← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 139

Sashe 78

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Doctor kamal ne zaune a office din shi da cikin asibitin sarki fahad,,,
Asibitin da ke a kan shifidaden titin, khalifas road's
Kujerar dayake sama tana dan juya shi a hankali,
Cikin dariya yake maganar shi a gaskiya Ahmad kana bani mamaki ace mutum ya zauna ya hali irin wanan kamar ba namiji ba
Shiko dai kana tsoron matan kane baka son ransu ya baci kake wanan rufa rufan da baida anfani,
Kadiba fa yau shekara kusan uku kenan da yin wanan auren naka,
In a lokacin kana ganin cewa yarinyar nan she is young yanzu fa da takai mallakin hannakilin ka,.
Sheriff dake kokarin mike wa da ga kujerar da yake zaune
Yake ce ma doctor kamal ni bansan ko may yasa kake yawan damuwa da wanan zancen ba,
Ina son kasan cewa ni ba saboda komai har na yarda a wanan lokacin aka daura wanan auren ba sai kawai don in tsirar da mutunci su daga wulakancin da ake shirin masu,
Saboda hakan kawai zan yi in masu gata su koma gida acikin mutunci,
Hmmm nifa tun wancan lokacin bawai nayarda da manufar ka bane,
Ai ba kai kadaine namiji da zai iya taimakawa ba ko,
Ina ga takaru nan yan uwasu da suke aure saboda kawai su zauna akasar sudan yi yadda suke so indan sun tashi tafiya sukashe auren kowa ya kama gaban sa,
Wasu kuma shikenan har abada su zauna atare,
To ni na fadama cewa don in tallafa wa wanan yarinyar yasa har na amince,
Doctor kamal din shima mike wa yayi daga kan kujera suna fuskantar juna su,
Cikin kashe ido yace ma sheriff Ahmad yan zufa ,
Duk a cikin taimakon ne hakan kamar yadda nagan ku a,wurin taron African youth development found,,
Baiyi mai magana ba har yakai bakin kofar fita office din sanan yadan waigo yana kallon doctor yana gyara kwalar riganshi,
Yace ban san abinda yasa kake sa kan ka ga abin da bai shafeka ba yan zu kamal,
Yabuga kofar daidai lokacin da doctor ke cewa zan zo har gida mu karasa zancen,yafadi yana dariya,,,,
Yana fitowa Yusuf ya bude mai mota ya shiga, suka fara hanya,
Yace ma Yusuf suwuce zuwa gida kawai, saida motar tazaunu a saman titin ne yakai kallon shi ga dogon agogon da yake tsaye a tsakiyar gari,
Wanda duk inda kake cikin garin makka zaka iya hango shi a tsaye,
Sai kuma ya dan lunshe idon shi a hankali gami da yin sanya,yaar ajiyar zuciya,
Tinyar tinyar abin yafara dawo mashi a rai kamar yanzu aka yi zan cen
A lokacin da matsi ya kai matsi ga duk wata takari dake zama a cikin kasar saudiya batare da lasisi ba,
Hjy Lailai ce tare da wani takaru na miji sukayi mai sallama a kofar gidan shi,
Cikin mamaki yake kallon su don yasan cewa baida wani halaka da su to may yakawo su gidan shi,
Bayan sun gaisa ne shiru yadan biyo baya sai shine yake ce masu ko daga ina suke,
Hjy ce ta tayi karfin halin fara magana don daga cikin su,
Ta ce mai sun zo gurin shi naiman taimako akan yaran takarin da ke aiki, agidan shi,
Shiru yayi kadan yana dan sauranta
Tace mai ansa mu wanda yaje yafada yan bagaladi cewa suna nan gidan shi,
Shine sukazo neman taimako akan cewa suna son ya taimaka ya rufa masu asiri don idan aka gane cewa su takari ne da gaskiya za,a iya yi masu mugun wulakanci don hakane ma tazo tare da wanan Alhj tanuna wanda suke tare,
