← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 139

Sashe 28

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gidan tsohuwa ya koma ya kwana cikin dakin shi na yarinta dake gidan,,, wanda bata yarda ta sa kowa acikin shi ba,
Dakin fes dashi kamar akwai wanda ke kwana aciki, don yawan gyaran da take sa ana ma dakin,,,,
Washe gari Saida ya karya kumallo da safe ya kuma, dan gana da wasu daga cikin yan uwan shi ,
Inda yai masu dan alheri so sai, yakuma, yi masu, bayani irin aikin da yake a,can kasar saudiya dakuma irin aiki dake gaban shi yanzu,
wanda zasuyi yanzu anan kasar ta Nigeria
Ya,yi masu wanan dan bayanin ne
Don kawai yadan wanke zargi da shankun sa da suke yi
tunda hjy mama tasa zargin shi, azukatan yan uwan nashi,. ,,,,,,,,
Sun ko gansu kuma sunyi aman na,dashi
Inda har,wani kanin mahafin shi kecewa
munyarda da zancenka Alhaji karami , tunda dayawan mun je mungani kuma mutanen mu in suntafi sunaganin ka ,har yau bamuji komai na assha daga gareka ba ,
Shiyasa koda tazo tai, taimuna wanan mugun tabon azuciyan mu, bamu dauka don ba mu yarda da ita ba sam
Don mu kowani ne yazo ya fadi wanan zancen baza mu yarda ba balle ita din
Ai, In,ma sherine kusan kanta taimawa don diyanta tunda suka tafi turai ba wanda yazo kasan nan ko sau daya suna can suna holewar su,
Itace mai binsu idan tana bukatar ganin su,, sai ta fake da cewa taje ziyaran sune,,don karatu yai masu yawa,,,,,,
Kuma labari ya samay mu cewa shashanci suke koyo a turai din,,
Da haka ya rabu da su sunata zowa suna mai sannu da zuwa da kuma godiya akan kulawar da yanuna masu cewa shidin nasu ne don bai ki su ba,,,,,
Da murna da farin ciki ya nufi garin Maiduguri,,
Don yagana da mahaifin shi kafin ya wuce zuwa Abuja inda zasu ga wasu kusoshin gwaunati kasar ta nigeria don su fara kaddamar da shirin su,,,
Na kafa company global da sauran masana,antu,,, acikin kasa,,,
Mr Williams zaizo, Nigeria inda za su hadu shi Abujan su gudanar da,komai,,,,,
Yasamu Alhaji lawal zannah a katafaren gidan shi da ya gina a G R A uguwar da mafi yawan mazauna wurin tsofafin masu mulki kasane da manyan attajirai sune mazauna wanan uguwar,
Mahaifin nashi yayi murnan zuwan shi so sai ,
Don dai dan nashi ya cika mai alkawain ya nuna mai cewa shi dan halas ne
Don yazo akan kiran shi dayayi kuma yaimai alkawarin zuwa gashi kuma yazo din,,,
Ga uwar gaiyar wanu,irin kallon da taron da yasamu gurin ta,, hmmm,hjy mama saidai kawai ayi shiru dama yasaba dà irin hakan daga gareta,,,,
Bawani sabon abu bane hakan da tayi mai don inda sabo yasiya da halinta,,,,,
Amma ita in,taje gurinshi ji irin taron da yake mata kamar itace mahaifiyar shi, Ankawo mai abinci inda ya nuna ma mahaifinshi cewa akoshe ya ke,
Murmushi dattijon yayi kadan ,daidai lokacin da yake zama a daya daga cikin kujerun dake wurin da aka tana da don cin abincin,,
Yace ma dan nashi, babana baka iya cin abincin mu ne yanzun nan ko kuwa, a koshe ka,ke,
duk da yagane cewa dan nashu, baison cin abincin hjy mamane kawai saboda hajiya tsohuwa ta hane shi tun yana yaro,,,,,
Ada bai dauki maganar dagaske ba amma da yafara girma yana wayau, sai yake fahintar cewa
lalai mama zata iya cutar dashi ,
don tana iya masa komai don ta salwantar da shi aduniyar nan
don haka yake taka tsantsan da al,amarin ta,,

