← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 139

Sashe 40

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan mundawo, gidane tawuceni fuuuu zuwa cikin gida, kayan nakwaso zuwa dakin ta,
Koda nashiga nata nasamayta har ta dan kwanta saman gado, tana waya,
Daidai lokacin tana fadin wlh duk tsiyar da zamuyi salwa saidai muyi
Mutun ace bai san darajan mace ba shi nashi kawai zuwa aikini kodyau,she ,,ni gaskiya ban iyawa,
Saida kawai ace wai yar aiki ce zata raka mutun don kitifi,
Kayan da ta sawo nake gyarawa asaman dressing mirror dinta
Amma azahiri ita nake sauraro ba wai aikin nake yiba,
Yaushe ne zaki ba da sakon a kawo don in fara barbada wa dan banza,.
Wani iri naji lalai wanan matar batada dama aiko zamu kwasa da ita ke nan,
Muryanta naji ta cigaba da fadin ai ina nan ina kokarin binciken inda takardun suke fara daukowa
Kalonta nayi cikin sauri wanda ita din ma,kallo na tayi batare da zargin ko naji may take cewa ba,
Tai min nuni da hannu cewa in wuce,
Daki na nakoma cikin yanayin damuwa, don nasan cewa akwai aiki ja agabana,

Tundaga wanan ranan nafar sa ido ga al,amuran nafisa sosai,
Tundai ma danaga wata bakuwa tazo wurita daga Nigeria
Wai umurah matar tazo shine aka bata sako takawo wa nafisan,
Aiko zargina yazama gaskiya don wasu magunguna ne kuli kuli a,kabata
Bayan kwana kamar uku, da kawo sakon Allah yabani sa,a ta tafi ganin masaukin bakuwar
Anso zuwa dani sai na kwanta nace banda lafiya,
Suna wucewa na kwashi sakon maganin sai masfala gidan hajiya laila,
Duk wanda muka bude an rubuta bayan nin shi da yadda zatayi amfani da shi,,,
Hjyan ce tai min dabara tasamo kayan mata masu kyau muka sa mata cikin kowani leda, ,,,ba wanda bamu canza ba
Nadawo gida na mayar mata da abinta inda taje,
Naci gabada harko kina,
Ina kallon ta lokacinda take barbada mai wanda akace ta sa mai ga abincin shi,
Dariya yakamani nagudu zuwa dakina naci dariya na can kamar in nutse,
Washe gari koda nashiga in gyara mata daki na isketa tayi daidai sanan gado tana wani lagabewa,
Aikinta takeyi waya, tana fada ma salwa cewa kwanan nan batasan may yasamu Sheriff ba don bai ko tausaya mata,
Dariyan keta yakamani
Nace lalai hjy laila takai tsuhuwar bariki,

Yanzu hankalin mu kwance gaskiya don mun rage wani fargaba kasan cewar muna da mafaka mai muhinmanci,
Baza,a taba zargin muna da halaka da takari ba in mun fita don duk inda zamu da motane ba wani labe labe ko bin lungu lungu, gudun kada akama mu,
Yauma nafito ne don in sayi kayan abincin mu da yadan kare,
Ina cikin wani shago sainaji hayaniyar mutane a kofar shagon,
Da sauri na biya kudina nafito bakin shagon da ,
Wasu takarine askarawa suka biyo su uku gudan wai tana suyan dankalin turawa sukuma saura su tsaye abakin titi suna saida gumama da rana,
Suna ihu suna bidan agaji amma ba wanda ko yakalli inda suke,
Inaji yar matashirya wace muna iya yin wari da ita tana fadin cewa uwar da ubanta duk suna gari ita ba takari bace,
Cikin dakiyar zuciya ganin kowa yaki ceton ta naje gurin nace masu ai,yakamata suyi mata uzuri tunda sunji abinda tace
Jinda sukayi larabcina tsab bakamar na yan koyo ba yasa sukadan saurareni,
Suka kalli yanayina sai sukaga banda alamar shigan banza
Nan shugaban nasu yace min intanbayeta ina iyayenta,
Karya nai masu nace iyayen ta suna nan harda kakaninta ma nabasu wrong address ,
Wanan yariyar tasamu tasha da kyat wurinsu nima dim gabana sai faduwa yakeyi,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣8⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

