← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 139

Sashe 134

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Na hana mariya da sheriff su fadawa su inna wanan zancen haka naci gaba da shayar da yara na nono cikin fargaba,
Sheriff kuma yana kokarin sayo masu duk wani magani da zai sa su karin kuzari
Ganin da nayi yaran basuyi komai ba yasa nadan fara sake jikina ,
Ga bukin Amal yana kawo lokaci don yan zu saura wata guda ga lissafin da naji su sheriff da Salim nayi,
Hakan yasa yanzu ban da wani time din zama gida sosai don muna shirin zuwa sudan can garin iyayyen Almustafa dan gyarawa Amal gidan ta na can,
Cikin dake jikina duk da yafara girma so sai bai hanna ni yin kuzarin aiyukan da yadace inyi ba,
Saida muka fara zuwa Nigeria tukun muka kwana uku, gurin shehi, sanan muka dunguma zuwa kasar sudan tare da yan rakiya daga dangin su Shehi mutum guda sai dangin ummi mutum guda
Abin mamaki saigashi ni a fanni na har mutum shida sheriff ya yarda in tafi dasu,
Salimat safiyya mariya Rugaiyta, matar Basiru, da hafsin mu,
Hafsi taiwa Ummi kumshi mai kyau irin na yan sokoto kafar yarinya yai radam yai kyau,
Mun isa lafiya, ankarbe cikin mutunci, a can muka samu kayan da sheriff yai oda a Dubai har sun iso ko don haka ba bata lokaci muka shiga gyaran gida don yin abinda yakai ,
Tun a cikin family su Almustapha naga mata da maza suna ta zuwa kallon ummina, da ke dauke hannu matar malam Bashir wace yanzu kusan duk kula da yaran ya koma hanninta,
Abinda sukeyi bai bani mamaki saida mukaje gurin wasan kamun ango da sukayi da yamman ana gobe zamu dawo Nigeria,
Naga an kewaye min yarinya anata kallon , cikin tashi hankali na isa gurin da suke a zaune a sasu a tsakiya sai kafan Ummibanan da yasha kushi ake kallo ana mamaki,
Tambayar su nayi a cikin larabci, harshen larabci ko may ke faruwa suka kewaye min yar diyata,
Sai ce min sukayi wai kumshi sukaga an mata shine suke mamaki,
Wai ita da batada miji may zai sa ai mata kumshi yar karama da ita haka,,,
Mamakin su kwarai nayi dan sai da sukace haka na tuna cewa larabawa basuyi wa diyan su mata kwalliya irin namu wai sai wacce keda miji zatayi irin hakan damu nan muke yi,
Nai masu bayani cewa mu haka al,adar mu take diya mace za,a iya mata duk wani kwalliya da macen aure zatayi
Saboda ta tashi da wanan tarbiyar na koyi da sunnar maaikin manzan Allah, SAW,,
Lokacin da naiwa yan uwa na bayani sai duk mamaki ya kama su su ma,
Salimat tace min ai lokacin da ta taba yiwa Asamu,u kum shi da taje massalaci da ita a madina wasu larabawan Egypt taruwa sukayi suna kallon ta,
Tace ai su haka akidar su take wai wa yaro zaiwa kwaliyar burgewa da har za,a bata lokacin yi mai kumshi haka,
Muka dawo Nigeria abin cikin jin dadi irin karramawar da dangin Almustapha sukayi muna akasar su,
Gidan buki yafara cika don yanzu aiki har yawa yake muna saboda dangin uban nin mu sun zo daga jimeta,,
Sungan mu mun gasu inda sukai min korafin rashin zuwa inda suke daban yi ba lokacin da na haihu,
Hakuri na basu dan ban da gaskiya duk da nasan cewa ba laifina bane barinane da ba,ayi ba shi yasa ban je ba,
Amma yanzu nai masu alkawarin cewa zan zo insha Allah kafin in koma saudiya,
Duk wani al,adar da akeyi na bukin aure anyi a wanan bukin na Amal don gaskiya yan uwa da abokan arziki sun zo tako ina don taya mu murna,
Nafisat ma tazo daga Abuja saidai bata kwana ba tace zata tafi maiduguri ta kwana acan,
