Sashe 74
Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sha mudan wuce, abin mu,,, Tsayawa tayi tana min wani kallo cikin mamaki tace hai fadima, Fadima kema kinsan cewa gurin ki kawai nake dan samun sauki acikin ku muryan ta yai wani rau, rau kamar zatayi kuka, Ban iya cewa komai ba don tabani tausayi harga Allah, Haka muka karasa har inda muka aje motar mu a bakin tin da ke gefen haramm, Daga nan muka wuce wurin gyaran jiki, Ga mamaki na nadauka ko itace kawai za ai mawa sagashi dani da ita duk an muna Nakoma kamar wata yar bakaken indiya komai na sur mace da nake da shi yakara fitowa tsab ajikina, Tun a mota Aziza ke yaba irin kyaun da nayi sai murmushi nakeyi kawai don nasan cewa ba karya tayi ba ,, Saida muka kusa shiga unguwar mu ne take ce min duk fa ke na siyo ma wayan nan rigunan , Cikin mamaki na,kalleta nace ,a,a aikin san cewa bani kadai bace sai dai ni da Amal , Sai ga tadan bata rai kadan can kuma tadan sake ranta tace kece kika rakoni kuma kedai na siyawa , Ba matsala zan raba da ni da ita kin ga tasamu albarkaci na aiko, Har muka kara gida tana min hiran jin dadin da tayi na ganin nasake jiki da, ita, Ko ba a fada ba nasan cewa Sheriff din mu yadawa daga tafiyan da yayi taniyar yin kwana biyu a babban headquarter kasar saudiya watau Riyadh, Da mamaki nakai kallona ga motar shi da naga yana yawan shigarta, Kamar Aziza ta gane mamakin da nakeyi azuciya sai tace ashe har sun iso don dama yau ba zai kwana a can ba don suna da wani meeting da ma,aikatar su gobe, Insha Allah,, A falo muka samay su duk kan su har almustapha sun baza wasu takardu a gaban su suna dibawa, Sallaman da mukayi ne yasa kowa dagowa kai don yaga ko suwa ye, Dammm gaban shi yafadi saboda ganin da yayi ko yaushe kara canzawa kawai nake yi, Cikin kwarewa da shagwaba take mai magana, har ka iso Sweet habibi, Kai kawai ya kada mata alamar eh , ga kaya ahannu mu niki niki ta,isa inda yake tadan man na mai kiss a tsakiyan goshin shi, Sai ta,Zube saman kujerar dake gefen ta tana cewa wassh Allah na duk nagaji wallahi, Aikin da sukeyi yadan aje gefe guda yadan kalle ta yace, U are to lazy, wanan dan fitan da kikayi kike cewa wai, kin gaji, Suna juna wani irin kallo cikin shaukin so,, Kayan nazo gaban ta na zube gefen kujera datake zaune, Kai yadago A,hankali ya bini da kallo sai kuma yawani lunshe idon shi a hankali kamar maijin barci , Kamshin turarain da yaji ina yi duk yakara rikida shi, Kamar mai rada yace mata wai har ina kukaje ne haka yau kuka kwaso wanan kayan mai yawa, Ke kaya basa isan ki dai ko nuna ni tayi da hannu ta guda tana cewa yau ai duk kusan sayayyan ga mai su can, Muna hada ido da Amal takara sakar min wata uwar harara da yafi nadazu,,, Ida nake tsaye ina,sha wata uwar harara daga Amal yadan kalla lokacin kuma hararan da Amal take min yabani dariya, Sai yayi sa,a ina dariya a lokacin, Abinda yadade baigani ba ke nan tun ina yar karama a Riyadh lokacin da nake shiga cikin ruwa ina wasa agidan shi, Murmushi ne ya subce mai ba shiri saboda tunawa da yayi da wanan lokacin Saboda yaga yadda nake wasa daruwa har dawo yakeyi ya tsaya ta glass din falon shi yana kallo na ,, Saboda haka kawai yaji in burge shi dan banda tsoro ko fargaba kai tsaye nake abina,,, Aziza ce tace min inzo in kwashi kayans intafi dasu, Tazabe duk wanin abinda take bukata daga ciki tabar min sauran tarkacen da rigunonin, Da alama sheriff yaji dadin hakan da tayi har cikin rashi yace mata Kai amma dai wanan fitar dama na tane ko , Tadan rausaya kanta tace aikasan dole in saya mata tunda har ta bata lokacinta ta rakani batare da nuna gazawanta ,,, Ina kwasan kayan gurin Amal na nufa direct dasu nara dai dai nace mata ta zabi duk wanda take so tabar min kashi guda,. Dariyan yake tayi ko shi don yayanta ya gurin ne don kada yace wani abu da bata karbi kayan ba, Amal tace a,a ki bari kawai in dauki wanan, Wani dan rigar barci kawai ta dauka, Tundaga wanan ranan wani irin shakuwa da amin taka ya shiga tsakani na da Aziza ,, Amal tai min fada taimin nasiha tace inyi hankali da ita don yar duniya ce, Badan Allah take so na ba ita tana ga da wani manufa take jana ,a jikin ta, Sai naga cewa kawai, kamar dai don basu ra,ayinta ne kawai,