← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 139

Sashe 125

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

🐎ZEEE MAKAWA🐎
[12/4, 11:20 PM] ‪+234 703 300 7734‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣2⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,,,

Tun cikin dare bayan tafiyan bakin mu, muka soma shirye, shiryen tafiya, zuwa maiduguri,
Natambayi sheriff ko a nan zamubar su gwago da su mariya yace mi aida su zamu tafi,
Shiru nayi saidai a zuciya sai ina gani kamar mun yi yawa ga tafiyan ace duk yan uwana har kusan mu biyar
Zamu je masu bakun ta a,gaida a gaskiya ina gudun abin magana saboda ban san irin rayuwar mutanen can ba,
Duk wani abinda ya kamata mudauka dan bukatar mu mun dauka , dan ba musan abinda zamu tarar ba acan,
Tunda sheriff yafita da yamma baidawo gidan mu ba saidai a waya ne mukai magana da shi, inda yake sheda min cewa tafiyan safe zamu yi,
Sai da safe ya shigo gidan mu a cikin shirin shi tsab
Duk da mun shirya karyawa kawai yarage muna muyi a lokacin,
Ina zaune bakin gadona ina baiwa ummibanan nono ya shigo dakin mariya dake tsaye gabana tanawa Abbazannah wasa tana jiran dayar tagama shan nono ta miko min shi tai niyar fita dakin,
Da hannu sheriff yadakatar da ita ta tsaya abin ta ba zama zai yi ba,
Inda nake yazo ya kai min dan sunbata a gaban goshi cikin larabci yake tambayar lafiyar mu na ce mai kowa kalau masha Allah,
Yace min duk wani gifts da yakamata arabawa mutane sa acan yasa Bashir ya tanadar min zan samay su acan ko,
Nai mashi godiya tare da yimai addu,oi da fatan alheri akoyaushe,
Sai kuma ya ce min duk da bai san ko kwana nawa zanyi can ba yana son dan Allah duk abinda muka gani dani da su gwago muyi hakuri da shi,
Nace mai duk abinda za ai muna insha Allah bazamu dauke shi komai ba tunda bashi yai muna ba,
Ankawo min abinci har dakina muka karya tare da shi don irin sakkon dayayi zuwa gidan mu nasan cewa baici abinci ba,
Yana cin abincin yana kara yi min bayanin cewa har gurin ummi yake sonmuje mudan kwana biyu
Na nuna mai murna na afili wanda hakan yasa shi jindadi sosai aranshi,
Duk mun fito cikin shirin mu tare dasu gwago inda ,
Suna rugumay da yara niko Aisha ce kawai na rike da hannu na zuwa bakin get,
Dan ni azato na da mota zamu tafi ashe jirgine zamu zuwa can, saidai wasu kayan mu za,a biyo mu dasu,
Cikin kwaliya muke na gani na fada saboda nasan cewa Sheriff mutum ne mai son yaga matar sa acikin shiga na kwarai na alfarma da mutunci,
Shima hakan ne dan wasu yadi yasa na maza na India Pakistan, yadin yana da kyau so sai kuma dinki kusan irin nasu ne,
A hanyar muta airport ne muna zaune a bayan motan nida sheriff nake tanbayar shi,
Amma dai shi ba dadewa zaiyi a can bako zai koma gurin aikin shi,
Saida yadan murmusa min kadan yace har kun gaji da gani na ne ko kuwa,
Cikin sauri na ce, mai haba wa ,ai bana fatan ranan da zangaji dashi a duniyar nan,
Yace to kina tsoron kar in bar ku can ne ku kadai,
Wani murmushi na danyi,
Sai nadan matsa kusa dashi kadan na kwantar da kaina saman kafadar shi,
Nai magana acikin tausa murya kamar mai rada na ce ba tsoron nake ji ba sheriff,
Indai son mijina a kusa dani ne kawai, bana son mu ni,santa da junar mu ko kadan,
Shiru yayi batare da ya ce min komai ba,
Saidai ni nasan cewa shirun shi na nufin wani ansa ce hakan nan , dole in sa ido in fahinci ansar maganata nan gaba,
Muna isa airport muka samu time din tashi har ya kusa batare da bata lokaci,ba muka shige sai tafiya,
Tayi ce mai dan nisa sosai mukayi wanan karon din afi wanda mukayi daga sokoto zuwa Abuja nisa,
Wani tunane yazo min acikin jirgin ina tuna yadda zan je in bakunci wasau mutanen da ban saba rayuwa da suba acan baya,
Kuma gashi da alama ba sajin hausa akasarin su duk yare suke yi,
Ban san ko ya mahaifin sheriff zai tareni ba kasancewa ta yar talkawa, badiyan masu arziki ba
A yadda naji su Amal na hiran arzikin shi da kuma irin rashin ko in kula da yakewa yan uwan shi,
Uwa uba kuma irin yadda zan riski hajiya mama,
Tuna ne sosai nayi har zuciya ta takoma min tunanen irin matan sheriff da an yi zaman kishi da su arayuwa na,
Sai dai kuma wata zuciya na ce min ina ruwa na da su suda suke gidajen su mai zai hada ni da su ,
Alokacin naji dadin tunanen da nakeyi har nakai kaina a makarin kujerar da nake zaune dan inji dafin tunane,
Nace nadai ji manya na fadin Namiji ba dan goyo bane, watau ke nan koni in yi hankali da Sheriff kenan arayuwana, dan zai iya zuwa wata rana ya juya min baya,
Na ce hmmm ni ko asani na ai namiji shi mafi darajan mutum wanda ke haska mace komai mukamin ta ko arzikinta ko mulkinta, ko kuma kyau,
Dazaran baki da aure duk wanan daular yatashi a free dan baki taba daraja a idon duniya,
Sai kawai a zuciyana nasa aikoda anan gaba sheriff zai juya min baya zan ita hakkuri da shi badon wai abin hannu shi ba ko kuma kwadan zama dashi,
A,a saidai kawai dan bazan taba mantawa da irin mutuncin da yai min ba arayuwa ta san nan kuma ga zuria, a tsakanin mu,
Nakara dan lunshe ido na nakara cewa acikin zuciya na,
To ai shi sheriff ma dole mace taso shi saboda irin hakkurin da Allah ya bashi ga kuma kyautatawa a tsakanin shi da mace,
A haka naita nazarin rayuwa ta da na sheriff a cikin zuciya na ni kadai keyi kuma ni kadai keba kaina ansa,
Jin sheriff dake zaune a kusa dani ,nayi yana dan murza min hannuwa na yace min batare da ya kalle ni ,ba yace, may kike tunawa haka kike ajiyar zuciya,,,
Chapter 125 · 0% Book details