Don yakauda zargi ga zuciyar mahaifin nashi sai yadan isa bisa tebur din cin abincin ya dan zuba fruit, salad kadan yana sha ahankali,
Alhaji yadan yi murmushi irinta manya ya kalli dan nashi
yace mai babana kayi imani da Allah azuciyar ka
cewa ba Amina ba duk wani mahaluki na duniya bazai iya cutar da kai ba insha Allah,,,,,
Duk da asiri taci annabawa Allah balle mu,
Kaidin mutum ne mai kula da yawan ibada da tsare dokokin Allah,
Yadda yakamata ,,,,, kuma nasan cewa duk wani kariya tsuhuwa ta tanadar maka dasu tun kana karamin yaro har izuwa yanzu,,,
San nan ina sane da duk wani gudun mawar da mijin mahaifyar ka ke yima,
Nikaina ina da wata yar alaka da shi wanda bakowane yasani ba kasancewar shi malam din mutum nei mai gaskiya da rikon amana,
Kuma inajin dadin yadda ka dauki malam din tamkar mahafin ka,,,,
Kakula ka kuma kara kula sosai da al,amura, su
Kaga yan uwanka da ke turai sam ban gane ma komai ba gamay da karatun da sukaje yi a can turai din
banda dan banzan kudin da nake ta tura masu,
Inbadon Allah yayini nai karfin arziki ba da yanzu na durkushe kasa warwaras,
Kuma mahaifiyar su bata son sam ayi mata zancen su,, ido nasa masu ita da su
Yakare maganar nashi yana hade wani irin malolon bakin ciki,, da ya tokaro mai a makogwaron shi,,,
Duk sai dan yaji badadi azuciyar shi,
Ada yadauka cewa uban bai damu da rayuwar shi ba sam,
Amma yanzu sai yake fahintan cewa ashe duk wani motsin shi mahaifin nashi yasa ni halarci ne kawai yake nuna rashin ko in kula gaban hjy,mama,,,
Muryan Abba ta dan dawo dashi seti,
Yace gamay da yarinyar da nai ma magana badiyar kowa bace illa diyar Alhaji abokina kuma amina,
Wanda ya nuna min cewa yana son hada zuri,a da daya daga cikin yara na da nashi,
Hakan yasa naga ba wanda yadace da wanan hadin sai kai,
Don duk cikin ku ba wanda zan iya tunkara kai tsaye da wanan zancen sai kai
Duk da kaima din bawai zan tursasa ka akan dole sai kayi bane ,aa kawi in kaga zaka iya sai kaje kuga juna da yarinyar intayi maka shi ke nan
Ahmad yadan dukar da kanshi kasa yace a,a Abba basai naje ba idan yariyanyar tayimaka is ok banda matsalar koma ni
Da mamaki mahaifin ke kallin shi wanda bai,taba zaton abin zaizo mai, cikin sauki haka ba
Hakika babana kadai halas ne tabbas nasan ka gado halarci gurin iyayen mu sosai
Don bakowani yaron wanan zamanin bane za,ayi juyashi cikin saukin kai haka ba
Tundai yadda kake jin kanka acikin lokacin ka, hakan ga, ga,kudi ga ilimin kowani iri katara,,
Nandai yabar komai wurin Alhajin nashi, akan yayi duk yadda yakamata don shi baida lokaci wada tace na kanshi yanzu,,,

Abuja yawuce ranan inda yabi jirgin da yatashi marance zuwa birnin taraiyan,
Saboda mr William's jirginsu zai yi saukan asuba ne,,

Komai ya kan kama a can birnin taraiyan inda shugaban ni sukayi farin ciki da wanan masana,antar da za,a kafa acikin kasa don cigaban kasa da al,ummanta,,
Kwanasu uku suka juya zuwa Dubai don kai takardun rije,jeniyar da akayi da Nigeria,
Al,amarin auren shi kuwa Alhaji da bashir tare da sauran yan uwa suka gudanar da komai kamar yadda addini da al,ada suka tanada,,,
Anje kano wurin iyayen amarya anyi komai cikin tsari,
Ansa lokacin daurin aure nan da sati uku masu zuwa
Don mahaifin nata yace yafi son taje can tayi azumi agidan mijinta,,,,
Duk wanan zancen hjy mama bata da labari saida aka tsaida komai na buki sanan yayan nata ta bugo mata,
Ga hauka irin nata aiko saita hau fada tana cewa an munafunce ta,
Ai diyar yayanta mace wace ta ke tayar wa taso hada auren ta dashi amma shine yayan nasu zai masu wanan cin layin
Hauka iri iri da zagi anjishi gurin hajiya mama,
inda take cewa ita ba ruwanta da wanan auren cin amana da yayan nasu yayi,,
Komai cikin mutunci aka,yishi tare da yan uwa da abokan arziki
Inda ango nacan Dubai yana yin sha,anin gaban shi,
Bashir ne yake gudanar da komai da yakamata ango yayi
Hjy tsohuwa tayi bakin ciki sosai da akace yar uwan hjy mamace Ahmad ya aura kuma tayi fada har tagaji inda akaita bata hakkuri,
Daga karshe tayi waya da Ahmad din yakwantar mata da hankali har ta dan huce,
Amma badon ta so ba yaghana dai batace komai ba ga al,amarin .
Chapter 28 · 0% Book details