← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 139

Sashe 109

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Bincike ya nuna cewa Fatima ta bar kasar saudiya, tun ranar da tabar gida
Kuma jirgin Nigeria ta bi zuwa gida Nigeria,
Amma tare da taimakon wata mata yar kasar Nigeria din,
Duk iya binciken da za,ayi anyi don a gano ko, da wace, ce fadima ta zo airport, a lokacin da zata wuce Nigeria amma ba,a gane ba,
Haka suka hakkura su ka koma makka cikin bacin rai,
Zaune yake saman kujera a falon shi, laptop din shi ke gaban shi yana searching din wasu kayan aiki da su,ke bukata a company su,,,
Saidai gaskiya a zahiri ne yake aikin a cikin system din shi,
A badili kuwa tunanen fadima ne fam a cikin zuciyar shi,
Yaso ace yana a Nigeria daidai wanan lokacin,
Amma hakan bai samu ba saboda tsaida shi da doctor kamal da Khalid sukayi akan cewa yadan dakata masu har su dan samu leave,
Ture system din yayi gefe guda, ya koma bayan kujerar ya jingina jikin shi akai, hannayen shi na rike da habar shi,
Wani irin iska mai fushi ya furzar daga bakin shi,
Yakara dan rintse idon shi , fadimar ce ke mai gizo a zuciyar shi,
Abuna farko da ya tuna dashi shine farkon ganin da yafara yi mata,.
Tana wasa da ruwa a cikin gidan shi na birnin Riyadh,
Sai kuma lokacin da ta tsinci wallet, din,shi a cikin shagon shi da suke gyara,
Yadan shafo sumar kan shi a hankali yakara furzar da iska,
Kuka takeyi sosai bayan irin wulakancin da Nafisat tai ma lokacin jiyar Ummi,
Mikewa yayi buzur daga inda yake zaune, ji yayi kamar a lokacin take kuka yake ji,
A hankali ya furta sunan ta yace fadima Y,? Y ? Why d u leave me?, fadima,
May yasa zaki tafi gida ke ka dai duk tsawon wanan lokacin da kika dauka baki gida,
Kawai sai ga yan maza yau hawaye na zubuwa daga cikin idon shi,
Ta dalilin tunawa da irin wahalal da yar karamar yarinya kamar fadima tayi a duniya,
Gashi yau ta koma gida tare da lalurar ciki a jikinta da kuma bacin ran rashin mutuncin da Aziza tai mata,
Kamar mai tuna nen wani abu da sauri ya haura zuwa sama bed room din shi ya bude cikin sauri,
Yana shiga ya nufi bayan wani da side drower dake gefe gudan dakin,
Yajawo shi a hankali wani drower ne yadan bullo bayan bangon dakin
Da alamar a manne yake jikin bango wanda ba kowane yasan da wanan drower, a gurin,
Wa su yan lambobi ya dan danna a jikin bangon sai wurin ya bude,
Yana budewa wasu irin gwala gwalai ne na mata masu matukar tsada da kuma kyaun gani,
Da guda guda yadinga daga su ya na dibawa , ya na maida su, inda suke cikin dan kit din su,
Saida ya gama ganin su tsab yakuma gamsu da irin kyaun su,
Sai yai wani irin ajiyar zuciya kawai,
Saman gadon shi ya koma yadan kwanta rigingine yana kallon rufin dakin
Daganin shi kasan cewa baya cikin hayacin sa,
Saboda harda wani dan kasunba ya aje a fuskan shi a kwanakin nan,
Wayar shi da ke gefen shi, ya jawo ,, yadinga bidan wasu lanbo bi,.
