← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 139

Sashe 112

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

don yadda taga Aziza tana farautar rayuwar ta dole ne ta firgice da ita, Don a ranan Amal tace sintiri ta kwanayi a kofar na ta, Tabbas kuwa ba aziza din bace inji nafisat ke wanan zancen acikin zuciyar ta, To wa ce ce wanan mai cikin wace har kira da wai matar shi, don dai gaskiya ita a iya sanin ta bayan Aziza da ya aura a bayanta bataji yakara wani aure ba,, Sunda dade nan gurin suna hiran su shida bashir don daga karshe duk kusan rabin hirar na hjy tsohuwace,, Fitar Bashi keda wuya Ahmad ya mike da niyar ya shiga dakin shi yadan kwanta, Nafisace tace mai wai wata matace kake zance Ahmad don ban fahinci maganar taku ba sosai, Matata, Fadima wace kika sani a saudiya mana, Fadima gabanta yaba da wani dam dam, Takara nanata sunar a hankali ta ce fadima yar takaru, Yace mata kwarai kuwa ita, Matar kafa kace kuma harda ciki, Cikin mamaki ya kalleta yace kina nufin kice duk tsawon shekarun nan bakisan na auri fadima ba ko may, Zaune takai daga tsayen da take duk da sanyi A, C dakuma dan sanyin garin bai hana Nafisa fidda wani zufa ba a goshin ta, Cikin rawar murya tace nasan za,a rina fadima nasan cewa zaki iya yin haka wallahi ko, Wani irin kallo yai mata cikin rashin fahintar maganar ta Yadan kalle ta kawai sai ya wuce nan yabar ta da dinbin tambaya a zuciyar ta, Duk wani zagwadin kasan cewa da mijin ta da takeyi sai taji ya fice mata aran ta Wayanta ta dauko ta dan na lambar mahaifiyar ta, kira na biyu tadaga wayan, Cikin tashin hankali take magana da maifiyar nata, Tace mama na shiga uku ashe Ahmad yana da wata matar bayan nida Aziza, Wai har matar nada ciko a jikin ta, Yanzu haka ma zancen da nake maki ma yana cikin kasar nan wai matar tashi ta gudo daga saudiya, Saboda Aziza da tasata a gaba akan sai taga bayanta, Sai da uwar taji ta idar da zancen ta ce maya nafisa ki kwatar da hankalinki ki natsu ki saurari abinda zan fada maki, Kada ki manta yadda kika koma gidan Ahmad wallahi duk kikayi wani abin da ki ka jawo wa kanki matsala ba ruwana a ciki, In ba abinki ba tunda ma har Aziza ta nuna cewa bata kaunar wanan matar ke mai zai hana ki nuna kulawar ki akai ta yadda Ahmad din zai kara amincewa da natsuwar ki, Kafin uwar ta ce wani abu nafisa tace mama wanar yar iskan yarinyar yar aikin namu ce fa fadima nake nufi ya aura, Uwar tace ina ruwanki aikowa da halinsa yake zama a gidan miji, Badon taso ba uwar har taci karfin ta tai nadama, da zancen, Washegari ne tafiyar su zuwa dogon daji,, motoci ukune kamar ta jiyan na hudun su hilux ce mai dauke da kaya , Motar farko wanan mutumin da zai gwada masu hanya ce tare da security guda biyu, Mota ta biyu Sheriff ne tare da doctor kamal a, baya sai driver da ke jan su,, tare da Shehi a gaban motar Mota ta uku Bashir ne ke jan ta, sai Al,mustapha da salim a ciki a tare da shi, Bayan su kuma hilux ce dauke da kaya sai security ma,aikatar su a cikin motar, Ba karamin gudu suke yi ba duk da kasancewar hanyar ba kyau ke gareshi ba, Gudu kawai suke yi abinsu, Doctor kamal ya,dan kalli Ahmad wanda ke ta , dajin da ake ta wucewa, tun dazu, Cikin kada kai yace wa aminin shi, ya ce kadiba fa irin wanan nisan har a ce wai wanan yariyar ta biyo shi ita kadai, Ahmad yadan nisa kadan ya gyara zaman shi, yace ma doctor, kamar kasan abinda ke acikin zuciya na wlh, Yadda wanan matar tadauki yar karamar yarinya tun daga nan har zuwa kano da ga kano kuma wai har saudiya, Wai bidar kudi kawai, Kai mutane ba imani wallahi, doctor,, Karfe uku daidai na rana su na cikin garin sakoto saboda uban gudun da sukayi, Kasan cewar motocin su duk lafiyyau ne,
Chapter 112 · 0% Book details