Almost true life story

Saida naga cewa mun daina ganin yan bagaladin mun masu nisa sosai
Daidai,Lokocin na danyi ajiyar zuciya, nakalli yariyar da muka kwato daga, hannu yan bagaladin,,,,,
Wace sai dan she shekar kuka takeyi tana, ajiyar zuciya kai da kai tanayi, tana dan share hawaye, a fuskanta,,,
Dafata nayi ina Tabayarta ko daga wani unguwa take
sai da ta dan share hawayen da ya dan silalo mata,
lokacin take ce mun ai daga wani dan kauye dake kusa da gari, take shigowo ,
Kauyen baida nisa da cikin gari can tsakan wasu duwatsu yake, larabawan daji ke zama agarin
Inda Mafi yawan yantakaru sun fi labewa a kauyu, ka mafi kusa da garin makka, don gudun kora,,,
Gida nazo da ita, nadan bata abinci ta ci ta, huta, amma duk a firgice take saboda tayi fitar kutsun yau,
saida naga hankalinta ya dan kwanta,san nasa a,kaita har inda zata samu motar da zai kaita kauyen na,su,
Tawuce tana ta zabga , muna godiya tana sharan fuska,,,,
Muna tsatsaye a waje duk jikin mu yai sanyi
Don muma mun san cewa bamu wuce hakan ba,,,
Duk sai ta bamu tausayi wlh,,,, wasun mu harda kuka,

Washegari dayake ranan weekend ne saboda su kasar saudiya,Alhamis da jumma,a, ce weekend nasu,,,,
Don haka nasan cewa mai gidan yana gari don duk sallar jumma,a a garin makka yake yin ta,
Hakane ma yasa yafizama a garin fiye da ko ina, don yana yawan yin dawafi duk ranan jumma,
Shiyasa mukatashi dawuri don muyi aiyukan mu saboda tun karfe goma yake wucewa masajid
Saboda koea yassn cewa idan kakai shadayan rana da wuya kasamu cikin masallacin saidai kasamu gefen masallacin ta waje koshi a mamatse,,
Don haka, Tunda safe natashi don mu yi aikin mu cikin lokaci kafin ya fita,
Nasan cewa yana dakin motsa jiki don halinshi hakan da yadawo daga sallah asuba indan sungama karatun Al,kur,ani maigirma,
sai ya sauya kayan shi zuwa na games wear,,,
Idan nasan yana dakin yin exercise ka,ida ne dole inkai mai cup da goran ruwa mara sanyi guda sai kuma milk mai sanyi ,sanyi guda,
A gefen wani dan standing table dake gefe tsaye nake aje mai,
Duk da nasan cewa bai shan koda rabin kofin milk din saidai hakan bai hana kulun in aje mai ,milk din ba, amma,na ruwa sha, kan shanyewa yakeyi kafin yafito,,,,

