← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 139

Sashe 68

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Acikon mota sheriff zaikai mu asibiti tare da Salimat da baby ta,
Amal ta mika min baby tace in zauna da ita agaban mota itada Salimat su shiga baya,
Ahankali yake tuki motar sai kira,an dake tashi nawani dan saurayin matashin balarabe,
Baby tai dan wani hirgita kadan tare da ajiyan zuciya madan sauti,
Cikin sauri sheriff yadan duko inda nake zaune da ita ,yadan kware showul din yana diban fuskan babyn
Wace ke ta sharan barci abinta,
Amal na kallon mu daga bayan mota da suke zaune, daidai lokacin ta dauke mu hoto a hanka, batare da sani na ba
Saida muka je aka diba lafiyan jariri da na uwa aka tab, batar da duk suna lafiya,
Sheriff ne da kan shi yabuga ma mijin salimat waya yasheda mai cewa salimat ta haihu,
Sunyi mamaki sosai don duk dauka akeyi ba month din haihuwanta ba ke nan,
Ba karamin kokari sheriff yayi ba saikace shi akaiwa wanan haihuwan
Satin ta biyu a saudiya mijinta yazo yadauketa zuwa Nigeria ,
Yai muna godiya sosai kafin su wuce , duk bamuso su tafi da baby Asma,u, ba wai sunan mahaifiyar mijin ta ke nan,,,

Karatun mu mukaci gaba dayi duk da bawai dogon lokaci yarage muna ba,
Saidai karatun namu sam bai hanamu yin ibadan mu ba,
Ko yaushe muna zuwa muyi sallah idan an idar da sallah mushiga muyi ziyara
Mufito wani lokaci kuma salim ne zai kwashe mu ga mota yakai mu baki,ya muyi ziyaran kaburbukan bayin Allah da sukayi sha hada,
Ina son zuwa ziyara a bakiya don ko ba komai zakaji wani karin imani nashigan ka,
Don zaka dinga gani kamar ace sahaban manzon Allah SAW dake kwace cikin wanan makabartan zasu tashi ka gansu,
Sai mutun yaji indan ana bada tarihin su kamar ace shima a wanan lokacin aka halicce shi yazaman to a cikin su,
Gurine da akayiwa security ankewaye shi da waya saidai ka tsaya ko kuma idan zaka iya hawa dutse ka,hau kaje kai masu addu,
Salim yana yawan sha,awar zuwa ziyara a bakiya, don kusan duk ranan alhamis sai yakaimu ziyara munyi masu addu,a tare yiwa kan mu ,muma fatan cikawa da kyau da imanin ubangijin mu,

Za,zaune muke duk kan mu cikin falon muna hira, kamar yadda muka saba yi indan weekend ne zama mukeyi inda mun dawo daga masallaci ayita hiran rayuwa
Yau,ma hakan ce ta kasan, da mu,
Amal ce zane a tsakiya ta magana wayanta yana a hannun ta tana dube dube,
Photo na dake cikin wayan ,sai idon ta yakai ga wanda tai muna ni da sheriff da baby Asma,u, wace muke ce ma husna,
Saida tadan tsaya taima hoton kallon tsab sanan take gwada muna,photo,
Mamaki yakamani kware daganin picture don basan lokacin da ta dauka, ba,
Idan ka gan mu a cikin photo zaka zaci cewa ko wasu ma,aurata ne nida shi,,,,
Salim yace kai dama ace wanan baby na yayan mu aida basan irin farin cikin da zaiyi, ba,
Kusan koyaushe sai yai min korafi akan yana son haihuwa , yana son yasamu baby shima,
Ace ai wanan baby shi don yace hjy tsohuwa tana yawan yimai korafi indan sun hadu,
Amal tace banga wace ke shirin haihuwa ba cikin wa yan nan yan gayun mata nashi,
Tace du matan nashi ni gaskiya basuyi min ba babu wace ta dace dashi acikin su,
Sai lokacin nasa masu baki a,zancen su, da sukeyi
Nace ,a a Amal ai aure mukaddari ne matan mutun kabarinsa,
Aiko duk matan nashi suna son shi kuma idan lokacin haihuwan su yayi ai zasu haihu komai fa dan lokaci ne,
Daga haka ban kacewa ufan ba, daga zancen nasu,
Wanan zancen yasa naji duk tausayin sheriff yakamani nai alkawri araina insha Allah zan sa shi a,addu,a ta, koyaushe,

