← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 139

Sashe 37

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ya iso haraban gidan yaga canji sosai har takai idon shi ya hango mai haraban da muka gyara inda za a ci abincin
Batare da ya nufi gurin da aikai decorating din, ba ya wuce cikin gida direct
Ya mai jin dadin hakan da yagani
Itako tana zaune falo tasa wani material, ja,dinkin shi yadan matse mata jiki,
Ta bayan ta yazo yadan rugumay ta kadan saboda farin cikin abinda yaga tayi don sai yau yadan fara cire shakkun ta da yake,
Godiya da taji yana mata yasa tatsaya sororo tana, kallon shi cikin mamaki,
Kafin yai wani magana itace tafara magana,
Tace ban fahince ka ba fa habibi,
Murshi yadan yi yajawo zuwa cikin jikin shi yana fadin wanan surprise din haka,
Tace na may ke nan fa, na taron bakin da kikai muna,
Tadan daga hannu ta alamar aa bata da masaniya ita,
Cikin mamaki ya ke kallon ta takara cewa wlh ban san may kake magana ba aikai
Ture ta yayi daga jikin shi rai bace,
Idan bake bace towa yayi wanan aikin ,cikin ikon Allah dai dai lokacin na shigo falon cikin shigar irin ta hausawa
Atamfa ce zani da riga koriya da dan ratsin flawer yello cikin jikin atamfar dinkinta yadan matse min jikina dan dagwas,,, sai gyale dana dan yafa yellow akai na
Da kagan ni, Duk alamar girma ya dan bayana min, dan kuguna yadan ciko cif cif ,kirjina yadan kunburo alamar dai nadan kosa komai na girma ya baiyana sosai ,ajikina,
Ban ko kula da su ba ina kokarin nuna wani dan center carpet da za,a dauka zuwa waje
Kallo duk suka bini dashi na mamaki,
Sai a lokacin nagan su tsatsaye,,,
Batare da wani damuwa ba nadan gaishe su cikin girmawa,
Nacigaba da abin da nake yi abina,
Da mamaki yabar wurin zuwa sama inda dakin shi yake,
Yau gezena,shadda yasa mai ruwan chuculate,, dinkin tazarce ne ,,,sai hula yar zanna bukar yar asali da yakafa akan shi ,,,,agogon company rolex yasa a hannu shi takalma bakake, suna wani irin kashe ido,
Yusuf ne yabugo mai waya cewa gasu nan sun iso ,
Cikin fara,a nake taron bakin zuwa cikin katafaren falon mu, daguda guda sukai ta iso wa gidan har suka gama zuwa,
Saura mutum guda ya rage baizo ba, wanda naji suna cewa Ali baba ,, wai ai baida iyali anytime zai iya iso, daga yamal,,,
Agaskiya duk wanda yazo wanan yar walimar taron amaryam Sheriff din mu ya yaba da irin tarbon da akai mai sosai,
Zirga zirga nake tayi cikin jama, don gabatar masu da abin tabawa ,,
Gefen mata daban na maza daban amma duk da haka ana iya ganin juna don duk guri gudane,
Wata yar matashir mata fara yar kabilar yarbawa ce, da baby ta, ina ganin haihuwar fari ce mata,
Yaron yanata kuka tunda sukazo, tayi lalashi yaron yaki yin shiru,
Kusan kowa a wurin ya tausaya ma yaron adda yake ta faman tsala ihu,
Zuwa nayi na karbe yaron a hannu ta nawuce cikin gida dashi, da ita,
Ruwa nasa masu zafi nai ma yaron wanka wurin cire pampers naga a she kashi yaron yayi,,,
Naimai wanka na gyarashi tsab tabani wani kaya na saka mai,
Lokacin da muka fito wajen taron, mu tararda har an fara cin abinci kowa sai yabawa yake yi da irin girkin da akayi,
Nafisa tana gefe fuskata babu ko alamar fara,a
Tun matan abokai na janta da yar hira har suka gaji su ka kyaleta,,
Tana ta wani matse fuska kamar mai jin warin mutane,
Muna ji suna hiranta kasa kasa suna cewa wanan ai ta tsofe ma Ahmad
Wata kuna tace yo ai auren zumunci ne inbashi ina zaikai wanan ai gwago ce,,,
Gyalen da nasa yana da sulbi sosai, gashi kuma ban iya yafa gyale ba dama sai dai inyi rolling din kaina kawai, gyalen yanata sabule min,
Ga kuma yaro a hannu na, duk na tsawala ina kokarin mika yaron wurin uwar shi sai gyalen ya karkare faduwa kasa,
Subbahanallah aiko idon maza caaaaa akaina cikin sauri na jawo gyalen na mayar akaina, daidai lokacin naga sheriff din mu yai min wani irin kallon banza
Wanda banji dadin hakan ba,
Duk sai naji na tsargu wlh,
Don ni ban san may nayi ba,
Daga inda yake yaga nadan shiga damuwa sai yadan yafito ni da hannu, Sukaina ce ke fada min yana kirana,
Cikin ladabi na isa inda suke zaune shi da su Yusuf,
Fura yace min in debo masu a cups,
Nakai masu furan sai santi sukeyi,,
Ga al,adan su duk wanda zai tafi sai ya aje wani kyauta mai muhinmanci arayuwar ma,auratan wasu na bada kudi masu yawa, suce aba ma amarya wahalar girkin ta,
To muma dai haka din ne don wani katon tire aka dinga zuba duk wani gift da aka samu a wurin
A gaskiya ba laifi don dai an samu alheri so sai,,,
Muna kallo bakin mu suka dinga barin mu da guda daguda har suka watse suka bar mu mukadai agidan,
Saida na ga duk mun gyara ko ina agidan sanan nasamu natsuwa,
Kayan gift din na hada wuri guda na nufi cikin gida da su wurin anty nafisa,
A Falo na samay shi zaune yana waya daganin shi yana cikin nishadi yau
yana ganin zan wuce da kayan gift din,inkai ma,anty nafisa,, dakinta sai yadakatar dani da hannu
naja nayi tsaye cak wuri guda,,,
Ina sauraron shi inji mai zai ce min,
Yana gama wayan ya dakai diban shi gare ni
yace min in,bude komai yagani a gaban shi na ,aje kayan
nan na duka nadinga cire kayan guda gudu ina kuma karanta mashi,sunan wanda yaba da gift din
Abin mamaki ina kai ga na karshe sai naji yace min, duk gift din kayan sawan in dauka,
Kudi kuma in dauka in raba ma duk wanda mukayi hidimar dashi,,,
Saura in,dauka,cikin mamaki nadago kaina don jin zancen shi,,,
Zan yi magana ya dago min hannu yace min ya isa
Jiki ba kwari na tashi don in wuce,
Sainaji yace min yagode da fitar dashi kunyan da nayi,,
Ina dan murmushin jin dadi ban san cewa anty nafisa tana bayana tsaye ba tun lokacin da na fara nuna mai kayan,
Gani ta dayi tayi murtuk da fuska yasani dan ja tsaye ,
Kauce mata nayi nadan bi ta gefen ta nawuce abina da kayan
Muryan ta naji tana magana cikin tsawa take cewa wanan ai wulakanci ne,
tayaya zai dauki kayan yaba yar aiki
Acikin azama naji yace mata wace,ce yar aiki,
Nida take gani zaman kaunar shi da suke ciki daya yake dauka, ba matsayin yar aiki nake ba.
Yace ko kin taba ganin yar aiki tafidda shugabanta kunya kar yadda taga nayi a yau din
Yace ko kintaba yakara tambayar ta cikin tsawa,,
Nidai na wuce abina nabarsu nan yana ta gagasa mata maganganu masu zafi,
Bayan na aje kayan dakina gurin Rugaiyya na tafi,
Na bata labarin yadda duk mukayi da Sheriff din kan gift din su,,
Ta dafa min kafada tace fadima halinki ne na alheri ya ja maki,
Duniya ance indan baka da kudin da zaka taimaka wa mai kudi to kataimaka mai da karfinka,
Kinga kinfitar shi kunya ,
yin hakan yasa shi jin dadin alherin da kika mai a yau ko mai yai maki kin can can ci hakan ne fadima,
Tana fadi tana har hada kayan ta don zuwa gida na mika mata kudin duka nace mata ta aje cikin wanda muke tarawa,,
Ashe duk kudin na a cikin jikin ta nan take boyewa gudun kada a sace muna,
Saida ta hada komai tadauki jakar ta da dan abincin da zata kaiwa su hajiya da su Umar,
Kawai sai naji banji dadin da zata wuce ba jinayi dama muntafi tare don ina kewan su hajiya, ina son ganin su ina son in kwanta tare da su muyi ta waka da labari har barci yadauke mu kamar yadda mukeyi kullun,
Ina kallo ta wuce ni raina yai min baki,kirin

