← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 139

Sashe 124

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da hujjan yin hakan ko Don dole in diba don inga dawa sukati kama don har yanzu bawai na saduda bane, dama wanan damar nake jira dan in tabbatar da cewa ko da kwana akai wanan cikin ko kuma da nasu ne kawai, Yan rakiyan nasu na cewa kwarai kuwa dan gani yakori ji, Cikin harshen kanuri Amal taiwa yan maiduguri magana, Tace masu matar Ahmad ce ta Dubai tazo ne dan ayi bala,i kawa, tace dan Allah su figita ta so sai , Haba Hindu dake wani tanar cingun kas,kas jin wasa yuka kawai tayi a bayanta, karrrrrr karrrrr ta waiga da sauri aiko, Anty Falmata ce ke wasa yuka sai wasu sauran yan uwan su cikin dangin mahaifin yaghana da suka zo ga tsaga yaba yaba a fuskan su suma sukace dawa Allah yagama mu bada kuma ba, Tashin hankali aisai gasu duk sun mike atsaye Allah yasa Amal ta rufe kofar duk shiga gidan Aikafin ace haka sai hindu ta dauki waya jiki na rawa ta kira wani wai hello Kura kana ina ne ku shigo kawai akwai matsala, fa, Allah ya taimaka Salim ya farga da mutanen tun zuwan su yai ma duk securities din gbayani akan akulada su, Sai da aka bari sun shigo tsakiyan sai kawai fitina yatashi tsakani su da security, dakuma su salim da mlm Basiru wanda tun gida sunci maganin tauri, Yanka guda yakawo wani security sai Basiru ya tare aka samay shi ganin gurin bai yi jini ba yasa gudan cewa Wlh muyi ta kan mu kura kada rana ta baci muna yau don da alamar yau ba nasara ga aikin nan Duk yadda su kura suka so suyi yun kurin gudu security da su malam Basiru sun hana su ga kuma wasu yan sanda da Bashir suka turo su ma sun iso gurin Cikin gida kuwa yau su Aziza sunga Barebarin asali sun kuma ga aikin su Daya daga cikin kawayen Aziza da tai tsauri mike wa dan gudu taga cikin masu tsagar na ta nufota da yuka tsirara ai,sai kawai ta fara kurma ihu ,, Tana bidan ceto, daga waje, duk sun tsorace gawayar su Kura ana kiran su basu daga ba, Nan fa hankalin hindu ya kara tashi kamar ta ce gara da bata zo ba, Aziza tace wa Amal Amal nizaki sa aiwa wanan rashin mutuncin haka, Amal tace au ke mutunci kikazo yiwa mutane ko may, Amal tace yara suna nan lafiya lau amma kisan da cewa babu jiniki cikin ko dayan su, Dan Allah yafiki yafi sheriki, dan bakiso koda ahaifi su din ba tunda kikaso kashe su tun a cikin ciki,, Allah ne ya kare fadima har takai ga haihuwar su lafiya batare da kin yi galaba akan su ba, Haba sai Azuza tafara cewa ni duk wanan zancen wallahi ban san dashi ba Amal Amal tace ai yau takare dai tunda ke kika kawo kanki don sheri, wai har zaku shigo kunawa mutane wulakanci a cikin gida, Amal takara wa matan nan yaren kanuri aiko sukayo kan su Aziza da yuka tsira gadan,gadan kamar zasu yanka su da gaske haba sai ga Hindu a kasa ta daga hannu biyu tana fadin aimata rai,. Aziza saida na fada maki kada muzo ki ka nace akan son kai yau gashi kin jawo muna bala,i a filin Allah, Matan na suka samu su Aziza suka murje su da kyau, sai sun baka tausayi, Kofar da ake duka ne kamar za,a balle shi yasa suka dakata da bugun su, kin bude kofar akayi,. Saida Bashir yai magana da karfi aka bude kofar, Shi da sheriff ne tare da wasu yan sanda suka shigo cikin gidan cikin tashin hankali suke kallon kowa don ganin mutane cirko cirko, Kallo guda Sheriff yai wa Aziza ya kau da kai cikin yare yai wa Amal magana ta juya da sauri ta hau sama, Ina zaune cikin tashin hankali ta fado dakin cikin sauri take