Bayan kiran da ya dan nawa dayan layin kamar second guda sai dayan bangare a kadauki kiran nashi,
Sallama tafara yi tare da gaisuwa duk a cikin lokaci guda,
Cikin larabci yake magana da matar mai suna Ma,issha,,
Yai mata bayanin cewa yana son ta shiga shagunar da ke cikin Garin da take masu kayan kware da kyau da tsada ,ta sayo mai kaloli masu kyau wanda zai yi pitting din mace mai chucuklet colour
Matar tace mai ba matsala yabata kwana biyu,
Yai dan ajiyar zuciya gami da lumshe idon shi,
Ya dan furta kadan yace fadima dole inyi duk wani abinda zai wanke ni da ga kowace irin zargi daga gare ki har ma da saurar yan uwan ki,
Haka,dai ya koma kamar wani ta ba be a wanan lokacin,
Allah ya taimaki sheriff Ahmad a wanan lokacin saboda ,duk wani process da yake yi a kan Company nin su yasamu karbuwa, so sai a idon duniya,
Hakan yasa Abu Abdallah yai mai kyauta ta musan man akan wanan gaga rumin cigaba da suka samu acikin wa yan nan shekarun da suka fara sana,a da Sheriff Ahmad,
Ashe wanan tafiyar da yayi har fadima tabar kasar saudiya saboda farautar rayuwar ta da Aziza ke yi mata,
Sheriff yasa hannu jari a wasu kamfuna, na Abu Abdallah,
Hakan ya janyo masa samun riba mai girma a ajiye ,a bankin kasar Dubai, al,amarin da cikin dan kankanin lokaci yasa shi bunkasa,
Hakan yasa yakara dadewa a she a wanan lokacin don yaga cewa komai ya kammala kafin yadawo saudiya
Saboda yaba son yafita ya shiga don ganin cewa shima ya kafa nasa company na,urar sadarwa a kasahen bakaken fata,
Ga damar tasamu gare shi don komai da yake bukata yanzu yasa mu
Sai gashi kuma wani fanni da yake gani na farin cikin sa ya gushe masa a lokaci daya,
Yaso ace wanan labarin da yasa mu na kammaluwar company sa fadima ta kasar saudiya a,yi gagarumin walima ,
Sai gashi komai ya tsaya mai cikin lokaci guda,
Duk yadda Almustapha yaso su ci gabada aiwatar da aiyukan su hakan bai samu ba saboda yarasa gane kan shugaban nashi sam,
Don haka dole yagaji ya kyale shi, har yaga farincikin sheriff din
Jin labarin cewa da akayi natafi kasar Nigeria yasa suka ga dan sasauci ga sheriffudeen nasu,
Yau ma kamar kullun Sheriff ne ke jar motar da kan shi, zuwa
Haram Saboda hakan da bi,ar sa ce dama, indai har yana a cikin gari duk ranar jumma,a ,
A massallaci mai girma yake yini sai dare yake dawo wa gida bayan ya idar da sallah isha,i
Zaune yake inda yasaba zama don yafi zama a kofar Sayidina umar A,s,w,,,
Yana dawo wa daga dawa fi sai yadan fito waje don yadan kewaya,
Wata yar karamar yatinya ce yagani yar takari ana ta faman yin artabu da ita da wasu mazan larabawa
Sungane cewa yariyar ba nakassa,sa bace dabara ce kawai ta neman kudi yasa ta daure hannu ta baya tankar wata musaka ,
Sun kewaye ta sai dangwarar ta sukeyi suna mata ihu
Yariyar nata famar kuka a tsakiyar su, tausayi taba sheriff
Bai san lokacin da ya je gurin yadinga ba wa mutanen hakkuri ba
Saboda ganinta yasa ya tuna da fadima a lokacin da take irin wanan harkan ta yawon bara don naimar wa hjy abin duniya,
Sai gashi duk wahalar da hjy tasa diyan mutane yi, an wayi gari daga karshe komai bata tsira da shi ba,
A wahalce ta koma gida da dinbin ciwon zuciyar da takwasa a sanadiyar damfar ta da akayi kashi kashi akasar saudiyar,
Tausayin yariyar ya kara kama sheriff din yakara kutsawa cikin jama,ar ya dinga ba su hakkuri
Kallon da sukai mai suka gane, cewa bawai tare da ita yake ba
Balle ya yaudare su iya kadai kila don suna launin fata guda ne yake son ceton ta,
Hakuri sukayi suka kyale yarinyar kowa ya watse kudi ya ciro daga aljihun shi yamika mata yace ta kaiwa shugaban ta,
Yatafi yin abinda yafito da shi daga cikin massalaci ran shi a bace
Yana tir da Allah waddai da masu dauko yan hara kanani hakan nan zuwa bautar wa da sunan wai neman kudi,
Arziki idan Allah ya nufe ka dayinta koda a cikin ramin kura kake sai kayi shi,
Har dare sheriff na cikin massallaci yana rokon Allah sauki da kuma yiwa fadima fatar sauka lafiya
Yana mai rokon Allah da yaba su zuria, mai albarka,
A hanyar shi ta komawa gida ne daddare ya dinga ganin matan takari a gefen titi suna boye boye wai suna gudun yan bagaladi su gansu, su kama su,
