← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 139

Sashe 113

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau tunda safe da na tashi sai kawai naji raina ya na baci don haka ba wani maganar kirki nakeyi ba,
Dama mariyace abokiyar zancen nawa sai ko innar mu da muke yawan zama tare, duk da wani lokaci Tumba takan shigo gidan mu hira wurin innar mu ,
Amma ni sam har yanzu ban sake jikina da ita ba sam don matar batai min ba,
Saboda mariya ta ji cewa wai zuwa takeyi dan taga ko wani irin launin da zan haifa,
Saboda tagane cewa dan larabawane ko bakar fata,,
Don taji dadin zuwa ta yada a gari, don gulma
Ganin da mariya tai min yau, shiru shiru ne yasa ita ma baitai wani damuwa na da surutu ba,
Bayan mun idar da sallah azahar ne innar mu ke ce min indan kokarta in tashi muje mu diba lafiyan kawu salihu
Wanda yai fama da gudawa yan kwanakin nan,
Duk da ba son fitar nakeyi ba amma ban iya cewa inna mu ban jin dadi jikina, yau, haka na daure na fita
Nashirya nida mariya muka fita, zuwa gidan kawu salihu,
A kan hanyar mune muka hadu da musa mijin hafsi, tare da malam Basiru,
Da alamar gidan kawu suka fito su ma don yar kwarkwadan da zata sada mu da gidan kawu ne muka hade da su,
Cikin girmamawa malam Basiru ya gaishe mu,
Sai kawai musa yace amma dai Basiru anyi mutumin kawai ,,,
Karasa wacce zaka duka ka gaida sai wacce ta fito yawon bariki,
Malam basiru ya dauka da farko ko wasa ne musa ke muna,
Saida yaji maganar da musa ya ci gaba da fada min ne, yagane cewa ba wasa bane wanan zance, ta shi,
Musa yaci gaba da fadin,
Don isa ma har yawon nuna sheda takewa mutane a cikin gari,
Ni wallahi su baba ma sun cuce ni da suka hana inturo masu yar uwar su,
Tun batazo nima watarana ta haifa min mugun iri a gida ba,,
Idan mace tana jin cewa kudin yawon duniyar ta na iya ruda musa ne wallahi tayi karya,
Dan ban ga wanin abin arzikin da aka zobda shi duk wanan uban dadewar, da akayi a uwar duniya,
Yai wata yar dariya irin ta yan iska, yace,
Dan musan gaskiyar komai wallahi, duk gumama ne aka tsira da shi, kawai,
Mariya ce ta,yi kokarin tsayawa dan ta bashi ansa
Duk da na, hana
mata hakan cikin tsawa hakan bai hana ta cewa idan baka sako hafsi ba yau daga gidan ka musa lalai uwar ka da zina ta haife ka,
Kokarin shirin dukan ta yayi saida malam Basiru ya tare shi ya ce mai baka da gaskiya musa,
Don dai yaran nan basu ce muna komai ba banda gaisuwa,
Malam basiru ya juyo inda muke yana mai bamu hakkuri,
Nasamu naja mariya muka shige gidan kawun mu
Mariya tana ta bambamin ta,
Jin muryanta da kawu yayi ne yasa su fitowa don jin komai ke faruwa,
Nan mariya ta kwashe komai ya faru ta fadawa kawu, salihu,
Kawu ranshi ya baci so sai yace aiko musa zaka ji kunya wallahi,
Dan daukar alhakin wanan yariyar da kukeyi a garin nan yai yawa wallahi don nagane cewa bakomai bane hassada ne yakawo hakan
Saboda kawai anga cewa yar kulu da yaranta Allah ya rufa masu asiri,
Bayan mun gaisa da kuwun mu wanda nasamu da kyat ya hakkura yai shiru, da fadan da yakeyi da musa,
Dan yace sai yai karar musa gurin maigari akan irin wulakancin da yake min,
Bawai wani dadewa mukayi ba agidan nakawu sai mukayi sallama da su mukabar gidan,kawu salihu
Don mariya na son zuwa gaida wata kawarta da bata da lafiya,
Saboda nasan yariyar sosai tana yawan zuwa gaida ni ko kuma ta dauki Aisha zuwa gidan su tai mata kitso har da kumshi,
A gidan su yariyar nasamu taron arziki sosai shine gida na hudu da nataba shiga tunda nazo dogon daji,
Gidan mu gidan kawu salihu, saiko gidan su hafsi inda akai muna mugun wulakanci saboda kawai hassada,,,,

🐎ZEEE MAKAWA
[12/3, 9:40 PM] ‪+234 706 078 6258‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣5⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,

