← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 139

Sashe 81

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaune nake saman gadona ba abinda ke fitamin sai hawaye,
Ina tsoro da fargaban maganar Salimat, tunda ta fara ganewa kada Amal ma da muke tare ta gane,
Allah Allah nakeyi har Aziza ta cire cikin ta kada wanda yagane cewa ina da ciki,
Don gudun zargi irin wanda Anty Salimat tafara min,
Nasan cewa ana iya jefe ni idan har hukuma taji,
Sheriff mutun ne mai yawan ibada nasan cewa sam bazai lamince min ba,
Ihun da naji Amal tayi ne daga dakin ta yadan katse min tunanen da na zurfafa ciki,,,
Da murnan ta iso har inda nake kwance ina kokarin tashi,
Fada min tayi saman jiki na da karfi saida naji wani irin abu cikin karfin hali da daurewa na dan mike ina mata dariyan yake
Tana murna ta na fadin Ummi nan acikin saudiya , tadan kara fadowa saman jiki na sai naga ta mike da sauri ta hadiye murnan data,keyi,
Ta dan kalle ne cikin firgici tace min fadima jikin ki da mugun zafi
Baki da lafiyane haka sai nadan wayan ce zancen kawai,
Lafiyata kalau may kikaji halan
Wani kallo ta watso min gami da dan taba gefen wuya na,
Kafin tai magana sai nace mata yaushe ummi ta iso tace wai yau takai kusan sati uku ai
sundai ki fada muna ne don kada muce zamuzo,
Nima na nuna farin ciki na sosai da zuwan ummin,
Don haka washegari muka shiga shirye shiryen taron Ummi da zata zo ganin mu daga makkah,
Duk abincin da a ka dafa komai na kasa ci daga ciki sai
"Ya,yan itace kawai nake sha kamar hauka, abinda takeyi tabari da sauri ta nufi hanyar kitchen hankali ta tashe ga abinda take hasa she
Kirana tayi daga kitchen din tace min inzo in kama mata aiki,
Ina shiga warin man da take suyar rotinar ya nashi hanci ai sai naci kamar in kurma ihu,
Kofar baya na nufa ina shirin kakarin amai,
Cikin sa,a aman bai zoba na, taso da kyat da niyar in koma ciki
Maman Umar din ce dai na ci karo da ita tsaye da cibin tsamar rotinar a hannun ta tana min wani irin kallon tuhuma,
Nai kamar ban gane nufinta ba nai niyar shigewa na ciki in barta,
Tareni tayi tana ce min, may take shirin gani a tare da ni haka,
Duk yadda naso in noke mata saida ta tsaidani amma fir nace mata Iam, ok
Sai kusan Yamma lis bakin mu suka iso saboda nisan da ke a garin wanan karo harda sister din su Amal wacce ke aure da yaronta aka zo,
Zokaga irin murna da farin cikin da muke yi a ranan,

