← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 139

Sashe 23

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Saida muka gama komai su har sunyi wanka sun kwanta natashi ina gyaran wurin da muka bata da ciye,ciyen da mukayi,, marana naji yadaure min
Da kyat na iya,daga kafa ta daga inda nake tsaye,,,
Sainaji yadan lafa min,,
Nacigaba da aikin da nakeyi,,,
Ciwon sai gaba gaba nakejin yana min,,,
Barci yadan daukeni aiko nafarka gigice ina wani irin kugi da nishi mai karfi,,,,
Cikin barci hjy da Rugaiyya suka farka a razane,,,
Amai nakama shegawa ga mara na ya daure tam,,,,
Kawai ban san lokacin da nafara mulmula akasa ba kamar macijiya,
Ga amai ina yi,,,,
Rugaiyya tasa ihu saboda rudewa, da firgita don duk iya zaman mu tare ban taba irin wanan ciwon ba,,,
Abinda zan iya tuna wa shine hjy ke tambayana may yasa mayni,,
I,hun da sukeyi yasa kowa fitowa acikin firgice,,
Suna tambayar su make faruwa,
Mairo ce ke fadin wanan yar karamar yar aikin nan ce zata mutu,,,
Daidai lokacin sheriff din mu Ahmad yafito dakin shi cikin jallabiya mai ruwan milk mai budaden hannnu kamar banga,,,
Cikin sauri yafada dakin shida mustapha da kowa yafito dakin shi kusan lokaci guda
Hjy mama tana zuwa taga halinda nake ciki sai ta fara fada wai ai ga irinta nan anjawo wa mutane magana,
Inyanzu na mutu a hannusu dole hukuma ta kamasu ta tuhumay su,,
Zataci gaba Alhaji lawal zannah yadaga mata hannu yace mata is ok pls,
Kibar mu muji da abinda yafaru, inke bakisan kaddaraba mu munsani ,,
Idan Allah yace a hannun mu zata mutu ba makawa sai ta mutu agurin mu,,,
Kingaki yadda da kaddara shine cikar imani,
Fatan mu Allah yabata lafiya, dole tai shiru badon taso ba,,,
Sheriff din mu, Yana diban yanayin da nake ciki yazaro wayan shi yakira wani likitan ma,aikatan,su, yai mai bayani,, likitan yace azo dani asibitin kawai, don zaifi,,,,,,,,,
Almustapha dayaji karshen wayan ya yunkura zai daukeni
Wani tsawa Sheriff Ahmad yabugamai cikin kaukausar murya,,
Saida kowa dake falon yakallo shi cikin firgici,,,
Hannu laulausar rigan dake jikinshi ya gyara wuri guda,,,
Dauka daya yai min sai gani kamar 4month baby a hannu shi,
Cikin sauri yake tafiya abayan mota yasani,
Shike jan motar yanayi yana waigen bayan shi ,don yaga yanayin da nake ciki,,,,
Sultan Abdullarahaman, specialist hospital ya nufa dani,,,,
Muna zuwa Wani kati yaciro cikin aljihun shi yamika ma wani balarabe da ke gaban wata computer,,,
Saida yasa katin yadago ido yakalli Ahmad da,kyau sai kira cikin asibitin akazo da keken daukar mara lafiya aka daukeni zuwa ciki sai wani irin kugi nake yi,,,,
Likitoci uku ke kaina duk abinda yakamata suyi min suyi,
Sundauki dan lokaci sanan suka fito,,,,,,,
Babban likitan yakira Sheriff Ahmad zuwa office din shi don jin bayanin matsalata,
Rugaiyya tana bayan shi hankali tashe,,
Bayan yan rubutun da yayi sai yakalli Ahmad yace,
Bawani matsala bane mai yawa,mungane cewa period ne zata,fara shi yazo mata ahaka,
Kuma gaskiya irin hakan zai iya, jawo mata matsala nan gaba,,,,,
Amma yanzu mun bata magani zamu barta nan
har nan da kwana uku muga yadda maganin zaiyi mata aiki idan munga bai karbeta ba sai mu canza mata wani,maganin
Tana yawan shan zaki wanda haka shima yabada gudun mawa wurin blocking din hanyar da jini zai fito mata,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 14:12] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Wadatar zuciya ya tabbata ga mutumin da akulun yake gode ma Allah akan kowacce baiwar da Allah yayi masa komai kankantarta ,kuma baya kai karan ubangiji Allah a, wurin wani halittansa.

