← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 139

Sashe 44

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Satin mu biyu muna cikin wanan sintirin zuwa asibiti da gida,
Inda ummi ke jiyan jikinta,
Saidai gaskiya ba laifi jikin nata yayi sauki sosai
Don yanzu har ummi na iya tashi mudan yawata cikin asibitin da ita,
Shakuwa sosai ya shiga tsakani na da Amal da Salim,
Saboda yawan zaman da mukeyi wuri guda, da su,
Sai ya kasan ce kamar mun san junan mu da ma ,har ina jin dadin su fiye da zaman da muka danyi da su jamila da mairo da suka zo kwanaki
Duk da nasan cewa Amal ta girmay ni sosai amma hakan bai hanamu zama guri guda ba da ita,
Muna mu,amula kamar kawaye,
Har tafiya Sheriff din mu yayi zuwa Riyadh yin wani aiki na musan man da yataso mai shi da mustapha suka tafi,
Nice yabarwa kula da duk wani lalura na asibitin
Har zuwa lokacin da suka dawo daga tafiyan
Tafiyan da kusan itace tafiyan da ta zama makowa nagidan alheri nan gaba,
Don ko Sheriff din mu yasamu cigaba sosai don yanzu ya samu sa hannu a kusan mafi yawan company tatar man fetur ta kasa,saudiya,
Saboda kasan cewar shi kwararen engineering da suka sani
Saboda suna ganin cewa zai iya barin kasan any time daga yanzu saboda hada hannu da suka ga yayi da company Abu Abdallah dake Dubai,
Cikin dare ya iso garin don haka direct asibiti suka nufa,
Suna iso wa lokacin su Amal na waje suna shan iska,
Nikuma ina tsaye kanta ina kokarin hada mata ruwan shayi,
Jin anyi yasa na waiga inga ko waye don nadauka ko Amal ce
Sheriff ne sai su almustapha dake binshi abaya,
Gurin mahaifiyar nashi ya nufa direct tana zaune saman gadon asibitin jikin ta yanuna alamar tasa mu lafiya sosai,
Mun mai sannu da zuwa inda yake ansa muna cikin muryan shi maikama da yanajin kasala ko yaushe,,,
Da kyat yake magana mai karfi don in kaji muryan sheriff to ta baci,rai ya gani tare da mutun ,,,
Waje nafita batare da sanin kowa ba don in dan basu wuri su dan zanta, shi da yan uwan shi don kusan nice kwai bare,,a cikin su,,,
A samane dakin da aka kwantar da ummi yake, don haka waje nafito, nadan tsaya,,,
Daga sama inda nake tsaye ina kallon ina iya hangen katon agogon nan dake mane a kofar shiga masallacin ka,aba,
Wanda duk inda kake cikin garin makkah za ka iya ganin shi
mutanen dake shige da fice cikin kofar asibitin, nake dan kallo jefi jefi,
A zuciya na kuma ina, Tausayin yadda naga sheriff ya,damu da mahaifiyar shi ne yakamani,
Don nasan cewa idan yai wanan irin tafiyan yadawo bai fita ko ina har wajen kwana biyu,
Yana gida yana hutawa saboda gajiya
Saidai in rana,kun ya dace da jumma,a a ne acikin ,, shi,,,, Amma yau sai gashi direct asibitin yanufa don gani mahaifiyar shi,,,,
Ya shiga yaga ni ,Yana,Ganin jikin ummin yayi sauki sosai yasa shi fitowa daniyar komawa gida, don yadan huta ma ranshi kadan,,
Turus yayi daga bakin kofar dakin lokacin da fito,
Don, yaga fadima tsaye wace hankalinta na ga kallon waje saidai kuma hawaye take gogewa a fuskanta
Wace ita kadai ce tsaye a wajen,,
A,hankali yatako zuwa kusa da inda take yadafa karfen dake gaban su, yace mata lafiya,
Kaduwa tayi duk jikinta sai yakama rawa saboda jin muryan da tayi na bazata, alokacin,
Kara tambayar ta yayi ko may take ma kuka hakana,
Cikin daburcewa tace mai ba,kuka takeyi ba abune ya fada mata a idon ta,
Bawai ya yarda da ansar data bashi bane kawai ya barta ne don yasan bazai samu ansa ba, a lokacin,

Nafisa ce zaune a falo tana waya ga Tufan da Anabi, aje agabanta sai madarar kwali wanda kwalin yasha rabar sanyin, friged ,da ke aje gefe guda tare da cup,
Waya take yi a,binta hankali kwance tana yi tana tsunkar Anabi din tana kadawa baki,
Sautin kidan yan kasar sudan ya tashi a cikin tv, dake man ne a falon, a hankali,
Kafarta guda saman dan stol din tangaran da ke falon
Har ya shigo falon yakare mata kallon Allah waddai,ya hau sama bata ankara da shi ba,
Sai gab da zai shiga dakin shi taga wulgawan shi,

