← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 139

Sashe 103

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau a gajiye yadawo gida saidai kuma lokacin tashi daga meeting din da suka shiga bai yi ba, saidai kawai ya kama jin ba dadi a ransa, don haka yafito abin shi zuwa masaukin shi,
Yadai dawo ne kawai saboda yau sam baya jin dadin jikin shi,
Yana shigowa masaukin shi ya aje yar briefcase din shi gefe kawai ya haye kujera ko takalma ya kasa cire, wa,
Nan waje barci ya kwashe shi kawai batare da wani bata lokaci ba,
Duk da barci bai yi nisa ba amma sai wani mafarki mai firgitarwa ya sa,shi farkawa a firgice yana mai yin salati da istigfar,
Gaban shi ne yakama faduwa saboda duk second sai yatuna da mafarkin da yayi,
Fadima ce yagani zaune a tsakar daji saman wani dutse, gurin duk ciyawa ne kore shar,
Saidai tana dago kai sai yaga duk cikin damuwa take da fargaba, ga hawaye jagab a fuskarta,
Wanan mafarkin ya tsaya mai a zuciyar shi,
Sai tunane yake yi anya kuwa, ba wani hali Fatima take ciki ba,
Tunda yasan cewa ta na cikin barazanar Aziza a ko wani lokaci,
Duk yadda,yaso mafarki yafita mai a rai ya kasa, duk abinda yake yi ,
Wanan mafarkin da yayi yake tunawa, abin har yana,son zama mai kamar fever,
A dadafe gari yawaye mai saboda duk ya matsu ya zo saudiya, hankalin shi a tashe yake,
Jirgin farko da ya sauka a saudiya daga Spain dashi a cikin sa,
Bai ko tsaya zuwa gidan shi na Riyadh ba,
Shatar mota ya dauka zuwa madina, shi kadai, ne a cikin, motar,
duk gudun da driver ke yi gani yake yi kamar baya gudu,
Karfe biyun rana suna cikin garin madina, direct gida ya dosa,
Duk wanda ke gidan saida yai mamakin ganin sheriff
Saboda ba su san da zuwan shi ba, a wanan ranar,
Gaba dayan su, duk sun shiga cikin rudanin ganin shi cikin wanan lokacin,
Kowa da ke gidan, yazo yi mai sannu da zuwa a daidai wanan lokacin,
Karba masu kawai yake yi yana dibar hanyar da zaiga na fitowan fadima,
Abinci mama umar ta gabatar mai a saman dinning table,
Kasa daurewa ya yi yace ma Amal wace ke zaune gefe guda duk a takure,
Fadima fa,
Amal kallo ta kaiwa ummi, don ta bada ansa, tambayar da yai mata,
Yadda yaga Amal na nunawa yasa shi mikewa tsaye a lokacin,
Kamar may rada yace may yafaru da Fatima Amal ,
A hankali Amal tace ba komai, yayan mu, kawai dai sai kuma tai shiru ta dukar da kan ta kasa,
Muryan ummi ce yaji daga bayan shi tana fadin ka kwanatar da hankalinka ka ci abinci tukun kafin ai maka bayanin komai,
Da sauri ya juya gurin da Ummi take tsaye cikin wani irin murya yace dan Allah Ummi ku fada min abinda ke faruwa da Fatima,
Ummi tace kayi hakkuri ka zauna insha Allah komai zai zo da sauki,ai
Girgiza kan shi yayi yace ban fahinta ba ummi, har yanzu ina fatimar ta ke ne wai,
Muryam salim yaji ta bayan shi yana cewa wallahi ta bata muna,
Da sauri ya juya gurin Salim ya riko hannu shi yace What,
Ta bata kamar wata dabba can, tun yaushe ta bata da baza,a fada min ba,
Har saida nagani da ido na,
Shiru duk sukayi,
Ba abinda yake nanatawa a bakin shi sai innalillahi wa,ina alahim raj,un, kawai yake ta fadi
Dan dir dir ya yi na rashin sanin abin yi sai kuma yasamu guri ya zauna yadafe kan shi da hannayen shi,
Nanda nan idon shi suka kada sukayi jawur, kamar garwashin wuta,
Duk suna tsaye tsarma tsarma suna kallon yadda ran yan maza ya baci yau,
Salim ya kalla yace mai kai min bayanin komai pls
Don insan ta inda zan fara bullowa zancen,
Salim ya fada mai dan abinda yasani gamay da batar nawa,
Amal ta karbe zance da yi mai bayanin duk abinda ya faru tun wucewar shi, sai kuma maman umar da ta bada nata bayanin ita ma,
Wani irin mugun kallo yai masu a lokacin cikin jin haushi da ta kaicin su,
Bai ce komai ba yasa kai kawai yabar gidan, cikin zafin rai,
Salim na ganin haka ya mara mai baya suka fita tare kusan lokaci guda,
Da farko gidan Salimat suka, nufa
Ita madai bayanin duk yadda fadima ta firgita da Aziza tai masu, amma ta kare zancen da cewa sun yi da ita cewa washegari zata dawo gidan ta ta zauna da ita har sheriff yadawo,
Sai kawai taji shiru kuma daga baya sai ga Amal ta bugo mata tana fada mata cewa fadima bata gida,
Shiru yayi nadan wani lokaci yana nazarin zancen ta,
Daga gidan Salimat gurin ja,mian tsaro ya nufa kai tsaye,
Batare da bata lokaci ba suka fara aiwatar da aiyukan su,
Dawowar sheriff da kwana daya su Salimat suka bar kasar saudiya ita da mijin ta,
Saboda ta kare karatun ta, dama karatu ta, tafiyi ga shi Allah ya nufa har ta kare,
A ranan bai kwana a garin madina ba Makkah ya wuce kai tsaye,

