← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 139

Sashe 135

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Saida akai sadakan uku, sannan muka fara shirin komawa saudiya,
Inna kan tace atabau ita bazata koma tare da mu dama zaman can ya ishe ta
Tace ace mutum kulun yana zaune bai aikin komai saidai aimai duk abinda yake so,
Gaskiya bazata iya wanan rayuwar ba itakan,
Ganin cewa inna ta matsa yasa Shehi ya cewa sheriff yasa amaida ita gida,
Banji dadin hakan ba gaskiya naso ace Inna tai hakkuri mukoma har lokacin da zan haihu amma sam taki yarda,
Hakan yasa muka dan daga tafiyan mu dan mu kaita gida tukun,
Wanan karon nasamu taron arziki gurin mutanen garin dogon daji so sai
Da kaina natafi gidan maigari batare da sanin kowa ba ,
Nakai makukan matsalata dan ina son in koma tare mama maidakin shi,
Sam baiji dadin yadda inna taki yarda ta zauna da mu ba a can yace mata ai anbar wanan kunyar da take yi yanzu
Yanzu koda gidan yar farin ta ne tana iya zuwa ta zauna, tare dasu balle ni da nake yarta ta biyu gurin haihuwa,
Hakan yasa muka dawo tare da mama matar maigari sai tumba wace ta leke muna da ita zamu tafi kasan cewa dama bata taba haihuwa ba kuma mijin ta yadade da rasuwa,
Mundawo lafiya saudiya komai yacigaba kamar yadda muka saba ada,
Mariya zata ci gaba da karatun ta, anan amma sai bayan na haihu,
Har zuwa yanzu sheriff bai walwale ba daga rasuwar hjy tsohuwa da mukayi abin ya buge shi so sai dan har da yar rama sai da yayi,
Yau ina daki na ina barci na hankali kwance saboda yaran suna can gurin su mama tun da safe,
A cikin barci nadinga jin murya sama sama, murya da sam bayi zaton jin shi ba a lokacin,
A cikin karfin hali na bude idona don in tabbatar bar in ba mafarki nakeyi ba,
Hjy mama ce tsaye a kaina tayi murtuk da fuskanta da yafara tsufa a,lokacin,
Muna hada ido ta watso min harara tana cewa saboda samun guri da ki ka yi shine wai har zaki bada dokar cewa kada atashe ki idan kin kwanta,
Kamar banjitaba nai kokarin saukowa daga saman gadon
Duk da nauyin da nayi hakan bai hana ni kaiwa har kasa ba ina gaisheta,,
Itama yi tayi kamar bata jini ba sai cewa da tayi min,
Samun wurin har ya kai an fara tara mai yara kamar haihuwar bera, agidan
Don kawai an samu dukiyar banza, ana son a mamaye guri,
Kaina yana duke akasa zuciya tana fada min in mayar mata da ansar maganar ta ma tun da ba mutumiyar arziki ba ce ita,
Saida na yaki zuciyata so sai nai mata yar murshi mai nuna alamar sam banji zafin maganar ta ba,
Nace cikin murmushi mama wanan ai ra,ayin maigidan ne, haka,
Dan yafi son yaga kowani lokaci gidan shi na albarka wai,
Namike dai,dai lokacin da nake fadin maganata ta karshe,
Hanyar fita dakin nanufa batare da na kalle ta nabar mata dakin nawa,
Don in har na tsaya mukaci gaba da maganar baza a kwashe da dadi ba,
Falo na sauko da kyat duk da kafa, na sun min nauyi so sai da kyat nake taka su alokacin,
Abba nagani zaune saman daya daga cikin kujerun falon namu yana , duk yadan ramay da alamar bai da isasar lafiya a jikin shi,
Cikin sauri na isa inda yake zaune ina kokari rusun nawa dan ingadashi,
Shima cikin sauri yake fadin ,a a fadima zauna abinki kawai mun samay ku lafiya dai ko,
Namayar mai cikin ladabi da lafiya kalau, yace gamu munzo kuma ashe maigidan yayi tafiya,
N
Cikin mamaki nace bai san da zuwan ku bane ko Abba,
Yadan kurbi ruwan tare da hade wani magani da ba ya ballo daga gidan shi yace a,a tafiyar namu zuwa jiya da yaune muka shirya shi,
Dan dama a US zan tafi ganin likitana na can sai kuma ahawara ya sake akan mu zo nan kawai,
Saida na tabatar da duk wani abinda za,a tanadar masu na ci da bukata an kawo masu, dan da kaina nafada kitchen din dan hada masu ,
Ko kallon hjy mama ban kara yi ba tun fitowar mu daki,
Chapter 135 · 0% Book details