Rugaiyya har ta kai kusa da gida ashe bata sani ba yan bagaladi suna biye da ita,
Tundaga unguwar su sheriff din mu suke biye da ita tunda sun san cewa duk bakin da akayi sun koma garu wan da suka fito, su,,,
Bata ankara ba kawai taji sun kewaye ta sun mata circle, ba ta da daman gudu,,,,,,,,,,

🐎 ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 14:31] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA 🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Allah ka tai Maki Musulumi Duk Inda yake,,,, ,Ya Allah Karufa ma Kullumin musulumi na Duniya Asiri Ameen

Anty Halima Garko

Almust true life story,,

Wa,iyazu billah abinda kawai take fadi kenan idon ta a rintse ,
Inbanda Allah ba wani abinda take iya fadi,
Basu yi wani dogon bincke ba suka gane cewa takaru ce ita bata da takardan zama yar kasa,
Rugaiyya bata basu wani wahala ba don haka bata wani sha wuya ba, wurin su,
A, haka suka tafi da ita zuwa inda ake tara kamamun irin su,,,
Duk wanan abinda yafaru a idon wani makwabcin mu ne, yana ganin an wuce da ita ,
Da saurin shi ya isa gidan hajiyan mu yana sheda mata duk abinda yafaru,
Sun yi kuka sunyi bakin ciki sosai wlh,
Chapter 37 · 0% Book details