Washegari duk wani bincike da zaiyi yayi saidai babu labarina sam,
Babu ma wanda yace mai yagan,ni a garin, makkah
Hankalin sheriff yakara tashi sosai don ya rasa ko ta ina zai fara binciken,
Shin ta Aziza ko ta Alin, zai fara, wata zuciya tace mai duk kan su,
A bokin shi doctor kamal ne ya bashi shawaran su fara bincike akan Alin tukun,
Duk iya binciken su sungano cewa Alin baya zuwa saudiya har yanzu tun lokacin da yai yunkurin sace ni,
Sai suka dawo kan Aziza, kuma,

A Dubai ya samayta inda ya buda mata wuta akan cewa lalai sai tayi mai bayani akan abinda taje yi saudiya bayan tasan cewa baya kasan a lokacin,
A lokacin Aziza ta dauki zancen da wasa so sai dan bude baki tayi tace mai
Amma dai tana da right din zuwa duk lokacin da taga dama ko,
Ko saboda yayi auren yar kwaila zai zo ya damay ta
To bari ta fada mai indai akan fadima zai zo ya tayar mata da hankali sai tayi maganin su shi da ita,
Kafin ta fadi wani kalma wani irin wawan mari ne ya sauka a fuskan ta saida ta gigice,
Ya shake mata wuya da hannu guda ya ce ki fada min ina kika kai diyar mutane ,aziza,
Fadima ta bace a saudiya ba wanda yasan inda ta tafi,
Ido ta waro waje don jin kalamin shi
Ta ce ta bace fa kace ya dan sasauta shakan da yai mata ya ce kwarai kuma ke muke tuhuma da bacewar ta,
Nan ya koro mata duk abinda Amal da maman umar suka gani a gamay da ita, lokacin da tasa fadima a gaba,
Ta yi mamakin jin cewa a wanan lokacin da tai ta sintiri a kofar fadima a ganta,
Harda yunkuri zuba Meagan da zai zubar da cikin fadima datayi,.
Cikin sanyi murya tace wallahi ba ita ce ta sace fadima ba san da tayi cewa gurin hukuma za a kaita kara
Indan kuma anyi karanta kasar Dubai zasu dawo da ita kasan haihuwar ta ne ba zasu kara barin ta shiga masu kasa ba,
Tai wani yunkuri don ta mike shiya sanya shi dan ne mata kafa da tasa
Yar kara ta saki ta ta dibe shi da sauri, sai taga ya canza mata ba Ahmad din da tasani bane yau,
Muryanta na rawa tace wallahi bani na sa aka sace taba,
Ni yunkurin zubar da cikin da ta yaudare ni ne kawai nayi,
Wani irin mugun shaka ya kara kai mata ya saida idon ta yafito waje don azaba,
Tunda take ba,a taba gwada mata azaba irin wanan ba,
Duk yadda taso ta motsa ko ta kwace kanta ta kasa
Wani zogi da radadi ya ratsata,
Kallon ta yakeyi yana nazarin irin rudewar da yagani a idon ta,
Can tace wallahi Ahmad ka yarda da ni ban san komai a gamay da batar fadima,
Cikin wani irin zafin rai ya sake ta yana huci yace barin fada maki aziza muddin bincike ya nuna cewa da hannu ki a cikin wanan zancen wallahi bazan raga maki ba ko kadan,
Bai kara koda second ba ya juya yabar gidan cikin fushi,
Nan Aziza ta rushe da kuka mai tsuma zuciya tayi da tasani ga shirin da tayi niyar ai,watar wa a kan fadima,
Wani abokin su ne ya basu shawaran su koma saudiya su kara bincike duk yadda akayi zaau gane inda fadima take,
Su Amal sun rasa gane kan dan uwan su tun da wanan abin yafaru,
Ya koma masu kamar wani mahaukacin zaki, sai jami,an tsaro ke masu sintiri a gida,
Wanan lokacin duk wqni wanda ke tare da shi yasan irin kaunar da son da yakewa fadima,
A nacikin wanan halin aka bugo mai waya daga Nigeria cewa jikin hjy tsohuwa ya tashi,
Gabadayan su suka zo Nigeria dan diba jikin nata,
Kwanan biyu ya koma saudiya don ci gaba da bincike,
Nasir abokin doctor kamal ma aikacin yan sandan ciki ya basu shawaran zuwa ma aikatar tafiye tafiye don adiba masu,
Sheriff yace yasan cewa fadima bazata iya kai kanta gida ba saboda tun tana yar karama akabar Nigeria da ita,
Don haka da wuya ta iya komawa garin su,
Ganin cewa Nasir din ya nace ne yasa su zuwa maaikatar tafiye tafiye na kasar saudiya,
Sunayen wa,yanda sukayi tafiya a wanan date din zuwa yanzu aka fitar da photos din su ,
A madina suka fara bincike basuyi nasara ba sai suka tafi jidda,
Ganin ko a jidda ba suyi nasara ba yasa yace masu su bari kawai don shi dama ya san ceqa ba zan iya komawa gida ba,
Doctor kamal yace sam sai sun tafi Riyadh sun karasa bincikawa,
Binciken farko ya nuna masu photo nadana Aisha a ranan da mukabar gida ranan nabar kasar saudiya zuwa kasata ta haihuwa Nigerian,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣1⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,,,
Chapter 103 · 0% Book details