Sashe 73
Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tabbas wanan yarinya yakamata ta taimaka mata, badon komai sai don hakan zaifi mata sauki da rufin asiri, Ganin da tayi cewa sheriff din mu yayi barci mai nauyi yasa fito daga dakin A cikin duhu take tafiya saboda kashe duk wani haske dake falon da akayi Saboda koyi da,sunnan maikin manzo sallalahu alaihim wasallam, Sai yanzu nake jin yuwa na dan damu , dama bani abu bane abinci drink's ne nake yawan sha, da corns, Don haka na tashi nafito falon gidan don inda samu abinda zan agaza wakaina, dashi, Dayake ahankali nake tafiya na sai naji kamar ana magana kasa kasa acikin falon don haka sai nadan rage tafiya na don jin kowaye, cikin wanan uban dare, Ga mamaki na sai naji muryan mace kuma da harshen hausa take magana, Kara matsawa nayi daidai gurin da sautin ke futowa, Aziza gabana yaba da dam, May takeyi haka acikin dare koma dai may ye sirine bata son kowa yaji ta, Har zan juya sai wata zicuya tace min indan dakata inji ko da kadan ne, Murya kasa,kasa take cewa Hindu na fada maki cewa bazan samu matsalaba ga wanan yarinyar insha Allah zata yi yadda nake so, Hindu tace Aziza wanan maganar ba karamar magana bace fa, maganace da ke bukatar siri acikin ta, Kinga ko gara mufita waje can mu samo wacce zata yi muna aikin mu cikin rufin asiri batare da kowa yasanaikin Sai, Muba ta kudi mu sallame ta tayi gaba in bukata ya biya, Azizs tace hindu wanan yarinyar itace zata iya zama dai,dai da nufin mu, baki ganewa ne shiyasa, Hindu, tace kidai bari mu, mukara dibawa ko zamu samu wacce ta dace da aikin Haka sukai ta sakawa suna walwalewa a tsakanin su,, Ina labe ina jin su duk jikina yai sanyi kamar in zunduma ihu, Ban gushe daga inda nake labe ba naji motsin Aziza alamar tagama waya zata dawo, dakin su, Shan jinin jikina nayi na lafe a bango, saida tazo dai kusa da inda nake labe sai kawai taja ta tsaya dai gurin, Gabana yafadi dam don a,zatona tagan ni ne har na rufe ido na ,nasadakat kawai ta gani, Shirun da naji yasa nadan diba sai naga a she, wayan take kashe, Saida naji takon, kafarta ta wuce har ta haura sama dakin su ta rufe, Nai ajiyan zuciya, da sanda na la,laba nadauki lemu na koma daki na hankalina a tashe, Juyi nake tayi barci ya ki dauka na, sai, Tunane kawai nake saboda bansan kowa ni irin shiri ba ne zasu ai,watar, hakana, Hakana na kwana da wanan tunane cikin zuciya na sai sake sake nake tayi har gari yawaye, Tsakani na da sheriff tunda wanan abin yafaru tsakanin mu bamu kara haduwa ba, Sai na bari rana yayi nasan cewa yafita zan dan fito waje, Yau nasan cewa yatafi ma,ia,katar su ta Riyadh aiki, Don yaune ranan zuwan shi can Riyadh din sai ya kwana biyu ko uku zai dawo garin makkah, Wando da riga nasa wandon jeans baki ,mai kafar pencil sai yar wata riga da nasa wanda tsawon, rigan yatsaya min iya gwiuwa na, hannu shi ma hakana ya tsaya min, Bakin gyale na daura a kaina, sai fuskana da ban mai wani makeup ba,,, A hankali na,tako zuwa falon gidan Salim na samu zaune, yana kallon wani shirin na Arabs got talents, Sai Amal dake gefe tana waya cikin kashe murya kamar wacce batason aji may take fada, Gefen salim na zauna don muyi kallon tare, ban wani dade da zama ba, wayana yadinga tsuwar alamar kira in agaza mai, Salimat ce takirani dan ihun murna nayi don jin dadin jin ta, danayi Dauki wayan ina fadin maman As,mau nayi fushi gaskiya, Tace ,a,a haba dai fadima idan kinyi fushi dani ai ko na shige su, Nace kawai kin wuce, abinki ko ki tuna da mutane Tace fadima kin san matsalar Nigeria har kauye saida naje gashe su, wani guri babu ko services da zan kira ki, Yanzu ma mun dawo kano ne shine,nace barin kira ki mu gaisa kiji motsin diyar ki, Munyi hira sosai har ina ce mata gaskiya na matsu ta dawo walahi ina kewan ta so sai, Amal da tagama waya ta zagayo ta baya na ta fisge wayan ta shiga yiwa salimat ,sheri Karshe dai taba mu hakkuri tace muna zata dawo bada dadewa ba Insha Allah, Saida muka natsu daga dariyan salimat da muke yi ne, Sai Amal ta jefo min tambaya wai fadima lafiya bakya fitowa waje duk kwana nan, Salim dayaji tambayar Amal sai na ji yana dan gyaran murya kamar wani mai shirin yin magana, Gaba dayan mu mukai diban mu gare shi, don ji ko ganin may zai ce, Dariya yakama yi yana ce muna ya mukr kallon shi haka, Amal tace fadi dai muji may zaka ce, kada kabari a ciki ya kashe ka, kai daya, Sam ban gane mai yake nufi ba sai naji Amal nace kai dai kace ba ni nace, Aji shi a bakin ka ba ruwana, Kafin wani da cikin