A, jere motocin suka gan gara cikin garin na dogon daji lokaci guda,
Duk wani wanda waje a lokacin yaga shigowar su cikin garin,
Wasu mutane ne maza mutum biyu ke tafi a gefen hanya gudan mutumin yana ta faman sababi ,da alamar fada yakeyi,
Motar da security ke cikine yadan tsaya a gaban mutanen biyu dan tambaya,
Bayan sallama da sukai masu gudan ya karba masu ne sai na cikin motar yake tambayar su dan Allah suna tambayar gidan mai gari ne,
Kwatace malam Basiru yai masu na inda zasu bi zuwa gaidan mai gari,
Gefe suka dan rabewa motacin don su wuce, sai dai duk suna bin motocin da kallo
Ta yadda za,su iya ganin wa,yanda ke cikin motar zaune,
Mota tabiyu ce tafi daukar hankalin musa so sai,
Yace kai mutumi kaga wani hadaden guy cikin wanan motar da ganin shi shege, naira ta zauna mai boko ya ratsa ko ina,
Har motocin suka shige kwanar gidan mai gari suna tsaye suna masu kallon kurullah
Basiru yace kila wasu jami,an vwaunatine suka shigo yin wani aiki,
Sai musa yace ka ko ga wanan motar ta bayan da alamar kaya ta dauko acikin ta,
Kawai gara mu isa kada aba mu labari,
Suka bi bayan motocin cikin sauri kamar zasu tashi sama,
Duk wanda yaga motar sai shima yabi don zuwa ganin ko may ke faru ,
Irin dai yadda kauye ke samun abin gulma duk akewaye,
Bayan security sun fito sukai saurin shiga wurin mai gari don naiman isa tare da jagorar malam illa,
Batare da bata wani lokaci ba fadawar maigari suka gyara masu guri zama,
Nan da nan mai gari yasa akawo masu ruwa mai sanyi da abin sha na gwangwani,
Inda aka masu masauki kafin suga maigari aji abinda yakawo su garin
Sallah suka fara gabatar wa,tukun acikin jam,i
Suna gama sallah saiga wasu yara sun shigo da furar shimkafa yaji nono da kan kara
Wanan irin taron da maigari yasa akai masu duk da bai san ko su suwaye ba,
Yasa sunji dadin hakan gaba dayan su ,,,
Cikin zuciyar Sheriff yace yanzu yafara ganin inda nadauko sanin darajan mutane,
Iso akai masu har cikin zauren maigari inda securities suka tsaya wajan zauren,
Sauran jama,an gari duk suna daga gefe sunyi cirko cirko dan jin ko wani irin sako aka zo dashi,
Malam illa ne yafara yiwa mai gari bayan dan abinda yasani na cewa daga Abuja yazo dasu don suna cigiyar garin shine yai masu jagora,
Bayan maigari yai masu barka da zuwa ne sai Shehi ya dauki zancen da cewa mai gari,
Lokacin ne Kawu salihu yazo wajen da niyar karar musa wurin maigari don sherin da suke kulla ma fadima yai yawa,
Kawu na zama daidai lokacin Shehi yaci gada fadin,
Mun shigo wanan garin ne a saka makon nemar wata yarinya da mukazo
Wace muke zaton cewa yar wanan yakin ce daga saudiya ta fito batare da sanin mijin ta ba lokacin da ta bar saudiya saboda yan wasu dalili lai nata,
Kafin Shehi yaci gaba da bayani, sai kawai muryan
Kawu Salihu ya cabe maganar yace ko fadima, cikin razana Sheriff da sauran suka shakka babu itace,
Ai sai kawai wuri yadauki salati,
Inda har nawaje suka shiga leken ko may ke faruwa da har ake salati haka,
Saida wurin yadan natsu ne maigari yace wanene mijin nata cikin mamaki
Da sauri Bashir ya nuna Sheriffudeen da hannun shi,
Cikin jin kunya Sheriff ya dan noke kan shi kasa don nauyi da kunya da suka kama shi a lokacin,
Maigari yace ma wani daga cikin mutanen shi ya tashi Sheriff yadawo nan,
Kawu salihu da sauran jama,a suka dauki murna da kuma shewa kamar yadda dattawa kan yi indan sunji dadin abu,
Kawu ya ce akan zancen ta ne nazo wanan gurin yanzu wallahi alheri ne ke kirana ban sani ba,
Ai, nan da nan maigari ya nuna masu kawu a matsayin kawuna kuma uba na dan shine mai kula da duk wani lalurar mu,
Kasancewa uban mu baida rai tun muna yan kana,na,
Gaida kawu suka karayi cikin ladabi,
Wani bafade maigari ne yadaga murya sama dan sauran mutanen dake waje suji saboda leken da suke tayi ,daga waje,
Yace Allahu akabar zato ko zunubi ne danko yau Allah ya wanke yar kulu da diyar ta fadima ,
Allah yakawo mijinta uban cikin ta har gida,
Yau zargi yakare ga munahukai yan hana ruwa gudu,
Ai kafin ace kwabo wajen fadar mai gari yadauki zancen cewa mijin fadima yazo daga saudiya
Wa, Sukuma su ce kila dai sheri nayi aka biyo ni daga saudiya,
Amma ina fadima ina wa yan nan mutanen haka,
Sun dai boyene, kawai,
Kai mutum baka iya sa wallahi, sai Allah
Batare da bata lokaciba maigari yasa a,kaisu gidan mu dan su tabbatar ko ni ce,
Chapter 113 · 0% Book details