← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 139

Sashe 7

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ginan gidan gaskiya ba laifi komai ya hadu daidai da zamani ,,,,,, kujeru ne manya manya sai, kayan kallo dana kida saiti masu kyau.
Ga dinning table agefe guda,,,, sai wata kofa da zata sada ka da kitchen , shima kitchen din ya hadu sosai komai na bukatar zamani akwai a cikin kitchen din.
Wasu samari guda uku tagani acikin falon gidan suna game kowanin su dagashi sai wandon tree quater, da yar singilati.
Sukayi ma hajiya sannu da zuwa ,,,,, guda daga cikin su ya , shiga ciki fada ma zinaro bayan kamar minti biyar yafito.
Yace ance tashigo daga cikin uwar dakin.

Hajiya Zinaro zaune a gaban mirrow tana shafa mai dagani daga wanka tafito.
A ,a mai sharwali kece tafe da safen nan
Hajiya na washe baki tace wlh nice zinaro.
Tun shekaran jiya da kika tafi kin barni da tunane kala kala azuciyata.
Shine nace bari inzo don bansan lokacin da zaki koma ba.
Zinaro ta lakato mai da yatsanta tana shafa ma kafarta tace,,,, "eh gaskiya zan wani dadewa ba zan koma kinsan yanzu ba wani harka sosai a cikin makka kamu sukeyi don haka a jidda ko Riyadh,
Sunta dan jefa hiran wa yanda sukayi zama dasu alokacin da suka fara zuwa aikin TAKARI na farko,,,,
Zinaro na bata lbr ai wasu sun dawo gida wasu kuma suna can wasu kuma sun rasu dadewa.
Cikin samarin dake zaune falo guda ya shigo yana fadin hajiya yau sai mun sayo kayan miya agidan nan don wanda yarage baida yawa kuma sun fara lalacewa.
Tace kadauki ga kudi can kaje ka sayo abinda duk yadace asaya.
Bayan fitar saurayin hajiya tace wa " yanan yaran "yan uwanki ne ko
Dariya sosai hajiya tayi tace yan uwana na,bariki ba ,Da su nazo daga can
Saurayi nane da abokan shi,,, saurayi fa kikace to may ye aciki don nace saurayi nane.
Hajiya takura mata ido har dan wani lokaci tace kai haba Zinaro,,,wa " yanan yan yaran zakice wai samarin ki yo ai wanan, ma mun kusa haihuwar su, Idan ma bariki kike so ai sai ki samu daidai dake amma ba wa yan nan yara ba
Wani irin dariya zinaro ta kyalkyale dashi na shakiyan ci gami da aje roban man da take shafi gefe guda tana rufewa,,
Ta ce lalai mai sharwali baki akasan don ina ganin ma ko a kanon kauye kike. Ai wa yan nan yaran sufi manya dadin sha,ani don su idan kika basu kudi kadan sai su biya maki bukatar ki fiye da yadda kike tsamani,,, kallonta kawai mai sharwali ke yi,,,,,,,,
Ta shashantar da maganar ita dai hajiya duk al,ajabi ya kamata, mamaki takeyi da wanan irin hali na su zinaro,,,
Saida tagama shirin ta tsab suka fito falon inda zinaro ke ma hajiya tayin samarin ko akwai wanda yai mata taja guda
Ai barikin nawa baikai can ba Zinaro inji hajiya
Taufa ashe har yanzu da sauranki maisharwali. Don ko kinga su nan ba karamin riba naci dasu ba zuwan mu wanan bukin,,,,,,

Zama akayi sosai da hajiya da zinaro taba hajiya shawarwarin abin da yakamata a,yi saboda tafiyar su saudiya.
Komai an,kan,mala game da tafiya duk wani hanya da za,a bi an yi,,,
Hajiya taba da kudade masu yawa saboda komai yatafi daidai
Aiko kafin hajiya zinaro tabar kasan komai ya zama daidai,,,,,,,,,

Lokacin tafiya kawai za,ajira yayi abar kasan zuwa sabuwar duniya

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
[10/3, 19:02] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣3⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

Ina duk masoya novel dina fatan alheri , nagode kware da kulawan ku yan uwa

Anty Mariya SB Allah ya baki lfy

Tunda hajiya ta dawo daga gidan zinaro mukaga canji sosai a wurin ta, Sai fa,ra,a takeyi da kowa
Mudai namu idanu kawai tunda babu daman mu tambaye ta,,,,,,,
Ai yukan mu kawai mukeyi kamar yadda ya kamata ,,,,, saidai mun ga hajiya kamar tana cinikin gidanta da shagon ta dawasu...

Mukan ba matsalar mu bace iyaka naji Sukaina yar sa ido na fadin kila hajiya zata maidamu gidajen mu don tana gani zata koma makkah da zama ne.
Jin haka yasa na fara murnan zan koma gida very soon,
Zanje inga hafsat dina da dattijo dan kani na ,,,,, har nace sai in saya masu bread da lemo in kai masu ,,,, haka nadinga sake sake a zuciyata,,,

Wasu mutane sukazo su biyu wurin hajiyan mu sun dade da ita cikin shago,,,,,
Hajiya takira Yumma tace taje tafada muna kowa ya gyara jikin shi da,kyau za ,a dauki photo ne. Aiko muka shiga murna za muyi photo.
Ta,ba mu, wasu kaya masu kyau doga yen riguna tace kowa yasa,a photo dashi,
muna ta murna zamuyi photo ban kwana da juna tunda ance hajiya zata bar kasa ne.
Sam bamu kawo cewa damu za,a tafi ba,,,,,

Bayan mai photo yadauke mu ya wuce da kwana biyu hajiya ta turo wata mace tazo tai muna kitso da kunshi masu kyau
Munata murna muka fito shar da mu kamar wasu yan birni,,,,
Tundaga ranan da akai muna kitso bamu kara zuwa shago ba kuma ,,,,,
Kayan dadi muke ci a gida babu wani tsangwama da ake muna yanzu,,,,

Bayan kaman kwana hudu tsakani cikin dare muna hira a falon gidan mu
Sai hajiya ta fito ta zauna a gefen mu duk mukayi shiru,,,,
Waya take yi alokacin amma saboda ladabi sai duk mukayi tsit wurin.
Tana gama wayan takai dibanta gare mu ,,,,,,, lokacin tai wani dan gyaran murya sai duk muka kara maida hankalin mu gareta.