su yakara fadin watakalma Aziza ce tafi to daga sashen su cikin shirin fita, Daya daga cikin wasu saitin kujerun da ke can gefen mu ta zauna a saman guda, Waya takeyi tana wani murmushi tana gyara rigar da tasa da kyau, Duk hankalin mu ya gurin kallon TV da salim keyi, Amma dai gaskiya muna kallon ta ta wutsiyar idon mu, Tundai ni da na ke fargaban shirin da naga tana kokarin aiwatar wa, a boye, Muryan ta na tsinkaya cikin murmushi take magana daidai lokacin ta taso daga inda take zaune zuwa gurin da muke, Cikin murmushi take cewa fadima unguwa za mu tafi yanzu , Ahmad yace kece zaki rakani ko tana fadi tana wani kashe ido irin na yan duniya, Gaba na yadan fadi don jin abinda tace Sai kawai na tuna da abinda naji tana fadi a waya, Ganin da tayi kamar ina dan tuna ne yasa tace min ko baki son fitar ne yau, ai sai in fasa har zuwa gobe Sai mu fita ko, takalleni tana wani kashe murya Saida nadan yi ajiyan zuciya saina ce da sauri, haba, haba, Ai kawai muje barin dan sa asshifal dina a sama kawai, Nakoma daki nadauko wata sabuwar Asshifal, baka mai kyau na za saman jikina nada nan nagyara daurin dake kaina ya koma rolling sai na aza dan gyalen wanan Asshifal din saman rolling din kana gani na kasan nayo shigar mutanen musuluman kasar, Sydney Ina fitowa falon inda take jira na muka hada ido da Amal saita sakar min wani irin uban harara, Cikin larabci tace min indai bi a hankali da wanan Murmushi kawai nadan yi mata don kada aziza ta gane cewa da ita mukeyi, Yusuf driver ne zai ja mu, muna shiga mota sai tace min ince mai kada yai tuki sosai yabi da ita a hankali pls,. Haka ko yakama tuka motar a hankali yake tukin , Naima yusuf magana nace yasa muna ki,ra,an Shuriem don ina son kira,ar shi sosai,. Idanuna nadan lunshe ina sauraren kira,ar ina kuma bin shi a hankali, sai ina tuna ne a gaskiya ba abinda yakai alkur,ani dadin sauraro, Muryan Aziza naji tana cemin acikin hausa shagon, saida kayan masu kyau zamu fara zuwa idan mun gama sai mu tafi wurin gyaran jiki ,, Sabon shagon da aka bude a cikin Bin,Daewood na kai ta sainaga duk ta rude saboda kyau wurin Komai akwai acikin shi shagone tundaga sama har kasa sai inda idon ka ya tsaya, da gani, Ganin cewa danayi gamu cikin massalacin Ka,aba ai yakamata mudan yi koda nafilla raka,a biyu ne kafin mu wuce, Nace mata idan mun gama sai mu tafi muyi sallah da dawafi, ko Saida ta dafani tana murmushi tace min idan munce mu tsaya yin dawafi ai zamu makara da zuwa gurin gyaran jikin mu ko, Sororo nayi saboda mamakin ta, ga wasu can nason suzo kota halin ka,ka Allah bai basu ikon zuwa ba, ita gata tasamu har tana barin damar ta a banza, Haka nabi bayan ta da mamaki fam a cikin zuciya naita Saidai ina ta jiran inji ko zanga wani abin da yashafi maganar da naji tanayi a waya ranan Sai banji komai ba shiru,, Hakan yasani nadan sake jikina da ita Munashiga shagon kayan kyalkaylin mata, sai, tafara jidan kaya masu kyau Masu kuma tsada hatta su undies sai da muja jido su kamar hauka, Har zan shiga wani shagon saida kayan kamshi sai ta kirani, Da sauri nadawo wata riga ce mai masifar kyau irin tamu matasa yan mata, Kala kala different design masu kyau, kowani da gyale ko wani abayan hada shi mai kama da alkyabba, Cikin sha,awa tadinga gyada kai, tana, yaba kyawon kayan tana cewa wanan kan sai ku yan mata, fadima, Ina kallonta takwashi kusan guda biyar kala kala, Ina tsaye gefe ta biya kudin kayan ,mamaki kawai nakeyi irin yawan kudin da naji an ambata akan kudin da mukayi sayayya haka, Saina tuna cewa ai ita, matar sheriff ce fa ita dole in ganta da kudi hakana, Muryan ta naji tana cewa Sannu fadima na gajiyar da ke yai ko, Na gode kware ki ji bayau ba ina son fitowa inda zaga gari rashin samun abokin tafiya ne yasa ban fito, Saida Ahmad yace min in je dake ai kin san ko ina a garin ke, Tace sai kuma ban samu fuska agurin kuba kin san dangin miji tundai Amal na fuskanci bata ra,ayina takare maganan cikin muryan tausayi Nace a,a haba dai aiko muna son ki sosai kedin ai matar,yayan mu ne kin ga ko dole mu soki, Tunda muna son shi, aidole muso duk abinda yake so ko, Cikin nishadi tace min kai amma kuwa yau naji dadin zancen ki walahi Ban san cewa haka zan samayki ba ai da tun tuni mun dade da shakuwa a tsakanin mu, Rashin ganin fuskan da banyi ba ne agurin ku yasa ko zama ban son yi wurin Ahmad, Bansan lokacinda da wata yar dariya ta subce min ba nace kai haba hjy saboda mu zaki ki zuwa gurin mijin ki. Muda ba ma,a garin muke ba, saida irin haka in munzo kawai,