magana tace wa safiya ta dauko jaririn guda ta biyo ta zuwa falo, Ban san lokacin da na mike tsaye ba dana ji haka Ido waje nake tambayar ta ko ina za su kai min yara, Batare da Amal tabani ansa ba ta sakai zuwa downstairs da yar baby a hannuta safiya na binta da dayan a bayan ta, Duk kan mu falon muka fito cikin rudani rashin sani may za,ayi wa yaran, Ganin Aziza da kawayen ta zube saman ties, yasa duk muka tsaya tur tsaye da mamaki, Daya bayan daya yadinga daga yaran yana nuna mata kamanin su da kyau, Duk halin da take ciki bai hanata yin ajiyar zuciya ba alokacin, A hankali na tako zuwa har inda suke nadan tsuguna daidai saitin inda Aziza take Nace mata hjy dan Allah kiyi hakuri kifita harka na da na diyana hakana, Allah yagani banda amanar ki shi yasa lokacin da kikaso cin amana na Allah bai baki ikon akaina ba, Duk cikin larabci nake mata magana don tana fahinta saboda zamanta a Dubai, Hakan yaba duk wace ke gurin dama masu jin larabci muka shiga za,aga masu maganganu cikin bacin rai, Saida sheriff ya tsawata muna cikin bacin rai sannan muka kyale su, Banko tsaya ba na, juya cikin kuka nabar falon cikin bacin rai, da tashin hankali, Bayan dogon shehin da yai matane yan sanda suka wuce da ita, zuwa tare da kawayen ta, Abinda mutane suke iya shedawa kawai shine kishi yakawo ta dan haka akai mata wanan mugun wulakancin da tazo da niyar ita taiwa mutane sai gashi reshe ya juye da mujiya, Ba wanda muka fadawa yadda zancen yake akabar shi arufe, Karfe hudu duk angama wani shiri akan walima, jiran isowar malamai kawai akeyi, Walimar yayi armashi so sai malama Zuwaira tai sherhi akan hakkin uwaye akan diyan su da kuma yadda tarbiya ke farawa tun yaro na shan nono, har zuwa girman shi,, Ana tsakiyar walimar Nafisat ta iso gurin tare da yan uwanta su kusan shida inda suka mara mata baya, Cikin shigar su ta yan gayu suka shigo wurin kowa idon su na akan su saboda irin yanayin shigar su, Duk da sundan rufa yan gyale a kan su kamar ba matan aure ba, Don daga kasan cewa ba,a tunanen mutuwa zata iya riskan mutun anytime, an shagala da duniy kawai, ba a tunanen gamuwa da ubangiji Kallo guda nai mata daga inda nake zaune naga tadan kara kiba sama da sanin da nai mata, Amma banda shi tanan bakar ta bata shafa man da matan zamani ke shafawa ba dan suyi haske, Daga inda akai masu mazauni muka hada ido da ita, duk da nike yarinya na hago ki shina karara a cikin idon ta, Nasan ko ba komai bane sai ganin yadda na sake lokaci guda na canza daga fafima yar takari zuwa Fadimar Sheriff Ahmad Lawal Zannah,,, Taro ya,watse cikin jin dadi da annatshuwa inda aka raba wasu manyan traveling bags dake dauke da showel da su sabulai da kuma kayan snacks a ciki da su sweet kalakala, Yan dogon daji da sukazo zasu koma gida matan su kowace turmin zani da dubu biyar mazan su kuma shadda da dubu biyar, ga kuma kayan buki kalakala, Hakanal yan maiduguri su ma kyauta iri guda akai masu da yan dogon daji, Naso hafsi ta tsaya saidai kuma saboda tafiyan mu maiduguri yasa na bari tabi sauran yan uwar mu zuwa gida, Su hjy umma wace take zama min kamar uwa yanzu takara min nasiga sosai akan zaman duniya inda ta lurar dani yadda sherin mutanen zamani yaje da kuma yadda zan zauna da mijina a cewar duk kishiyoyina ,suna da matsala atare da su, Da zu tafi kamar kada su tafi su barni nake ji don duk kusan lokaci guda suka wuce bayan alherin da Sheriff yai masu ta bajinta tare da yi masu godiya,,,
Chapter 124 · 0% Book details