← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 139

Sashe 87

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A falon gida muka samu kowa zaune wasu na hira wasu na kallon tv ,
Sai ummi ce zaune da casbaha a hannun ta, tana ja,
Shigowar mu yasa Aziza shiga cikin wani guntun tunane
Shin tare muka fita da sheriff ko kuwa ya akayi muka hadu,
Abin mamaki sai naga yarikide min kamar da kamar bashi bane yaga min wa yan, nan kalaman dan lokaci kadan da suka wuce,
Anty falmata ce ke min sannu da jiki, dakuma tambayana ko zan ci wani abu,
Kifin inyi magana muryan Amal ne take cewa ai don taga kowa na damuwa da ciwon ta ne shiyasa taje kara narkewa mutane,
Abarni kawai idan naji yunwa nida kaina ai zan bidi hanyar abinci,
Ummi tace mata amma Amal baki da tausayi yarinya tana fama da lalura irin haka har zakina ce a kyale ta,
Dan murmushin yake nai ma Amal kawai azuciya na kuma ina cewa ummi ta kyaleta tana da gaskiyar ta sanin da tai min bana yan zuba,,,
Maman umar takawo min fruit's masu dan sanyi da kuma lemon kwanko,
Nadanci kadan sai kuma yau naji kawai ban ra,ayin ko fruit din
Wani irin amai ne yataso min narike bakina da hannu guda da sauri nature kayan plate din gefe na fada daki, na,
Aziza ce ta tashi da sauri tabi bayana don ita azaton ta ina shirin zubar da cikin ne,
Nafito daga bandaki ke nan tafado min cikkn daki a hasale,
Cikin tashin hankali take maganar ta, fadima may kikaje kikayiwa dana,
May aka baki ki kasha kike wanan aman haka,.
Don lafiya kalau kibar gidan nan koda natashi akace min kin tafi asibiti, wai,
Tana batun kara matsowa kusa dani , ni,ko ina tsaye ina kallon ta cikin mamaki,
Muryan Sheriff ne mukaji ta bayan mu yana cewa,
Aziza cikin ki ko nawa da mamaki ta waiga inda yake tsaye tana mai kallon mamaki,
Cikin rashi, facinta, ta ke mai, kallon shi wani iri,
Ya buga mata tsawa yace may kike zaton zatayiwa cikin da ke da uban shi,
Cikon da baida uba wanda ba,a yarda dashi shine ake ma yunkurin halakawa akoda yaushe,
Yanuna ni amma ba irin wanan mai uban ba, kuma uban mutum mai tsoron Allah irina ba,
Macuci wanda zai cutawa rayuwar yariyar da bataci ba batasha ba,
Ya karaso inda nake tsaye ya kama min hannu a hankali yace min in zauna,
Za taimagana yakara daga mata hannu yace may zaki fada min
Aziza shin mugun kudurin da ki kayi niyar yi, da yar mutane ko kuwa nida kike,so ki kulin ,sheri kikeso yi min bayani,,,
Dan murmushi tayi irin na yan duniyar mata,
Ta tako har inda yake tsaye,
Itama wani irin harara ta dankara mai tace kana nufin ka gane nufina akan wanan cikin da nasa ai mata dashe ko may,
Ya buga mata tsawa yace ke dan Allah yimin shiru,
In ba haka ba yanzu in kira maki hukuma atafi da ke,
Aiko kamar ya tunzura ta, ,, matstawa tayi har gaban shi ta rike kugun ta da kyau,
Tace har yanzu ban fahinci irin butulcin da kake shirin yi min ba,
O saboda rashi tausayi Ahmad shine zaka ce wai yanzu kai ne uban wanan cikin
Saida ya dan murmusa kadan yace mata,
Aziza kin so ki cuce Allah bai yarda ba kamar kuma yadda kikaso ki cuta wa mata, ta fatima da mugun nufin ki na kudirin sai kon haihu ko ta halin kaka,
Ai idar har kina son haihuwa da kin haihu da kanki
Kiga alokacin zan san cewa ki na kaina na

Cikin nuna alamar bata fahince shi ba take maganan ta still,
Tace au kana nufin kun hada baki ne da fadima ku cuce ni,
Tobari kuji,
Sperm dinka da nawa likiti yai amfani dashi yasa ma fadima
Kaga kenan abinda ke cikkn cikin fadima nawane nida kai ,,
Ita nata wahalar kawai shine tai min rainon ciki idan ta haife in karbi baby na nagama da ita,
Idan kuma har kana da ja ga wana maganaa shirye nake da muje wurin duk wani hukuma ta duniya don ai muna sheri,
Saida sheriff yadan kallo inda nake zaune lokacin da tai kalamin ta na karshe,
Kafin wanin su yai wani zance muryan UMMI ce ke tambayar may ke faruwa ne haka,
Shiru duk kan mu ukun mukayi a lokacin,
Mamata dan kalli gefen da yake tace mai matar ka bata da lafiya kazo kuma kuna daga mata hankali haja a gabanta,