Yauma haka dine ya kasance,,, ,yana tsaye yanata tafiyan daba iyaka bisa exercise machine,din shi,,
A hankali na shigo dakin hannu nadauke da tire din drinks,
tunda nashigo nagan shi saye da dogon wando irinta maza masu exercise, da bakar singilati, sai yar karamar tawul da ya, rataya saman wuyan shi,,,
A hankali na isa saman dan tebur din na aje mai dan ture din da na hado mai drinks din ciki,
Na juya don in fita dakin,
Karar waya shi da yaji,,,yasa shi dan tsagaita tafiyan da ba tsayi din, dayakeyi,,,
Da hannu ya nuna min gefen da wayar ke yar tsuwa,,,
Nagane nufin shi indauko mai ita yake nufi,
Wayoyi ne kusan guda uku a wajen, ashe,,,
Ita mai tsuwar ita ce nadauko mai, ashe wanyan mutanen Nigeria ce, sunan yan uwan shi ne kawai aciki sai abokai shi, yan kasar Nigeria,
Malam baba naga an rubuta baro,baro, a fuskan wayan
Ina mika mai wayan yadiba yaga kowa ne ke kiran shi yanzu cikin wanan lokacin daga nigeria
don yasan cewa ana batun sallah asubu ne yanzu haka a Nigeria
Tunda munan a,lokacin karfe bakwai darabi nasafe, ne
Wanda yayi, daidai da karfe hudu darabi na asuba, a Nigeria,
Yana ganin sunan malam saida yaji gaban shi yafadi, don yasan cewa ba kiran lafiya bace
Don iyakar malam din yakira shi da misalin karfe biyun rana na nageria lokacin muku ma ana batun yin sallah la,asar
Daidai lokacin danaga yadaga wayar
Nikuma ina shirin barin dakin sai naji yana fadin Innallahi,
Da karfi na waigo don nasan cewa wanan kalman ba karamar kalama bace ,sai idan tashi hankali yasamu bawan Allah,
Ganin ina kallon shi cikin tashin hankali yasa shi dan controlling din kan,shi,,,
Jinayi yana fadin tun,yaushe ne ciwon yafara mata haka malam,
Sainaji ya ce dan Allah malam akaita asibitin Maiduguri zai ma Abba waya kafin ku zo, asan abinyi,
Karshe dai yace ma malam din insha Allah gashi nan zuwa, shima,
Batare da yadauki ruwan da na aje mai,ba yasauko daga machine din,yanufi hanyar fita, dakin yana fadin ,
Kiramin Almustapha, da sauri,,, pls
Bayan shi nabi cikin sauri don zuwa kiran almustaphan, din

Kafin wani dan lokaci komai na tafiyan shi,an kan mala mai, anshirya komai zuwa Nigeria
Su Almustaphane suka kaishi jidda don booking din jirgin su kayi tun kafin su iso ,jidda wasu ne sukayi mai hanyar komai, don sun saba dashi,tun baro Nigeria dayayi zuwa nan
Suna isa sunyi sa,a dama an mai booking din jirgi
kusan daidai time din da jirgin zai tashi su, suka iso wurin

Mudai mun san cewa ba tafiyar lafiya sheriff, yayi wanan tafiyan ba
don ni agabana akai mai waya din, akan mara lafiyan da yatafi,
Amma sai gashi ga mamakin mu,
munga matar gidan sai busha shanta takeyi,ba abinda yadamayta,ita
Don har wata kawa tasamu wai ita yar lici,,,, wata fara duk man bilicin ya bata mata fuska kamar kuturuwa,
Tana magana tana kashe ido tan turo baki, wai ita yar takari,,
Saboda yanzu kusan sau biyu kenan ina ganin Yar lici agidan namu,
Wace hararane kawai ke rabani da ita, idan tagan ni,
Don ina ganin ta sai naji kawai batai min ba don wata irin gogagiyace da ganin ta,,,
Tunda sherrif din mu ya wuce zuwa nigeria
suke zama a falo suna ta sa kade kade da raye raye dasu, wake,waken su ,na bin rawar,
Mu ko, Sai, Abinci da muke ta aikin dafawa, kala kala,
Don basu koshi sam sanan
Ga wani irin shewa da sukeyi kamar an gafarta masu, zunuban su
Yau duk nagaji da aikin da mu kasha saidai kuma idan na tuna cewa sheriff din mu yayi tafiya cikin tashin hankali sai inji duk zuciya na ta min,suya,,,
Duk da bansan koma may ye matsalar ba, ,hakan baisa nadaina jin bacin rai ba,don nasan ba ta kyauta wa mijin nata ba
,Don inga mutunci ai duk abinda yasamay shi ai yasamayta, itama,,,,
Amma sai ga amatsayin matar shi tana, ta holewar ta, ba abinda yadamay ta ita,,,,,
Duk gidan kowa sai mamakin ta yakeyi, don dama da ganinta kaga tantiriya,
Chapter 40 · 0% Book details