Kowace da kayar saidawa a gefenta wasu kuma sun rike a hannu suna nunawa mutane masu wucewa,
Ya girgiza kanshi cikin takaici, ya natir da Allah waddai da masu irin wanan halin kwadan,,,
Koda yadawo gida duk a gajiye yake saboda tun safe da ya karya bai kara cin komai a yinin yau ba,
Sako yasamu daga doctor kamal cewa su shirya zuwa wani sati sutafi Nigeria
Ba karamin dadin hakan yaji ba don dama duk hakkurin shi yaso karewa ga jiran su,
Tundaga wanan ranar ya, fara shirin tafiya Nigeria,
Shirin da bakowa yasan irin tanadin da yayi mata ba,
Sai dai abinda ke damun sheriff a zuciyar shi ita ce
Shin a Nigeria a ina ne zai je nemar fadima,
Sanin dayi cewa kida a cikin garin kano take abu ne mai wuya kafin yagane ta,
Tau yanzu shin ya ya zai yi, waye ya kamata ya fara tambayar inda zai zakulo Fatima a cikin Nigeria,
Maman umar ce ta fado mai a rai don haka washe gari itace yafara tambayar ko tasan garin da fadima take a Nigeria,
Tace wallahi duk zaman su da fadima bata taba sani ko yar wani gari bace,
Tace ai ita ta dauka cewa ko yar garin kano ce ita,
Jin dayayi cewa bazai gane komai a gurin ta ba yasa shi sallamar ta,
Tunane yake tayi to yanzu gurin waya kamata ya binciki labarinta,
Duk wani gurin da yakamata yatafi har gurin hjy laila yatafi ,
Itama dai ce mai tayi wallahi haduwar su da hjyar mu a nan saudiyace kawai bawai sun san juna bane dama,
Tundaga wanan lokacin yakara yin tir da Allah waddai da masu hali irin nasu hjy,
Yana mamaki taya mutum zai shigo cikin duniya batare d yabar wata sheda da za,a iya gane cewa ga asalin mutum ba,
Duk wanda yashigo cikin duniya indai bahaushe, ne saidai yace ai daga kano yake,
Yakara jan dogon tsaki yakara karkata motar shi zuwa tsohon uguwar da muka zauna kafin mu dawo gidan shi,
Ga mamakin shi duk bakin fuska ne agurin duk wani bayani da ya yi a gamay da mu ba wacce ta gane mu, daga cikin su,
Haka yadawo gida ga gajiya ga bacin rai duk atare da shi,
Bayan kamar kwana uku da yawon nai manta da yaketi bai gane komai ba , yasa yafara shiga cikin wani sabon damuwa,,
Yau yana zaune da dare bayan ya gama komai,
Cikin rashi ba wani dafi a tare dashi,
Salim ne ya kira shi dan su gaisa da yayan nashi,
Inda yake tambayar shi ko anji labarin fadima din,
Cikin rashi wallawala yace mai tana Nigeria saidai yarasa ko a wani gari take a can din,
Salim yace yatam bayi Amal ko tasan inda nake kasancewa zaman da mukayi tare da kuma irin shakuwar da ke tsakanin mu,
Sheriff yaji dadin wanan shawar so sai don shi sam ya manta da zancen tambayar Amal,
Kiran Amal din yayi bayan yar vaisuwar da sukayi ne
Itama din taje tambayar shi labarin fadima ya sheda mata cewa tana nan a Nigeria
Saidai bai san a kowani state take ba, kuma duk yatambaya amma ba,a samu wanda yasan garin su ba,
Shiru tayi a lokacin tana tuna wani hirar da muka tabayi da ita,
A likacinda muke kallon lambobin da yan makaran tar su suka bata,
Inda naga sunar wata yar class dinsu na nace mata akan wai sunan yar garn mu ce
Nace mata sai ta buga min wayar ta muji ko tasan iyayyena,
Duk iya buga wayar da mukayi bamuyi sa,a mai lanbar wayan ta dauka ba,
Tun ina tambayar ta akan tabuga min idan mun buga ba mu samu yasa har uka daina
Shirun da sheriff yaji tayi ne yasa yace mata ya, naji kin shiru Amal,
Nan tadan bashi wanan labarin a takaice,
Cikin zakuwa yace mata may ye sunar yariyar da nake son takira min a lokacin wace nake ganu kamar yar garin mu ce,
Tace mai murja dogon daji,
Yakara maimaita sunar yace murja dogon daji,
Dogon daji a wani state yake tace gaskiya brother ban sani ba wallahi,
Amma dai a lokacin ita wanan murja din a kano take zaune,
Shiru yayi yana nazari ko ba komai yasan cewa zai dan samu wani dan aarin haske a wanan labarin, insha Allah,
Amal tai sallama dashi akan cewa ita ma zata kara kokartawa ko zata samu layin wanan murja din,
Yai mata godiya so sai kamar ance mai ai an gane garin da nake ne ma ko,
Duk wani bincike yabar shi ahannu bashir kafin su shigo kasar Nigeria din
Bashir din yai mai alkawari ya kwantar da hankalin shi insha Allah indai har a cikin kasar Nigeria nake za,a gane inda nake,,,,,,,,
Chapter 109 · 0% Book details