Cikin mamaki take kallon ummi ta nuna inda nake da yar yatsarta tace
Fadima ce matar Ahmad kuma,.
Saita bushe da wani irin dariya tana tafa hannayen ta,
Tace mamaki yau kuma kulin sheri ne haka wai don aimin dabaran rabani da abinda na kwallafawa rai,
To karyan ku don baku isa ba wlh,
Ganin da yayi idonta ya rufe zataima harda ummi rashin mutunci yasa shi cewa cikin tsawa get, out my friend,
Ai baka isa ba Ahmad sai naji matsayin da kuke son ku sa cikina aciki tukun,
Ummi da bata fahinci zancen ba sai take cewa Alhamdullah mata biyu da ciki lokaci guda,
Aziza takara kawai ummi kallo tace wai nida wace matar tasa,
Wanan karon falmata ce a kofa jin da sukayi fitinar yana kara yawa suka taso gaba dayan su zuwa dakin ,
Tace kina nufin kice baki san cewa fadima matar shi bace tobarima kiji don inaga ita din ta rigaki auren shi, tana mai nuna inda nake zaune,,,
Tawani kyalkyale da dariya kamar wata tababa,
Tace yau naji na gani,
Hindu ce tayi kokari ta kusa kai cikin dakin taja hannun Aziza tana fadin ki kwantar da hankalinki Aziza muji bayanin su,,,
Hindu wa yan nan mutanen suna son su raina min wayo,
Kiji fa wai cikin da nasha wuya kafin samun shi ,shine yau suke son su cuta min akan shi,
Yai dan murmushi yace mata Hindu ki barta har in bata yarda ba sai mu koma gurin likita taji da kunnen ta ko,
Cikin fushi ta fita dakin Hindu ta mara mata baya,
Adakin su take ta zirga zirga taje tadawo,
Hindu tace saida na fada maki cewa karki yarda kiyi wanan plan din da wanan yarinyar kika ce min ai baza a samu matsala komai ba ke kinyarda da ita to yanzu gashi irin abinda ta jawo maki,
Kidiba irin wahalar da mukasha, da irin kudin da muka kashe akai,
Hanna tadaga wa hindun tana hade wasu miyau masu daci tace,
Bar wanan zancen Hindu aiba zaiko sabu ba wai bindiga a ruwa,
Ni za,ai wa wanan drama din,

Da sauri ta jawo jakarta ta lalibo wayarta,
Number doctor Khan takira bayan sun gaisa take sheda mai cewa tana son su zo wurin check up da da wanan yarinyar ,
Doctor Khan yai dan shiru nawani lokaci, can yace mata,
Ai bai ma wanan yariyar komai ba saboda yarinyar nada ciki already a lokacin,
Hakan yasa baisa mata komai ba don babu zancen yin artificial insemination, ga wanda ke da ciki,
Yakare zancen da cewa ta diba prescription din da yabata tagani zata ga komai ai a rubuce,
Da sauri ta jawo jakar da tasa takardun a ciki diban farko ya nuna mata cewa ba ai min wanan dashen ba,
Ta wurgar da wayan don ta daina jin zan cen doctor Khan wanda kamar ruwan zafi yake kwararo mata a kune,
Sai a lokacin take tuna nen cewa kudin da ta tura mai na aikin tabbas bai cire ba har tanawa Hindu complain din haka,
Aiko nan da nan idonta yakoma kamar garwashin wuta,
Sun wani kade sunyi jajir
Yau ita Aziza za aiwa rainin wayo haka,
Ita Ahmad zai wa cin amana haka,
Tare da yar yarinyar da take ma daukar yar ficiciya,
Wasu irin hawayen bakin ciki suka ahiga zubo mata, daga idon ta,
Tarike kan ta da hannu biyu,tana fadi sharaf saman gadon ta,
Tashiga rusa kuka kamar wata yar karamar yarinya,
Ita Aziza za aiwa rainin hankali irin wanan babu abinda zata sa agabanta wanda bata samay shi ba,
Babu wani wanda zai mata wanan rainin hankalin ta kyale shi,
Kowaye dole ne saita dauki fansa akan wanan cin fuskan da ake shirin yi mata,
Hindu ce takara kwantar mata da hankali akan cewa ta bari,a bisu a hankalin har ta dau fansa a,kan duk wani cin amanar da Sheriff yai mata,,,,

Dan Allah kuyi hakkuri saida na gama typing tun a,round six saboda yau weekend ne ashe banyi storing ba sai ya goge kuma wlh nagaji da typing,
Pls kuyi min afuwan 👏👏👏👏👏

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣👣
7⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,
Chapter 87 · 0% Book details