← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 139

Sashe 70

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bakaramin mamaki text din yabani ba saidai ban gama mamaki ba naji anturo min kofar dakina,
Firgigit nayi natura kayan gefen gadona na zauna kamar ba komai nakeyi ba,
Amal ce tashigo dakin da murmushin ta zo har inda nake tadan zauna bakin gado tace min,
Ashe baki barci ba nace mata eh, saita ke ce min yanzu yayan mu ke fada min cewa wai gobe akwai inda zamu da karfe, hudun marance,
Sainake cewa ko kin sani shine yace min yafada maki ai kin san da zancen
Mamaki yakamani tunda nasan cewa bai fada min komai ba,
Iyaka ce min yayi insa blue din kaya gobe kuma bai fada min komai, ba ai,,,
Washegari sai ban fito ba har wani lokaci ina daki ina karatu abina kusan ba wani abin da zan bukata wanda babu shi,
Aisha ce tazo min dakin da kukan ta wai umar ya dake ta,
Dole natashi nafita daga buyar da nakeyi yau, agidan don kusan ince
Yau ba wanda zaice yagani acikin gidan sai maman umar da taji shiru tabiyo ni dakina da abinci na tace min inci
Ta hanyar baya nabi don kada su gan ni cikin rashin sa,a sai gashi na hade da salim
Murmushi yaimin kadan yace wai fadima maye sirin ne kulun fa sai kara girma kikeyi da kyau,
Salim baka gajiya da zolaya kai ni yau ko mirrow ban diba ba bale in gyara fuska na,
Kafin inkai wurin Umar din saigashi yasamay mu inda muke tsaye da salim,
Nadan mai fada akan ya daina saurin dukan mutun ,
Idan yasaba ba zai ji dadi ba nan gaba in ya girma,
Nan na fara ba salim labarin marin da Almustapha yai min lokacin da na raki hajiya tsohuwa dawafi,
Salim yadinga yi min dariya kamar a lokacin abin yafaru,
Nima dai dariyan na kama nacigaba da fada mai yadda nadinga ji kamar in rama marina in gudu alokacin
Salim yana nunani yana dariya yace fadima an fada min cewa bakyaji kina karama sosai,
Dariya muka karasawa gabadayan mu nayo baya da niyar in dan waiga gefen tsuntaye na ingani sai naci karo da
Sheriff tsaye cikin wasu yan kananin kaya sunyi matukar daukan shi kamar shi yayi kan shi,
Fuskan shi atamke babu alamar dariya cikin dan dukawa nayi cikin ladabi na gaishe shi,
Batare da ya ansa ba yake ce ma salim yabi yo shi sutafi,
Saida naga sun bace min azuciya na ce bahagon mutun ba,a gane gabas dinka sai kaso,
A falo nukayi kicibis da Amal tace min kin gama kwanciyar dakin kin fito ne,
Murmushi kawai nai mata don nasan komay zance mata bazata yarda ba sam
Ita madai din shi tabi ni dashi tana tafiya tace min fadima karfe uku da rabi zan shigo wurin ki mu gyara jikin mu don tafiya zuwa wajen walimar da za,ayi na yan African Youth Found mazauna saudiya saboda tallafawa yan uwa musulumi kasa shen,baka ken fata ,
Nace mata to a zahiri
Amma cikin zuciya sai cewa nayi wanan ba wurin zuwan yar takari ba ce saidai ku masu hali,
Bama zan koyi rigimar cewa zan tafi ba tunda ko mai gidan bai sheda min ba,
Kuma na hadu dashi dazu bai ce min komai ba kenan wanan fitar bai shafe ni ba,
Saidai in ita Amal din keson ta kasa dani,
Chapter 70 · 0% Book details