Sashe 133
Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Jin zuciyar shi yakeyi kamar zata tsage mai gida biyu, saboda jin kukan da takeyi kamar ana mai yayafin ruwan zafi ne a jikin shi,
Burki yataka da karfi saida ta dan razana, don yadda ya taka birkin mutanen da ke gefen titin suka dinga kallon su,
Shiru yayi yasa ma min idon ina ta faman gumzar kuka, na,
Ganin yadda ya faka motar da karfi ga kuma mace aciki tana kuka yasa yan bagaladi zuwa inda motar take dan ganin abinda ke faruwa a cikin motar,
A hankali suka kwankwasa glass din motar dan na ciki su bude masu,
Katin shedan wurin aikin shi yadauko yafara nuna, masu cikin girmamawa , suke ce mai may ke faruwa ne haka yace,
Masu ba matsala su wuce kawai, abinsu sai yai godiya yai kick din motar shi, yadau hanya,
Muna shiga get din gida mu ya dan waigo inda nake yace, idan har ina son su Ummi su san abinda nake cikine inci gaba da kukan da nakeyi
Dole nadan saita kaina nashare hawaye da tmyai min jagab a fuska,
Cikin dakiya nadan daure na bude mota zuwa cikin gidan
Cikin sauri na haye matakalan hawa sama ina mai zub da hawaye ,
Shiga na da kamar min ti biyar naji anturo kofar dakin a hankali,
Shiru naji ba ai min magana ba ni kuma ban waiga inga ko waye ba,
Don ni a zato na sheriff ne wanda yanzu haushin shi nake ji don gani nakeyi shi yai min wayo har aka kai ga haka,
Muryan mariya na ji cikin wani yanayi tana fadin haba anty dan Allah ya kamata ki daina wanan kukan haka,
Sai a lokacin nadan waigo kadan , fresh milk ta miko min a cikin wani cup din tangaran maidan sanyi kadan,
Bamusu na karba don kusan shine abinci na yanzu,
Duk son da nakewa fresh milk din yau sai naji shi kamar wani guba nake sha ,
Ko rabi ban sha ba na aje a sidedrower dina na koma ina batun dunku lewa a saman gado,
Mariya tace wai anty fadima kin san may kike yi kuwa,haka,
Bafa cikin shege kikayi ba cikine mai uba kuma uban ba gajiyye ba wanda ko kun kai ku nawa ne zai iya kula da ku,
Anty ko dai ni dake kasa gare ki aibani wanan abin dan nasan cewa ba mai wuce kaddaran shi,
Balle wanan abin alfahari ne ai agare ki,
Da sauri na dan waigo ta dan jin abinda tace min,
Ta ce eh mana, shin ki ko san cewa a kauye duk da talaucin da muke yi har gasan haihuwa suke yi a haka nan,
Fuska na alamar mamakin maganar ta ya nuna ,karara,
Taci gaba da fadin a cikin wanan talaucin za suyi ta zuba diya waidan kada kishiya tafi su tara diya,
Shiko miji ko oho,ho,ho, wata ma da kyat ake samun dan akuyan da za ayanka mata,
Gashi ba wani wada,ttacen abinci da mace zata ci takara kuzari,
Hakan bai hana kafin kwana biyu kiji ana fadin ai wance ciki aggareta,
Kinga sun samu riba biyu kenan gashi sun raya sunnan, ma,aiki (S A W) ga kuma ribar kishi da suka samu, ace ai wance yanzu aurenta shekera kaza ne diyanta kuma kaza,,,,
Kafin taci gaba sheriff yashigo dakin dauke da ummibanan a hannun shi tana yar fitinar ta da alamar nono take so,
Cikin ido na yake kallo yaga ko zan karbi yarinyar ko kuma zanki karban ta ,
Ina karbanta na bude nono na mika mata tai wani irin ajiyar zuciya takama nonon
Sai faman aje zuciya take yi don jin dadi da alamar tadan dade tana kuka,
Mariya ya dan kalla sai kawai ya fahinci cewa aikintane hakan,
Gefen gado yadan zauna batare da kalle ni ba, ,yana fuskan tar kofar dakin,
A hankali ya ke magana yace min Fatima kiyi hakkuri dan Allah ki shayar da yaran nan har zuwa lokacin da ya kamata a cire su a nono,
Wani iri naji a cikin zuciya da yace haka dan ban san lokacin da tausayi kaina da na yaran ya kamani ba,
Wani sabon kuka na sa masu mariya dake shirin barin dakin ta waigo tana fdin Ya Salam,
Anty fadima wai ko lafiya kike da wanan abin da kike yi,
Shin kisan cewa Bintu ta haihu da wata uku ta samu wani ciki,
Duk da kuka nakeyi saida nadan waigo dan mamaki jin maganar yar kaunata mai dabiar manya mata,
Tace walle ko bata kumayi wani fitina ko shiga tashin hankali ba,
Iyaka dazata haihu uwar ta ,ta taho, tadauki yarinyar ta farko, anka barta da dan jaririn,
Takara she zance da cewa to balle ke ga Ummi da Inna damuwa mika damuwan ki banda ki cika ma yaya sheriff gida da yan diya,
Wani irin harara da bugu nakai mata ta mike tana dariyar keta,
Sheriff da ke jin mu ya kama muna dariya yana dan murmusawa,
Fitar ta keda wuya sheriff yadan matso kusa dani kadan yadan sau,sauta muryan shi yace min fatima, kafin yafadi wani magana,
Nai saurin toshe mai baki , na a,za kaina asaman kirjin shi, nakama kuka,
Rungumay ni yayi ya na dan shafa min kai alamar lalashi,