Happy new year 1st muharram 1439AH
O ALLAH!
Make it easy for us to utilise the year better than the last for achieving everlasting blessing in JANNAH Allahuma Ameen👏👏👏

Almost true life story

Saida likitocin suka gama yi min komai yadda ya kamata,, suka kaini dakin da za,a kwatar dani kamar yada sukayi bayani,,
Kwance nake ina barci acikin kwancir hankali,
Ba kamar dazun da nake ta kugi ba,
Sheriff din mu, Ahmad ne dakin sai Rugaiyya dake gefe guda tsaye cikin takura da tashin hankali, ,,
Tana tunanen zuwan da mukayi batare da sanin hajiyan mu ba,,,,,
Jin muryan sheriff Ahmad, datayi yadawo da ita cikin hankalinta,,
Batare da ya kalleta ba yace,
Ina iyayen wanan yarinyar suke,,,
Jin wanan tanbayan yasa Rugaiyya yin hawaye,
Gefen navain dinta tasa tana goge hawayen da ke bin, fuskanta ,a hankali,
Jin shurun da yayi yasa shi dan waigota a hankali don yaga ko tana jin tambayar da yai mata,,,,,
Ga mamakin shi sai yaga hawaye take gogewa, ma,ana tambayar yai mata ciwo ke nan,,,
Dakin yai niyar bari, don yana ganin bata da niyar bashi ansa
Yana batun barin dakin don jin shirun yai yawa,
Sai yaji muryanta tana cewa iyayen mu suna Nigeria,,
Nigeria ya kara nanata sunan,,
Wayazo daku nan,kasan sanan may yakawo ku,,, to,,
Rugaiyya bata boye,mai komai ba tabashi labarin tunzowan mu gurin hajiya
Har zowan damu, saudiya ,duk ta, bashi labarin mu, tun farkon har zuwa lokacin da muka fara aiki a gidan shi,,,,,
Shirun dataji yayi shiyasa ta dan daga kanta kadan ta dube shi,
Sai taga tunane yakeyi shima din,,,
Abinda yafado mai arai tunda ta fara bashi labari shine irin son kudin da mutanen yazu keda shi wanda har zaisa asake yarinya kamar wanan har wata kasar
Wai zuwa neman kudi diya mace ai ba abin yin sakaci bane,atarbiyanta,
Yatuna lokacin da yazo karatu farko akasar saudiya akayi case da wasu mutanen kasar Cameron,,,
Inda wani yazo da yara maza matasa yasa aka sare ma wasun su hannu,saboda su dinga bara suna samo mashi kudi,,,
Wanda yin hakan ba bisa ka,ida ba guda daga cikin yaran yasamu matsala har takai ga ankai shi asibiti.
Nan akaita bincike har aka gano gaskiyar maganar,,,
Tun wanan lokacin yatsani duk wani mai irin wanan halin na bauta,,da yara kanani,,,
Wanda akasari mutanen mu bakaken fata ke wanan dabi ar,
Sam bai son yaga irin wa,yan nan masu wulakanta kasu da sunan neman kudi,,,
koda a,hanyane don abin kunyane ace mu mukafi kowa wulakantar da kai akasa mai tsarki,,,
Zuciyan shi namai kuna yabar asibitin don zuwa gida saboda gari ya soma wayewa sosai,,
Gashi kuma zai kai Alhajin shi ganin likitan shi dake nan zaune cikin birnin madinan, wanda saboda ganin likitan yazo garin dama dashi da hjy mama,,,,,

Saboda samun saukin dana danyi ban farka ba daga barcin,, barcinake yi hankali kwance, sai Rugaiyya dake gefe guda zaune,
Tunda na kwanta barci ban farka ba har kusan awa bakwai , ina ta barcin saboda irin alluran da akaimin don in huta,
Sheriff din mu zuwan shi biyu ban farka ba,,,,

Sanu a,hankali, nadan motsa kadan ,,
a,hankali nakara,motsawa,duk jikina ban jin karfin sa,saboda yai min wani, nauyi,,nakara gyara kwanci na,,,,,
Saidai idona arufe yake har lokacin,,,,,
Muryan Rugaiyya naji tana min sannu da jiki tana dan gyara min kwanciyar danayi,,,,,

A, hankali na bude idona , naga Rugaiyya zaune a,saman wani kujeran roba blue, kalar na asibiti,, saina gane cewa a asibiti nake
Kaina,na,dan gyara a,hankali, don inji dadin kwanci,,
Hakan yabani damar yiwa dakin danake ciki kwance, kallon tsab,,,,,
Turo kofan da akayi ne a hankali muka,kai kallon mu ga kofar dakin gaba dayan mu don muga mai shigowa,dakin,,
Subiyo ne suka shigo dakin sheriff din mu Ahmad, da almustapha,,,
Chapter 23 · 0% Book details