Sheriffudeen Ahmad shine yashigo karshe daga cikin su ,
Daidai lokacin nafito daki da murna na nafada bisa jikin Ummi,
Nalafe nadan wani lokaci batare da nai magana ba,
Itace ta dagoni a hankali tana min kallon mamaki tace fadima ke ce haka,
Sai na kara noke kaina ajikin ta ina dan dariya,
Sheriff na tsaye ya kura min ido gaban shi na faduwa saboda irin masifafen canjin dayaga nayi na lokaci guda,
Nai wani irin fari ko ina nawa ya ciko cif,cif kamar wata katuwar budurwa,
Gashin jikina yayi kwance lub, lub fatana yakara wani shiki da haske,
Jinda nayi su Amal na mai sannu da zuwa yasa nadan daga daga jikin UMMI na nufi gurin shi don in gashe shi,
Yana tsaye cikin shigar turawa yasa suit a jikin shi,
Har na isa gab da inda yake idon shi na akaina, yana min wani kallo cikin sha,awa,
A,hankali nai mai sannu da zuwa kamar yarda muka saba idan yazo,
Yadago yakalleni idon shi yayi wani jajir kasala ta sauko masa da kuma wata irin sha,awa,
Tana fisgan shi,,
Gabada ya lokaci guda duk ya birkice, wuri guda,
A sanyaye ya ansa min da cewa ya nake,
Nace mai lafiya lau,
Amal tace wai lafiya lau ko jiya da dare jikinta kamar garwashin wuta, yake don zafi,
Muryan bakuwar da suke tare ne da su tace wanan ce fadimar,
Amal tadan jawo ni tace itace fa kedai anty falmata,
Mai suna falnatan tace masha Allah sam barka,
Nadan murmushi yake na ce mata barka da han ya anty cikin ladabi da girmamawa
Hannu ta miko min alamar inzo gurin ta natako a hankali na zauna gefen ta inda ta nuna min,
Mukayi gaisuwa na musabi,a
Saida sukayi sallah har mu sannan muka zo falo gabadayan mu gidan don cin abinci dinner da aka shirya ma zuwan su
Su salim da Amal sai washe baki sukeyi,
Dan yaron Anty falmata na karba ina mai wasa UMMI tace min in aje shi kawai inzo muci abinci,
Kamar in ce bazan ciba sai dai nadaure natafi don kada UMMI taga banyi mata biyaya ba,
Sheriff dake zaune gefe da tasbaha a hannu shi guda,
Yanajiran azuba mai nashi sai dai duk idon shi na ga duk wani motsi nawa a fakaice,,,,
Wani irin shauki so da kaunar fadima kawai ke fisgan shi,
Ji yayi kawai yana son ya kasan ce tare da ita,
Bude abinci da maman Umar tayi don ta fara zubawa mutane yai daidai da shakar kamshin abincin da nayi,
Har ina ture Amal gurin tashi da sauri na toshe bakina da hannu guda na shige daki,
Duk suka bini da kallo gabadayan su,
Amal ce tace bansan wanan sabon salo da fadima ta dauko ba walahi duk aka bude abinci ko ta shaki warin turare sai ta ce wai ita mai, ta fadi karshe da alamar nuna ko oho,ho,
Ba sheriff ba hatta UMMI saida taji wani irin shock din zancen na Amal wacce ita bata kosan tanayi ba,
Ture kujerar dake gabanshi yayi ya nufi dakin nawa,
Ina ciki duke a bakin toilet inata kakarin amai
Ina,gamawa, sai nadago daniyar in ja kafa na zuwa kan gado na
sai na ji na kasa kuma ga sheriff a,tsaye gaba na ya kura min ido kur cikin tuhuma,
Ganin shi danayi tsayen cikin kallon tuhuman da yake min shine,
Yasa na, dan ja kafana nadafa bango don kiris ya rage min in fadi a yadda nake ji,
Hannu ya mika min alamar in miko nawa dole na mika mai hannu yakamani a hankali har ya kaini saman gado
Yazaunar dani ko yanzu ido yakara kura min, a hankali na sada kaina kasa
Don ban iya jure wanan kallon,
Muryan shi naji yana fadin may ke damun ki fatima,
Bakomai na ce mai haiyya ,,,
Kai kawai yakada yakoma falo zuciyar shi na ta mai wani irin tuhuma, akai na,
Lokacin da yashiga falon duk ido suka sa mai don jin ko ya mukayi,
Banda UMMI daketa cin abincin ta, mama umar ce ta yan ko min fruit a plate ta nufo daki na dashi
Sai Amal tace shine kawai abincinta yanzu nayi fada amma bataji sai ,,, bata karasa ba ya daka mata wani irin tsawa saida ta firgita don tsoro,
Ita batasan cewa maganar shi jinta yakeyi kamar zubar ruwan zafi a zuciyar shi,
Ummi tace Amal kin faye surutu da yawa kiyi mata fatan Allah bata lafiya kawai ba wanan surutun naki ba,
Sheriff baici abincin ba tashi yayi ya fita kawai duk suka bishi da kallo

Ina kwance ba barci nakeyi ba idona biyu hannu na rike da handout ina kokarin dubawa amma tunane ya hana ni shakat,
Sheriff na dakin nawa cikin wata jallabiya baka yasa yar fulla fara daidai tsakiyar kai,
A hankali nadago idona na bishi da kallo har ya zauna, kusa dani
Minti kusan biyu da zaman shi duk munyi tsit dakin yace Fatima na ansa a tausashe da na,am,
Yace min tun yau she ne rabona da inyi period, dina,
Sai a lokacin na tuna da zancen period din da nakai wani lokaci ban gane shi ba, fa,
Kuma batare da na damu ba na share zancen kawai, abina
Ganin da yayi cewa bazan asa mai ba yasa shi mikewa yabar dakin cikin tashin hankali,
Washegari kowa kokarin cin break fast niko yayan itace ne a gabana inata masu shan hauka,
Ummi ce ta min Fadima koba kyson cin abinci ki daure kici hakana kinji ko zaki amayar ba duka zaki fitar ba dole a samu wanda yadan tsaya maki a ciki
Don kinga bake kadai bace yanzu,
Maganar bai wani bamu mamaki ba tun da bawai mungane ko may take nufi bane,
Sheriff ne cikin kamar hasala yace min in shirya ya kaini asibiti kawai,
Batare da wani bata lokaci ba na mike zuwa shiryawa,
Ina fitowa naji muryan anty falmata na cewa UMMI sun dace a gaskiya da yaya wannan itace daidai da shi walahi,
Yariyar ta burgeni sosai walahi,,

Cikin shakku da fargaba nai wanan tafiyan zuwa asibiti ina ta rokon Allah yasa kada aga komai a tare dani,,,
Chapter 81 · 0% Book details