Aziza ce zaune duk ta rikita mai lissafin shi adole sai sunje sunga likita a kasar Germany, yadibata
Saida yagama jin korafinta yadan yi murmushi yace aziza mubar ma Allah zabin sa idan lokaci yayi sai yaba mu bawai sai munje muna ta nuna rashin tawakkalin mu akai ba,
Allah da yayi mu bai manta da muba,
Ganin da yayi shima dai din yana son yaga baby shi a duniya yasa har ya amince mata
Bayan aune aunen da sukayi likita yatabbatar masu cewa lafiya lau, maigidan yake kuma ita ma din zata iya samun ciki saida akwai wani abokin shi dan kasar indiya yafishi kwarewa ta wanan fan,ni sosai,
Don haka yace suna iya zuwa su ziyarce shi,
Bayadda aziza batayi da sheriff ba amma yace shi tunda lafiya lau yake bai zuwa ko ina,
Itada hindu sukaje gani doctor Khan a indiya din bayan duk wani awo da zai mata yayi ya,kam,malla ne yake sheda mata cewa, agaskiya mahaifarta bazata iya daukar ciki ba da kanta saidai inda zata yarda ai mata artificial insemination, to ko shi din sai kila ne cikin zai iya tsaya mata,
Haka suka dawo gida cikin tashin hankali ,don tasan cewa idan ko har baza ta haihu ba , ba makawa sai sheriff ya kara wani aure tunda nafisat itama har yanzu gata can shiru ba wani labarin ciki,
In akwai abinda bata kauna shine taga Ahmad dinta, da wata mace koda ko abokiyar aikinsa ce,
A ranan tashi yi mai mita ke nan , shi mamaki ma take bashi, saboda irin mugun kishin ta,
Tun ajirgi take ta rusawa hindu kuka, hindu tai rarashin kawar nata har tagaji,
Jiki ba kwari tadawo mai a Dubai suka hadu yana ganin ta tagane cewa batai nasaran tafiyan ta ba ,
Shima dai din cikin zuciyar shi baiji dadi ba,
Saida dare bayan sun gama komai sun kwatane take mai bayanin da likita yai mata, saida ta boye mai cewa ance ko artficial insemination din bazai zama dole ya tsaya mata ba,
Tana kai karshen zance yamike har zaune daga kwancen
Yana fadin tir Subbahanallah wa,iyazu billahi
Ai wanan rashin imani ne da kuma aikin jahilci, taya za ace mutum bai imani da Allah ,
Idon shi yai ja sosai don irin masifan da yake ta balballa mata,
Yakawo mata aya da ku hadisai masu kashe jiki,, yai mata,
Rai bace sukayi barci a wanan ranan batare da kowa ya kara cewa tak ba,
Tunda safe ya shirya tafiya a ranan saboda bacin rai yabaro Dubai din zuwa saudiya,
Satin shi guda ta wuce Nigeria saboda wayan da akai mai cewa hjy tsohuwa ba lafiya sosai,

Yana zuwa yaga irin yanayin da take ciki yasa adauko ta zuwa asibitin Abuja,
Cikin ikon Allah hjya tadan samu sauki,don tasamu kulawa sosai,
Acan Abujan ma bai tsira daga fitinar nafisat ba don ita ma din so takeyi suje suyi gwajin haihuwa ita dashi don aji ko may ye matsalar,
Shi mutun ne mai kokarin fitar wa natare dashi da hakkin zaman tare,
Don haka baki zuwa ba bayan da likta yai ma su shiya tayar wa nafisat da hankali,
Inada yace masu mahaifar ta ya samu matsala drug's din da take sha yasa ba zai taba iya daukan ciki ba,
Cikin takaici suka iso gida ga kukan da nafisat ta i she, shi da shi
Suna shiga gida tazauna tai tagumi hannu bibiyu ta ta zub da hawayen bakin ciki,
Tunda ya ajeta ya fita bai dawo gidan ba sai cikin dare yadawo,
Zuciyan shi duk ta jagule mai,
Duk kan su, su,biyu kusan case din su guda ne, ba zasu iya daukar ciki dan dama azizan da yake tana kan tracings na doctor ne tukun,
Yana sa ran cewa zata iya samun ciki indan har Allah yakawo,
Hakuri nafisat ta kama bashi akan don Allah yayi hakkuri kada ya bari iyayyen ta suji wanan zan ce,
Bai samu ce mata komai ba saboda bacin rai,
Tunda safe yaje gidan Bashir don yagaida hjy tsohuwa don tace sam bata zuwa gidan nafisat ta zauna
Saboda hakane aka kaita gidan bashir din don ta zauna can
Bayan sun gaisa ne da hjy sai ga ya shigo dakin dauke da,yar diyar shi tana wasa da fuskan baban nata,
Sheriff Ahmad ya mika hannu don yadauke sai taki, zuwa, ta kara rungumay mahaifin nata,
Bashir yadan hada kai da fuskan yar yarinyar yace, baki zuwa daddy ya,dauke ki ko,
Dariya yar diyar tayi na kuyya,
Hjy dake kwance gefe tace, yanzu Alhaji karami ba zan ga zuriar ka ba , sai bayan na mutu,
Sai tadan kama kuka kamar wace akai ma wani abu,
Dakyat suka samu suka lalabata shi da bashir, har tai shiru yai mata alkawarin cewa,
Insha Allahu zata gani bama zata mutu ba sai ta yi ta goya mai zuri,an shi,
Dahaka tadanji sanyi ,sanyi tai shiru tana fadin Allah yasa Allah yasa,
Chapter 68 · 0% Book details