Cikin sauri ta tashi ta rufa mai baya ,
Tana shiga ta iske yana na balle butur din rigarshi yana son shiga wanka,
Ta bayan shi tazo ta rugumay shi tana sun,sunar shi,
Batare da yace mata komai ba yadan juya ta kadan ya wuce zuwa bayi,
Ido tabishi dashi tare da mamakin wai shi wani irin mutum ne haka,
Sam mace bata agaban shi,
Kwanan shi kusan uku baya gari yanzu kuma da yadawo gashi ya nuna mata bata a gaban shi,
Zaunawa tayi tana jiran shi ya fito daga bayin,
Daure da rigar wanka yafito ajikin shi ga mamakin shi sai yaga Nafisa kwance rub da ciki, saman gadon shi tana dan daga kafar ta da ta mayar baya, a hankali sai hannuta da take, lalatsa wayanta, dagani abinda takeyi a wayan yadauke mata hankali sosai,
Wardrop ya nufa ya ciro wata jallabiya mai ruwan A,she,colour yasa
daidai yana zura rigar ta taso daniyar rugumar shi ,,
Dakatar da ita yayi cikin tsawa, yakama hanyar fita dakin,
Binshi tayi abaya tana fadin walahi ita tagaji da wanan halin ,
May wai yake nufi da ita ne ma, da zai dinga mata wanan wulakancin ita yau tana bukatar shi,,,,,
Daidai lokacin mukayi, Ido hudu dashi kuma a,daidai lokacin da take wanan furucin nata,
Ji yayi kamar ya nutse a kasa don kunya,
Saidai kuma ya basar da zancen nats kamar ma bada shi takeyi ba,,,
Ita ko bata daina ba sai kara ci gaba da fadin kalmar da bata dace ba da takeyi,,,
Takardan da muka dawo dashi wanda zai je yayi filling, gobe akan gwajin da za,ai wa ummi na karshe,,,,
Na mika mai gami da juyawa da sauri, don ganin irin halin da na riske su ,.
Dakatar dani yayi don jin bayanin abinda takardan ya kunsa,,,
Batare da bata lokaci ba nai mai bayanin takardan a gurguje don jin irin hucin da Nafisat ke yi a bayana kamar wata zakanya,
Da sauri sauri na,sauko saman step din don ji nake kamar zata biyo ni a bayana,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
24/10/2017, 1:50:13 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣1⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,

Tun karfebakwai na,safe muke asibiti don yaune gwajin karshe da za,ayi wa ummi,
Kuma ance ya kasance muna wurin kafin a shiga da ita
Saboda zasu fitar da result din abin da yake damun ta
sosai, hankalin mu yatashi jin cewa ya kasance suna gurin ,
Anshiga da ita wani dan daki da zasu sa mutun cikin einjin don awo,
Muna waje tsa tsaye dukan mu cikin da muwa saboda bamusan ko wani irin saka mako zamu samu ba,
Shehi da sherif din mu sai addu,a suke yi daga inda suke tsatsaye,
Ina gefe tsaye bakin kofa, sai Amal da ke daidai inda nake tsaye ta dan zauna Salim kuma ya na daga waje zaune,,cikin zulumi,,
Jin karan bude kofar da akayi ne yasa hankalin mu duk koma gurin, da aka bude kofan
Wani, Dan likitan balaraben yafito yana mai cire kayan da yayi aikin da shi
Ummi ce aka garo ta kamar matatta, babu ko alamar ta na motsi ko kadan,,,,,,,
Aiko muna ganin haka muka bi bayan su da sauri, , cikin tashin hankali
Kwance take saman gado asibtin inda nunfashin ta ke tafiya a hankali
Wanda zaka gane hakane a jikin dan abin nuna nufashin dake mane kusa bango, gefen kanta,
Dakin yayi tsit ,ba wani mai kwakwaran motsi cikin, sai karan fanka dake tashi da sauran na,urorin
Waje na sulale ba wanda yasani nakoma narike karfen da ke saiti da dakin mu,
Bansan lokacin da na fara hawaye ba,daga haka har nadinga kuka wiwi ni kadai a waje,,,
Bakomai yasani kuka ba sai ganin halin da ummi ke ciki duk da gatan da aka mata,,
Sai kawai tunanen Inna da ke yawan damuna kwanan nan, yadawo min sabo
Ganin da nayi zuri,an ummi,duk sun kewaye ta cikin damuwa da tashi hankali,
To inda Inna na ce yaya zatayi,
Sai tuna ne ko cikin wani hali take ciki yanzu haka,
Idan ma tana cikin damuwa ne ba wanda, ko wani rashi lafiya saidai hafsat tayi ta kokari,
Ita daya batare da ni ba,
Kenan ni bazan samu ladan da "ya" ya ke samu wurin iyayen su ba
Hakan ke sa duk naga babba ina kokarin tausaya mai,
Don nasan cewa nima inna na tana can tana bukatar taimako
don hafsat ba,zata iya ba ita kadai,
Chapter 44 · 0% Book details