← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 139

Sashe 94

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Da sauri Amal ta juya cikin fushi tabar dakin nawa, A dakin Ummi ta samay ta rai a bace take mayar ma ummi da komai dake faruwa agidan
Hakalin UMMI yatashi matuka don sam bata zaci hakan ba daga Azizan,
Ina kwance a daki kasan cewa yau ban shiga school, yasa da nagama abin da nakeyi sai na koma na kwanta , saboda in samu indan huta,
Jin sallaman Ummi na daga sama a cikin dakina nayi mamaki kware har na nuna mata hakan a fuskana,
Mikewa nayi zaune daga kwanciyar da nayi, ina mai gaida Ummi, dake kokarin zama saman yar kujerar da aka a je a cikin dakin
Shiru yadan biyo bayan zaman nata,
Can takira sunana a hankali tace may yasa kibar ma Aziza dakin ki
Alhalin kisan cewa wana dakin shine dakin ki na halal malal,
Saboda ko wanan gidan saboda ke ce yasa aka gyara shi,
Idan har ba zata zauna inda yace na baki ba da ai sai ta koma inda tafito
Don ni ba ga abinda yakawo ta wanan garin ba tun da Alhajin karami baya kasar, ban san zaman may take anan ba,
Saida na barin ummi ta kare zancen ta duk kai na yana a kasa,
Can nadago kaina ido na sunyi raw ,raw alamar kuka ,
Nace , La, ummi ai ba komai anan din ma inda nake babu wani matsala gaskiya,
Ummi kinsan cewa ita ce, matar sheriff, itace ta can can ci zama a wanan dakin bani ba,
Ummi kinsan cewa aurena da Sheriff kawai nufi na ubangiji amma ai ni ban kai matsayin auren shi ba,
Ummi tace min assha, fadima aure ai baida wani can,can ta ko sa,ayi,
Abune mukaddari daga Allah,
Idan har kikace haka to gaskiya baki godewa Allah da ni,imomin da yai maki ba,
Nace a hankali na gode mana Ummi, baga shi ko ina godiya akai ba,
Dan murmushi na manya mai nuna cewa yaro dai yaro ne tai min,
Tace fadima wa,yan nan kishi yoyin naki da kike gani basu san Allah, don basa aiki da maganar Allah,
In bashi ba gaskiya da batayi wanan abin kunyar da tayi ba
Donko kowa yasan cewa ai ba dakinta bane dakin ko,
Son zuciyane kawai irin na marasa tsoron Allah, wa yanda basa tsoron gamuwar su da Allah
Aida tana da imani da ta tausaya maki acikin wanan halin da ki ke ciki haka,
Amal ko tana waje sai faman kiran layin dan uwan su takeyi bata samu ba,
Sai a na karshe ne tasamu layin nashi ya shiga,
Bayan sun gaisa ne take tambayar shi ko yasan cewa aziza tana saudiya kusan sati guda,
Yadda yai ihu mamaki saida Amal taji shi,
Yace nafada mata cewa ina na turkey muna kokarin muga cewa duk kayan mu ansa a conterner neno anturo muna dasu gaba daya,
Maimakon Amal taji yai magana sai taji kawai ya ma kashe layin nashi gabadaya,
Dif kake ji,
Wani haushe yakamata tadan kali wayar tai tsaki,
Tace in fa yayan mu yasan cewa bazai iya daukar wanan amanar ba gwara kawai saki diyar mutane
Don kada su taru shida matan shi su cuta min, tunda duk sun fini wayo da sani ta duniya,
Azizs na daki abinta hankali ta akwance sai waya takeyi ta yarda zata samu ta samu, sa,ata taci
Nasarar lalata min cikina ko ta halin kaka, sai taga bayan cikin nan,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
7⃣6⃣
BY
🐎 *ZAINAB*IDRIS *MAKAWA*
🐎 *HUGUMA* *GROUP*🐎

Almost true life story,,,,
Chapter 94 · 0% Book details