← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 139

Sashe 63

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakina na fada tunda mukazo nashige abina nafada bayi nai wanka nadauro alwala,
Bayan na sallamay sallah na nadan zaina gurin ina dan tunane,
Daga nan natashi don inje ingaida hajiyan mu da su yumma, tunda nazo basu zo suntare ni ba,
A hankali na ke tafiya cikin wani dogon riga mai kama da silk ina tafiya yana shaking,
Ina zuwa sashen dakunar su sai nai turus, wuri guda ganin dakunan nasu duk arurufe suke, ba alamar akwai mutane aciki,
Da saurina karasa har kofan dakunan nasu sai ga ,alamar andade ba,a cikin daku nan don duk wurin yayi dan datti da yanan gizo
Hakan bai isheni shedaba saida nadan tura kofan inji ko abude suke,
Gabana yaba da dam dam dam,
Cikin wani irin sauri nake tafiya kamar zan tashi sama, don sauri,
Tunane nakeyi azuciya ina hajiyan mu da su yumma, ina yan uwana, ina gatana ,
A falo mukayi kicibis da sheriff shida Salim ganin da yai min cikin tashin hankali kuma yasan daga inda nafito,
Cikin daga muryan da bantaba yi ba agabanshi yau nai magana da larabci mutanen akbass nake magana cikin sauri sauri nace ina hajiyana da yan uwana suke,
Ido ya kura min kamar wanda ba zaiyi min magana ba,
Sa can yai magana cikin murya mai taushi fa natsuwa yake ce min
Shine gaisuwar da zan mai kokuwa shine karatun da nakoyo,
Sai alokacin nadan sami nadan yi kokarin natsa kaina guri guda,
Nagane cewa ban ma gaisai dashi ba, sam na ma kasa ganin cewa yanzu ya iso gidan daga tafiyan da yace yayi,,
Dakin shi ya haura sama batare da yakara yin wani magana ba,
Wurin Amal natafi tana zaune tana gyara kayanta, cikin jakar hannunta,
Ina shiga na fada jikin ta ina wani irin kuka mai gumza,
Duk hankalin Amal din sai yatashi, saboda ganin irin kukan da nakeyi
Da kyat tasamu tadan lalashe ni nadan tsagaita kukan nawa,
A natse take tambayana komay ke faruwa nakwashe abinda nagani gurin dakunan nasu nafada mata,
Karazancen da cewa kodai yan bagaladi sunzo sun kama su ne ba,afadamin ba,
Sai kuma nakara shige mata cikin jikinta ina wani irin kuka mai tsuma rai da zuciyan bawa,
Har maman su Umar saida ta iso dakin don jin ko mai ke faru ne haka,
Amal tadan dago min kai tace indan saurareta inji dan Allah,
Jin danayi tace dan Allah yasa nadan tsagaitata kukan nawa,
Ina saurarenta, tace min fadima kinsan dai duk inda suke yayan mu yasani ko , kai nadan kada alamar eh,
Tace kuma dai kinsan bazai bari ai masu wulakanci ba ko,
Kallonta nakeyi ina naxarin zancenta a hankali,
Ganin da tayi nadan tsagaita kukan yasa ta fara share min hawayena da hannun ta a hankali,
Bata barni ba saida taga nasamu dan natsuwa, tukun sanan tayarda naje daki na
Ranan ko abinci banci ba hakana nasamu guri nadan kwanta don indan samu natsuwa,
Tunda na kwanta ban tashi ba sai cikin dare, nafarka, natashi, nadauro alwala, nazo nayi nafila raka,a hudu kamar kulun
Saida gari ya waye san nan na tashi a hankali naje na gyara jikina tsab nafito cikin shigar wasu jajayen, da dan ratsinyau
ki,baki kayan yan na mutanen Japanese ne mata, rigan yanada dan budewa a kasan shi sai dan guntun hannu daidai, gwiwar hannu,
Bakin gyale nasamu nadan daure kaina dashi,
A hankali na ke tafiya kamar banson taka kasa, fito wa nayi zuwa falon gidan
Don indan samu abinda zan danci saboda tun jiya ban ci komai ba, yunwa nake ji yau
Zaune suke shida Salim a dinning table din suna cin abinci su hankalo kwance,
Ganin da nayi masu shi yasa nai niyar komawa daki sai kuma wata zuciya tace min ban gaida sheriff ba,

