← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 139

Sashe 110

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

🐎ZEEE MAKAWA🐎

[12/3, 9:38 PM] ‪+234 706 078 6258‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,,

Duk wani bincike da yakamata Bashir yayi akan wanan garin da suke tuhumar cewa fadima ta na can ya yi shi,
Da kyat da sudin goshi yasamu wani bawan Allah mutumin kano yace lalai ya taba jin wanan sunan abakin wani abokin sanar shi,
Sai dai yana tuhumar cewa garin yana can cikin jahar sokoto ne
Hakan yasa suka bidi wani mutumin jar sokoto da ke cikin kasuwar wuse
Don jin ko yasan wanan sunan gari , sanan ta ina ne garin yake dan Allah,
Dan dattijon malam iliya yai yar dariya yace kwarai kuwa ba shakka nasan wanan garin a can cikin jahar mu ta sokoto take , garin baida wani nisa sosai da cikin garin sokoto so sai,
Dattijon ya kara yar dariya irin ta manya yace Dogon Daji mai rijiyar Biri zam,zam ke nan,
Yace ai gari ne mai tsohon tarihi, acikin yakin sokoto ga arzikin noma da kiwo Allah yaba mutanen wanan garin,
Bashir yaji dadin samun wanan labarin dayayi
Saboda bai son wani abinda zai sa dan uwan shi cikin tashin hankali,ko kadan,,
A hanyar shi ta komawa gidan shi ne yai wa Sheriff text a waya akan cewa an gama komai, ko,
Sheriff shima da alokacin yana hanyar madina zuwa makkah yai yar murmushin jin dadi tare da shafar suman kanshi,
Har cikin zuciyar shi yaji dadin wanan sakon na Bashir don gani yake yi kamar har ya isa garin su fadima ko,
Yasan kowa ye Bashir dama shi yasa yake kara son shi yasan tun suna yara Bsshir yana damuwa da damuwar shi,,,
Yai yar ajiyar zuciya yace fadima i will surprise u, insha Allah,
Duk inda kika shiga cikin duniyar nan zan iya tono ki,
Yai dan murmunshi da saida fararen hakoran sa suka baiyyana waje, yace,,,
Ke tawa ce ni kadai fatima, bazan iya rabuwa dake ba, duk ritsi bazan barki ba,
Tun a wanan lokacin yaji kamar yai tsuntsuwa yaje Nigeria,
Sai yaji kamar an sauke mai wani nauyi ne a kan sa,
Chapter 110 · 0% Book details