita kamar uwarta, an nade ta cikin farin shawul,
Amal akafara ba sai ta wuce direct inda Sheriff yake tsaye nisa da mu cikin damuwa,
Saida yakare mata kallo ban sha,awa sanan ya kalli gefen da nake tsaye yace min indauko mai dabino da ruwan zam,zam cikin sauri natafi na debo mai su nakawo mai
Na iske yanawa baby kiran sallah da yagama yakarbi dabino yadan tauna yasa mata abaki,
Yakama dan lasa mata ruwan zam zam din,
Saida yagama yadago kai mukayi arba dom dama duk mun kewaye shi,
Da sauri na dukar da kaina kasa
🐎ZEEE MAKAWA🐎
,✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎 HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,

Saida komai ya lafa, ne kowa ya dan natsu guri guda,
Maman Umar tagama gyara komai sai ,Sheriff din ya shigo dakin don yaiwa salima sannu da kuma barka da arziki,
Ina kitchen naje hada mata abincin da zata dan ci , abinci mara nauyi nai mata,
Sam basan cewa ya shigo dakin ba don da banshiga ba alokacin,
Salimat nagani na ta ce min sannu fadima da kokari,
Nagode kware da hidimo min ki,,
Gare ni Ubangiji Allah ya baki miji na gari,
A kunyace na ansa mata da amin aiba komai,
Sai alokacin nagan shi tare da su Amal da Salim suna ma baby wasa,
Amal tace aidole ki godewa Fadima salimat, tunda itace yau nurse mai karban haihuwa
Cikin mamaki Sheriff yace, what fatima, yana mai dan nuna ni da yatsa yace
Yace interesting nd welldon,
Ke yar karama da ke har kin iya karban haihu kuma agida,
Dan murmushi nayi gami da sadda kaina kasa,,,
Amal tace ai fadima tayi kokari don daini gaskiya bazan iya ba,

Sheriff yace gaskiya dole a,tafi asibiti da baby da uwar don adiba lafiyan su
Yadan kalli gefen da salimat ke zaune tana wani irin zufa yace mata kin san kunyi kasada kware don haihuwa ya tatare da matsala acikin shi
A sanyaye tace wallahi sheriff a bazata abin yazo min don ban dauka cewa haihuwa bane,
Allah yasa fadima tazo itace ta taimake ni,
Chapter 67 · 0% Book details