Takawa nayi har inda yake nadan karasa cikin ladabi na gaishe shi nai mai yaya hanya,
Salim yai min tayin abinci, yace min ya dauka ko nima barcin nakeyi don baiji motsina ba,
Batare da nace mai komai ba nawuce kawai zuwa cikin kitchen inda na saba diban abincin mu,
Saboda gaskiya ban iya zama inci abinci agaban sheriff din mu, yana kallo nha
Har nakai kofar shiga side din da zai sada ni da kitchen din sai naji muryam sheriff, cikin harshen larabci yana ce min inzo, a hankali nadawo har inda suke kujera dake gefen Salim ya gwada min in zauna sama,
Sai naji wani dummm narasa yadda zanyi sai naga ya mike yabar gurin yana waya,
Nawaiga a hankali sai naga yabar falon gaba daya, hakan yasa naji dadin zama nazauna naci abinci na hankali kwance,
Saidai zuciya cikie take fam da tunanen inda yan uwana sukaje,
Batare da sani wani
Ina tashi wurin maman Umar na nufa don inji komay mafitar zancen,,,
Itama dai hakkuri tabani tace min in bari zata bincika min a hankali,
Amma dai duk ida suke shariff yasani ai
Kusan kwdayataso baice min komai ba nikuma cikin damuwa nake sosai
Ranan da muka cika kwana biyu ne ina zaune a daki na ina nazarin a kan wani sabon computer da yafito sai naji anturo kofar dakin na a hankali,
Nadauko ko Aisha ce sai dai kamshin turaren da ya ruda min hanci yafada min kowaye
Cikin shigar kananin kaya yake yau kayan sunyi mugun karban jikin shi,,
In ganin shi sai nayi niyar saukowa daga saman gadon ,
Hannu yadaga min a hankali yai min nuni da inzauna inda nake,
Gefen mirrow dakin yaje yadan tsaya yajingina jikin shi da mirrow
Hannu shi cikin aljihun Kafan shi na harde cikin guda,
Ido yadan zuba min kusan na minti biyu sai yakira suna na ahankali, nakarba,
Ina mai dan dago kaina shima ahankali nadan kalle gefen da yake sai na sauke idon nawa
Yace min wani irin tambaya kikai min shekaran jiya,
Shiru nayi ba ansa yakara ce min haka yakamata kiyi tambaya,
Ko kinga cewa hjy zata bace a gida nane,
Karshe yace hjy da sauran yaranta sun koma gida Nigeria, dammm dammm gaba na ya harba
Wanan karon kallon shi nakeyi cikin ido sosai saidai na kasa dole na sauke kwayar idona da yacika fam da hawaye,
Na maimata maganar nace sun koma Nigeria,
Yaushe, kuma ta yaya san nan nifa ,
Ni may yasa suka wuce suka barni, sai kawai nasa kuka mai bala,in tsuma zuciya,
Ganin da yayi nafara kukan yasa shi fita dakin cikin sauri, duk da yaso son yai min bayani komai amma ina bai iya tsaya yanajin kukan mace a gaban shi hakana,,
Nai kukana har saida nagaji banda wani bayani dole na hakkura na maida lamari na ga Allah,
Sati biyu zamu yi a makka don haka muna garin sheriff ya wuce zuwa Nigeria wurin wani aiki dayataso mai akan sabon kamfanin su,
Don haka mu kadai yabari a gidan,,
Ganin da nayi bai gari yasa na shirya zuwa masfala wurin hajiya laila, don inji bayanin abinda ke faruwa tunda na fuskanci sheriff baida niyar fada min komai,,,
Ina zuwa sai nai rashin sa,a ance hjy laila ta koma birnin Riyadh da zama
Haka nadawo gida hankalina tashe, banda wani sukuni ko kuzari tare da ni ko kadan
Maman su umar ne nasamu take dan kwantar min da hankali yanzu,
Saiko Amal wace take iya kokarinta wurin kula da al,amarina ,

Saidaga baya na fahinci cewa aziza ba ,a garin take da zama ba ashe wai a Dubai take zama don a can take sana,a har tagamu da sherrif din mu awajen wani taron yan kasuwan kasashen afirika da akayi,
Tun lokacin ta lake mai so sai, da taga gurinta ya cika,
Tana son sheriff don yayi mata kuma tana ra,ayin kudin shi ,,,
Wanan zuwan da yayi Nigeria har da batun dawowa da nafisat gidan shi yakai shi,
Nafisat zata zauna a Abujane tunda yanzu zaidinga zuwa aiki can sosai,
Ita kuma aziza zata dinga zuwa nan saudiya ko kuma shi yaje can inda take,
Ya iske kaunar shi yayan su Amal ta hai ko suna ba,ayi ba
Yai mata sha,uku na arziki ita da mijinta har su shehi da sauran yan uwa sunji dadin wanan zuwan nashi so sai,
Kamar yadda maman su Umar tai min alkawarin bincken labarin su hjy mu haka din ne ko
Saida ta binciko mai tazo min da labarin yadda maganar yake cewa hjy da su yumma sunkoma gida ne da taimakon Sheriff saboda gwaunatin saudiya tasa anata binciko mata duk inda takari suke zaune akasan
Hakan da yagani ne yasa yai masu bizan komawa gida suka koma tare da su yumma,
Saidai akwai sauran bayanin da batai min ba tadan boye min su,
Jin hakan da nayi yasa nadan ji sanyi azuciya na sosai ,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣2⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,,

Har muka kare hutun mu a makka Sheriff bai dawo ba daga tafiyan da yayi, don yace daga Nigeria zai biya kasar Italy
Mundawo madina lfy, munci gabada gudanar da karatun mu lafiya,
Bamu da wani matsalar rayuwa yanzu don koda yaushe sheriff yana turo muna da kudi
Duk da babu abinda muka rasa na rayuwa amma sai ya aiko muna da kudin nan,
Salimat tasamu ciki mai wahal da ita sosai, don kusan duk abinda taci sai ta amayar da shi,
Don haka yanzu kusan karatun mutum biyu nake yi , inyi nata inyi nawa,
Saboda gaskiya ba yabon kai ba wlh ina da gwargwadon kokarina sosai,
Shiyasa koda nake hada aiki na da na Salimat ba wai wani mugun wuya nake sha sosai ba,
Dagani har Amal muna iya kokarin mu wurin kula da ita saboda inkaga yadda ta koma sai ta baka tausayi sosai,
Ganin irin wahalar da take sha ne kuma gata gidan ita kadai ne aciki yasa mijin ta yabugo min waya cewa don Allah yana son mu taimaka mai salimat tadan dawo wurin mu ta zauna har taji dan sauki,
Chapter 63 · 0% Book details