Inda shikuma yadan gyara tsayin shi ya shiga yiwa sheriff bayani yadda abin yake cewa komai zai iya faru dasu,
A ,kakauce yace to may ye mafita aciki sai Alhj yace zaiyi kokari ya samo wanda za,a daura wa aure da mutun gudan su idan yaso koda za,azo sai a nuna wanan takardan kan cewa yan uwar su ne sukazo daga kasar su yin umrah bawai zama sukeyi ba,
Magana dai takai har Alhj na batun dukawa kasa akan sheriff yarufa masu asiri ya yarda akawo wani na miji adaura aure,
Sunbar wurin shi da niyar cewa zasu dawo tare da mijin bizan da zasu dauko ne,
Shine Almustapha yakara yi mai bayanin yadda abin yake sai yaga rashin dacewar hakan ,,,
Sai tunanen shi da na hjy laila yazo daya don hakane ya yarda akan cewa za,a daura mai aure da Fadima saboda yasan cewa yar karamace ni daga cikin mu
In yaso idan yagama shirin yarda zai taimaka ya maida mu gida Nigeria gaba dayan mu sai ya maishe mu,
Saikuma ya hasale min auren shi tunda dama, ba wai da sani na bane,
A massalaci aka daura auren bayan sallah jumma,
cikin din bin al umman musulumi da suka halarci sallah jumma,a na ranan,
Alhj umar mai takari sarkin takarin tsakiya da Shehi mijin mahaifiyar sheriff, sune suka zama uban amarya,
Inda Su doctor kamal su ka tsaya a bangaren ango,
Murmushi yakarayi saboda tuna abinda yafaru bayan dawowar su, daga wurin daurin auren,
Inda abokan shi suka sa shi agaba akan su na son su san kowacece wanan Amaryan,
Sai ce masu yayi su bari idan lokaci yayi na su sani zasu sani,,,
Auren yaba duk wani abokin Ahmad mamaki saboda basu da masaniyar hakan don sun san cewa bai ko zancen aure da su,
Sai mamaki sukeyi ko wace,ce amaryan da basu san labarinta ba,
Kudin sadakin da a kabayar a masallaci Alhj umar sarkin takari ya kawo ma sheriff yace yarike a hannu shi asamu abinda akayi ma amarya na samun karuwa, cigaban ta,
Sai yaba Shehi mijin mahaifiyar shi bayan yai mai bayani duk yadda maganar yake,.
Don adinga juyawa kudin kafin in girma ko in wuce Nigeria,
Saidai shi a lokacin har ga Allah taimakon mu yayi don gudun wulakanci,
Saidaga bayan auren ne aka gane ko waye kewa yan takari wanan sherin wurin hukumomin kasar na saudiya
Inda shima akasamu wasu suka tona mai asiri, akan harkan saida kwayoyi, dayakeyi,,,
Duk da auren na sheriff da fadima yana nan daran.
Sarkin takari yace abar shi saboda gaba zai mata amfani tunda tana cikin kasar har yanzu,,,
Saidai yanzu ne kuma gaskiya, yake dan ji wani abu agamay da fadimar wace ada banda tausayi ba abinda yarinyar ke bashi,,,
A hankali yai ajiyar zuciya don yasan cewa duk wanan abin fadimar bata da labari
Saboda kafin ta dawo yasamu damar daukan nauyin hajiya mai sharwali tare da sauran yaranta zuwa gida Nigeria tare da guzuri mai tsoka wanda zasu iya tallafawa kan su idan sun koma gida Nigeria
Wanan abin yai ma su dadi so sai inda hajiya ta roke shi alfarman rike mata amanan fadima yarinya mai kirki da mutunci,
Saboda tayi dana sanin zuwa yawon takarin da tayi don abin bai amfana ta da komai,
Yanzun haka yazo ganin doctor kamal kam yawan damuwar dake damun shi,
Inda doctor yagano abin dake damun sheriff har ya sako mai zancen auren shi,,,
Chapter 78 · 0% Book details