← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 139

Sashe 116

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai alokacin yake ma mariya magana cikin harshen turanci saboda ba hausa sheriff ya iya ba sosai daga harshen su na kanuri sai ko turan ci sai kuma idan yaci sa,a mutum najin larabci harshen da ta zauna mai a baki daram kamar itace yaren shi ta gado,
Murmushi mariya tayi mai tana dan bashi ansa a cikin dan turacin ta wanda bai nuna ba,
Lokacin sallah magrib da yagabato ne yasa shi fita daga dakin na inna,
Din shi duk abinda yake yi hankalin shi na ga ibadar shi,
Sai bayan fitan su sheriff ne wanda kamar bai fita ba saboda kamshin da suka bar muna acikin gida
Inna ta samu yi min magana,
Tace min fadima kada kiyi wasa da damar da Allah ubangiji ya baki akan rayuwar ki,
Naga kamar shedan nason ya rude ki kiwa wanan bawan Allah wulakanci,
Duk da ban san komay yahadaki da shi ba ina mai kara horon ki a rayuwa da kizama mai hakkuri da yafiye, aduk al,amari,
Taci gabada fadin fadima idan har kinyi fushi dashi banga amfanin
Lokacin da na kwashe wurin koyar da ku tarbiya mai inganci,
Nace inna aiba fushi nakeyi dashi ba ,
Tace fushi kikeyi mana tunda baki yi dibaiyar cewa sun fito daga wata uwar duniya zuwa nan gurin ki ba,
Ai da kamata yayi a ce kin tare su da hannu bi,biyu tunda har suka zo mahaifar ki,
Ba saboda komai ba sai saboda darajar ki,
Ga alama fa bake ka daice a gurin shi ba kamar yana da wata matar,
Amma ya iya biyo ki har kauyen ki kuma yazo batare da yanuna muna wani kyama ba ko raina kama,
Tace mu mata sauda dama muna wasa da damar da Allah ya ba mu gurin nuna jayayya da hukuncin ubangin jin mu,
Barin fada maki duk abinda yai maki har kizo nan yanzu da alamar ya jaye su,
In ma har wani barna ne kinsan abin barna shiga rai ke garesu,
Daga lokacin da akace wanan abin baida kyau ko kuma adaina shi,
Haramun ne mutum zai ji yana son aikatasu, fiye da komai arayuwar shi,
Shiyasa aka ce an zagaye wuta da abubuwan kawatawa, na ban sha,awa,wanda zuciya keso
An,zagaye aljanna da abubuwa ki wanda zuciya bata so,
Duk wanda ya kama hanyar aljanna zai ta haduwa da abubuwa da zuciya bata so, haka wanda ya kama hanyar wuta zai ta haduwa da abubuwan da zuciya ke so,
Shiya sa akace daga cikin hakkurin da akeson mutum yayi a cikin rayuwar shi harda hakkurin biyayya ga Allah da manzon sa kuma mu mata da hakkurin zaman gidan aure ma,ana biyayya ga mazan mu,,
Yin fushi da mutum ko a kaurace mashi baya hanashi, aikata abin da yasaba sai dai ma ya kara,
Amma jan mutum ajiki shike sa mutum ya tuba daga abinda yake aikatawa,
Don haka matakin da kika dauka bayan zuwan su har nan ,
Nakin kula su ba zai raba ku da mijinki ba,
Sai fa in har kin tsaya kin kwanatar da hankalinki har kowa ya fahinci may ye matsalar da har tasa ki ka fito daga dakin ki bada sanin mijinki ba ki ka zo nan,
Kinga ta hakane har zaku fahinci juna a sulhunta tsakani, inko ba haka ba damuwa da kuma shakku ba zai kare ba a tsakanin ku,
Inna tana kawai na ta wuce ta dauki buta da niyar zuwa tayi alwala, ta bar mu nida mariya a tsatsaye tsakiyar daki cirko, cirko,
Mariya ce ta kalle ne tace min anty fadima yazama dole ki daure ki fadawa su inna damuwar ki dan asan ta inda za a bulluwa maganar
Dan kinga da tun farko kin fada masu komai da duk kafin suzo ansan abin yi,
Dan damar zancen ma da hjy umma tazo tadan walwale ma su kawu dan kadan daga zancen,
Kallon mariya nayi yar karama da ita ta iya wanan zancen haka,
Sai kuma natuna da cewa ai ba abin mamaki bane,
Don mu yaran kasar sokoto komai kankantar yariya tasan iya zama da jama,a
Koda aure aika mata da shekara goma zata iya zama da irin mutanen da aka kaita cikin su,
Zaka gansu kamar kauyawa amma wallahi da wayon su fam, kauyanci daine kawai
Sallah muka gabatar gaba dayan mu ,
Saidai na lura da cewa duk inna ta rude ta rasa may zata bakin mu na abinci,
Sallama mukaji ashe mai gari ne ya aiko masu sheriff da abinci cike, cikin wasu manyan cooler rubo guda biyu,.