Tace duk ina son ku bani hankalin nan ku saurare ni da kyau ,
Mukayi shiru cikin ladabi, tafara magana,
Tace dukan ku, ku ,biyar, zamu bar kasan nan zuwa kasar makka gobe da asuba insha Allah
Nasaida gida na da wasu yan abubuwa nawa, saboda tafiyar mu,,, nasan cewa baza mu dade ba shiyasa ban fada ma kowa cikin yan uwan kuba saboda dazaran angama aikin hajji zamu dawo nan kano muci gaba da sana,ar mu,,,,,,
Naga ,su Sukaina duk suna ta,murna sai Antyna Rugaiya ce naga bata wani murna sosai kamar sauran.
Naga kowa ya shiga hada kayan shi,,, sai hajiya ta shigo dakin na mu da kanta,,,,,, Tace muna ba wasu kaya masu yawa zaku dauka ba kada ya wuce kala biyu kubar sauran idan mun dawo sai kuyi amfani dashi,,,,,
A , haka muka dan tsinci dan abinda muke so mukabar saura da niyar in mun,dawo mu kwashi abin mu zuwa gida,,,,,,,

Tunda asuba masu adaidaita suka zo suka kwashe mu zuwa filin jirgi
Hajiyar mu ce da wasu suke ta zirga zirga a wurin mudai muna gefe guda, muna jiran ,,, Yadda za,ayi damu
Barci nake ji inna hamma Rugaiyya ta ce in kwanta ajikinta kafin , hajiya mu,tazo daukan mu,,,
Ina cikin barci naji ana tashins natashi firgigit dani naga an bamu wasu kumshi kaya ance kowa ga nashi ,,,
Wai goro ne a ciki dasu kayan miya irin namu na nan kasar ,,, wasu kuma wai turamay zani ne a cikin kunshin da sukayan amfanin mata,,,

Barcin da bankara yi ba ke nan duk inda zamu don a auna mun je an muna komai da ya kamata ,,,,, Kuma cikin ikon Allah kowan mu ta samu tafiya saboda an hada mu da wasu mutane can da ban waidasu zamu.

Allah mai ikon shi yau ni FATIMA Mohammed Sani ,ce acikin jirgin sama zuwa makka ,,, wai a sanadin yar ga aiki yau kuma suna zai koma TAKARI,,,,,,,,

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:06] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

Yan uwa musulumai na, duniya ina muna murna da sallah Allah ya kara ma musulunci daraja da dauka
Allah ya rupa ma kowa asiri Ubangiji kataimaki dukkan al,umman musulmai ameen👏👏

(Dogon Daji)

A gaskiya kamar yadda mai gari yayi alkawarin cewa zai taima ,haka din ne kuwa don ya taimaka sosai wlh wurin neman Gajiye,,,
Yakuma fadi a masallacin jumma,a ataimaka ayiwa fadima addu,an Allah yadawo muna da ita lfy,

Aiko mutanen kauyen mu su kasa Gajiye gaba da tsina da Allah waddai da ita.
Wasu sukace ai tayima inna maganine kafin tadaukeni wasukuma suna fadin ai kwadai ne yakai inna badani ,,,, wani gefen kuma sunce ai anfada masu an,sayar dani ne wurin yan yankan kai don Gajiye har tayi arziki a birni ko.

Wanan maganganu sune suke kara tayar ma inna da hankali sosai ,,,, duk tabi ta ramay bata cikin hayacinta so sai yanzu,,
Yayana hafsat ma da ta,fita sai ta dawo gida da kukan ta,saboda gorin da ake mata acikin gari.
Inna kullun tana kai kukanta ga Allah ,, Allah ya tsare mata fadima,tar
duk inda take,,, tana kuma tuba da cin amanan mareniya da tayi

Ana cikin haka kawai saiga Gajiye wani mutumin kauyen mu ya gani a Abuja a kasuwan wuse,,,,,,,,
Bata ganshiba yayi ta binta har yaga gidan da take ya tambaya ko nan take akace mashi eh lalai a nan take zaune tana haya,,,
Ya aika gida cewa yaga Gajiye har ma gidan da take zaune ya bincika anfada mashi,,,
Cikin kwana biyu mutanen dogon daji suka zo wurin wanan mutumin

Da taimakon jami,an tsaro aka kamata ,,, tana ta fada tana fadin ita mai tayi daza,a zo har nan inda take zaune ai mata cin zarafi irin haka suka ce ai kawai tazo gida mai gari ne ke bidan ta.
Koda aka isa dogon daji da ita tana wani,wuri wuri da ido har aka kira inna yar kulu tazo kofar maigari,,,,,,

Maigari yayi gyaran murya ya bude taro da addua , da kuma yima mutanen shi ,nasiha na su ji tsoron Allah aduk lamarin su na duniya,,,,, su sa Allah agaba saboda zafin ne ma baya kawo samu,,,,,,
Chapter 7 · 0% Book details