Kuma ko can din wai ba,a gidan Abba ba,ina jin suna fada da sheriff a cikin waya yana ce mata aida bata zo ba hakan zaifi mai sauki,
Hjy mama ko sakon Allah sa alheri bata aiko wa Ummi ko sheriff da shi ba, har aka ci aka sude,
Yan uwan Almostapha sun yaba kwarai da irin karancin da akai masu da sukazo don kusan duk abinda sukai muna da mukaje hjy Umma tasa mukai masu ninkin banin kin,
A gaskiya abin ba,acewa komai a lokacin, a gurin wanan bukin yan uwan mu ke cewa wai a hada mariya aure da Salim
Ban boye ba na nuna masu cewa hakan bai yu,yuwa sam,
Saboda ko nasan cewa halin su ba zai hadu ba, za,a bata goma daya bai gyaru ba,
Sanan shi Salim nafi kowa sanin yanada budurwan, da suka dade tare tun muna karatu a madina,
Ana gobe za a wuce da amarya kasar sudan inda zasu dan kwana biyu kafin su wuce saudiya,
Muka wayi gari cikin tashin hankali,don duk mun hada kayan tafiyar mu duk da sheriff yace bazan koma Sudan, ba dan tafiyan yai min yawa, hakana,
Sai gashi mun wayigari cikin tashin hankali, anyi sallah Asuba, lafiya da hjy tsohuwa ,
Inda take zaune tana lazimi sai Allah ya karbi ranta agurin,
Ba wanda yasan da haka sai lokacin da wata jikanta tashigo gurin ta ansar kudin kosai da ake mata sadaka duk safiya,
Taimagana taju shiru tana kai hannunta taga ta fadi gefe,
Sai ta sa ihu kawai cikin tashin hankali, lokacin ina dama ma Abbazannah madara ya sha,
Naji wanan ihun tashin hankali, Sheriff wanda yafito wanka alokacin ya na tsane ruwa a,kan shi,
Jin ihun yasa shi saurin sa rigan shi yai waje cikin tashin hankali,
Dauko yaron nayi nima mukayo waje inda yarinyar keta tsala ihu tana nuna falon hjy tsohuwa da hannu,
Cikin sauri ya fada dakin hjy tana kwance yadda ta fadi har yanzu,
Da sauri ya isa gurinta yana jijigata koda yadaga hannunta yaga ya biyo shi sharkaf,
Salati ya, sa,a lokacin yana mai zubda hawaye,a ciki tashin hankali,
Ina kawowa naga sheriff duke a gaban hjy dake kwance, bashiri naja da baya cikin tashin hankali,
Wayan sheriff na dauko lambar Bashir nafara kira sai na Shehi,
Batare da bata lokaci ba saiga,su,cikin gidan hankali a tashe,
Duk wanda yazo sai ya tabbatar da cewa ai hjy tsohuwa lokaci yayi,
Shehi ne da kanshi ya kira wayar Abba dake maiduguri ya sheda mai abinda ake ciki,
Kafin wani lokaci gida yacika fam da yan uwa da abokan arziki,
Andan jinkinrta ma Abban su Sheriff dan yazo yaga gawar mahaifiyar nasu, shida wasu yan uwan su daga Maiduguri,
Kulli nafsin za,ikatin,mau, yau muna kallon cikin tashin hankali da kuma jimamay aka wuce da hhy tsohuwa makwancinta,
Dole aka jinkirta tafiya da Amal wace taci kukan rashin kaka na gari da sukayi,
Duk shekarun da nayi da sheriff wanan ne karo na biyu danaga yana zub da hawaye arayuwan shi,
Duk da nasan cewa bakaramin rashi yayi ba na mutuwar hjy,
Amma kuma hawayen danaga yanayi yasa nakara gaskanta mugun shakuwar da ke tsakanin shi da yar tsohuwar mai mutunci ga zumunci da sanin ya kamata,,
Abba zanna ya ce lalai dai a wuce da Amal washe gari tunda ko an tsaya ba wai dawowa hjy zatayi ba,
Amal na kuka muma muna kuka kamar bazamu kara haduwa ba aka wuce da ita,
Tare da yan rakiyan ta duk da Abba ya hana atafi da yawa daga nan,
Su hjy umma da Salimat suna cikin yan tafiya, tare da mariya na,

🐎ZEEE MAKAWA🐎

[12/15, 9:59 PM] ‪+234 808 968 1079‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣8⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,
Chapter 134 · 0% Book details