Godiya inna tayi so sai dan ice darbejiyan dake kofar gidan mu wanda mahaifin mu ya shuka tun yana da rai ,
Nan mariya tai masu shimfida a samar wani katon tabarma guda biyu wanda ta anso gidan Dije,
Zaune nake gurin da na idar da sallah zuciya ta sai sake sake take min dan a,gaskiya a halin yanzu in har sheriff yace zai koma da ni saudiya nasan cewa zai dauko magana dan ji nakeyi bazan kara barin inna ta cikin wanan rayuwar ba ni in koma cikin daular duniya,
Sallamar hafsi ne yadan katse min tunanen da nake yi,
Jin muryanta nayi yau kasa,kasa ba kamar yadda tasaba ba,
Tana cewa innar mu ashe baki ankayi, inna ta ce mata eh,
Tace shina ankaki aika min,
Akan mina za,a aika miki inji mariya ,
Dan mutanen gidan ku suji dadin kulla muna wani sheri,,,,,
Bata karasa ba ni da inna mukai mata tsawa, amma sai da tace
Ta ce walle, andai ji kunya,
Allah ya tona asirin mahassada,
Ta wuce fuw, hafsi tace ke dai kin ka sani,
Inna da ta lura da cewa na idar da sallah tace min,
Fadima tunane ni kai ko mutanen ga za su iya cin abincin mu,,
Nacewa innar mu za su ci ai , kila,
Sun kuwa ci din don kaji ne dakwale har kusan guda bakwai mai gari yasa aka gyara masu shi irin gashin kauye na ainihi ba wai na oven ba,
Sai kuma fura stuwon shikafa danya da miyar yakuwa, da alaihu yaji man shanu, sai kamshi ke tashi,,
A gaskiya ban da abinda zancewa maigari sai dai godiya kawai, da fatar gamawa lafiya,
Hafsi dai tana zaune shiru gefe guda sai duk tausayin ta ya kama ni,
Ce mata nayi ta bari a kira mata sheriff su gaisa, dashi,
Sai inna da mariya suka ce a,a ta in,bari kawai ai basai yazo ba,
Aisha ce naiwa larabci ta tashi taje inda suke zaune tafada mai cewa ana magana dashi,
Batare da bata lokaci ba ya shigo ciki rike da hannun Aisha,
Yana mai sallama cikin muryan nan tashi mai taushi da dadin sauraro ko yaushe,,
Da larabci na fada mai cewa ga yayata nan wacce nake bi wa,
Tazo gaishe shi, cikin girmamawa yafara gaida hafsi da hausar shi da ba ganewa akeyi ba dan ni ban ma taba jin yai hausa ba sai yau,
Da larabci yake fada min cewa zasu koma sokoto su kwaba duk da shi yasa ya kwana a garin
Saidai saboda doctor bazai tsaya ba dan kada ya barshi shi kadai,
Yai ma innar mu sallama dasu hafsi mariya ce tabi bayan shi suna magana ,
Daidai lokacin innar mu ke ce min bazan bishi in mai rakiya ba,
Ashe bansan cewa rakiyar bako har kofan gidan yana da falala ba ga Allah,
Tashi nayi da kyat zuwa inda suke da hafsi suna magana ina kawowa naga yafito da kudi masu yawa yana mika mata,
Cikin sauri nake tambayar mariya ko kudin may sai tace min cewa yayi abawa inna ai masu breakfast, da safe,
Na sheda mai cewa akwai kudi a hannu na ai zai isa ai masu komai batare da ya saurare ni ba wuce kawai yana mai muna saida safe,
Nabi bayan sheriff da kallo sai naji yabani tausayi,
Dan nasan cewa bai saba da wanan wahalar ba sam, gashi a dalilina ya shigo kauyen mu yau,
Bashir wanda yadawi yanzu daga cikin garun sokoto,
Shine kuma mariya taiwa sako akan yakoma tare da su yasayo mata duk wani abinda zasu bukata goben,
Ashe , sheriff yabawa Basiru kudi, yakaiwa maigari kamar yadda yabawa inna mu,
Mai gari yaji tsoron yawan kudin dan har dubu dari biyu ya bashi a lokacin,
Bayan mariya ta gama ba malam basiru sako tadawo dan ta kidaya sauran kudin ssi naji tayi dan ihu
Duk hankalin mu sai ya koma gareta
Tace inna har dubu dari biyu yabayar fa,
Duk sai naga sun rude hankalin su ya tshi,
Dan murmushi nayi nacewa innar mu kadan ke nan daga aikin sheriff nan nadan fara ba innar mu labarin
Ko, waye,Sheriff, dan daga halinsa nadan fada mata ,
Mariya tace ai naga alama anty don naga duk mutanen nan dayazo da su shine ogan su,
Hafsi tai muna sallama, mukai mata saida safe ta wuce har kofar shiga gidan mu nadan rakata nadawo,
Chapter 116 · 0% Book details