← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 139

Sashe 114

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Masu karatu nadai fada maku irin fasalin gidan mu tun farkon labarina,
Dan haka gidan mu gidan laka ne mai dauke da dakuna biyu na laka saman dakin mu jinka ne,
Gidan mu an kewaye shi da zana ne da kuma karar marasa,
Yan kayan aikin mu suna a tsakar gida gefen darni inda muke girki,
Sai yan dabbobin da inna ke kiwo a gidan raguna guda biyar da awaki sun kai hudu,
Sai kaji, da kuma tantabaru, da Abdull ke kiwon su,
Don haka da zaran ka aje wani abu yanzu kiwon nan na inna zasu far ma abin da ci ko tono,
Shiyasa bamu aje komai a fili duk cikin daki muke aje kayan mu,
Tafiya sukeyi da kafa sai jama,a dake bin su a baya mata harda leke sukeyi a darni gidan su dan ganin zahiri,
Sheriff sai waige waige yakeyi yana nazarin irin gidajen da ke gare mu a kauyen,
Yana tunane a ranshi cewa a wanan irin gidar fadima ke rayuwa aciki,,
Ganin da sukayi kawu ya nufi wani dan tsukarken gida
Wanda a,ganin su bai fi daki daya ba,don kilama ba filin gida acikin shi,
Anan kawu ya tsaya kofar gidan yana kwada sallama,
Kawune akofar gidan innar mu yana kwada sallama, Abdull da Aisha dake wasa ta tsakar gida suka amsa mai
Innar mu dake fitowa daga daki tace mai ,
Koni am shigo mana Salihu sai kace wani bako can,
Yace aida bakina muke shinassa
Bakin shim to lale marhabin da bakin mu inji inna,
Tace mai shigo dai ni,daita agidan,
Sheriff da doctor sai bashir dake bayan su duk suka kutso kai cikin gidan na inna bayan ison da Kawu yai masu,
Ganin datayi bakin sam ba suyi kama da mutanen kauyen mu ba yasa inna saurin jan zanin da ke daure a sanan wanda ta daura dama kusan da bi,ar mutanen kauye ne daura zani biyu,
Ko kuma a aza guda a saman kai
Aisha da ke ta zagayan gida wata yar akuya karama tana kora akuyar sunata faman guje guje
Daga kan da Aisha zatayi sai kuyi arba da sheriff,
Wani irin ihu tayi don gani da taima cikin mamaki tana fadin Abu,Abu,,
Ware hannayen shi yayi tafada mai ajikin shi karamar yarinyace sai kawai tasa kuka,
Duk wanda ke gurin saida hannkalin shi yatashi dan yadda Aisha ke kuka,
Daki inna tai masu shimfida, a samar wata tabarmar kaba mai ruwan ja da shudi,
Bayan fitowar mu gidan kawar Mariya bamu tsaya ko ina ba sai gida,
Abinda na dan lurada shi ,shi ne yadda yau nake samun gaisuwa ga yan kauyen mu ,
Koda ban san mutum ba zai ce min fadima ho,
Mariya ce ke cewa ingwaiyya,,
Duk da ganin mutane dani kofar mu hakan ban kawo komai a raina ba illa saurin da nakeyi kawai in shige cikin gidar mu
Kaina yana a duke har muka shige batare da na tantace ko suwaye a waje ba,
Ashe salim na kallona da shi da Almustapha acikin su,
Ganin da sukayi mun dukar da kai a kasa yasa suka kyale mu
Wai sun dauka ko al,adar garin mu ce hakana,
Uwar,Tunkiyar inna ce ke fitsari samar takalmar sheriff takalman da akalla zasu kai dubu saba,in indan ankiyasta da kudin Nigeria,
Mariya na kokarin cewa inna ga wasu mutane fa akofar gidan mu tsaye,
Sai kawai hancina ya shar min kamshin da bazan taba mance mai amfani da wanan irin turaren ba arayuwata,,

Hakalina a tashe na furta a hankali na ce Sheriff,
Sheriff mariya ta maimaita abinda nace ina mai nuna mata kofar dakin innar mu,
Ta, waiga da saurinta ta isa kofar mutum uku ne zaune sun cika muna daki da kamshi sai innar mu da ke can ta kuryan daki rusun,ne,
Cikin sauri ta isa kofar tana kokarin lekawa, cikin dakin,
Sandarewa nayi tsaye inda nake don sam bantaba zaton cewa Sheriff zai biyo ni har kauyen mu ba,,
Nadauka cewa mun rabu ke nan har abada, dashi,
Don ban zaci cewa kamar sheriff zai tsaya bata lokacin shi ga yar aiki irina ba,
Waigiwar da sukayi dan jin muryan mariya yasa su hango ne tsaye cikin mamaki,
Doctor kamal ne yai min larabci yace min inshigo, mana,
Ganin da yayi kamar ban motsi a tsayen yasa ya fadawa sheriff,
Cikin sauri duk suka nufo inda nake tsaye sandare ina dogon tunane,
Jin muryoyin su da na yi a kusa dani yasani dawowa a cikin hayaci na,
Cikin sauri sheriff ya rike min hannu na muryan shi naji gab dani ya na ce min in zauna tukun,
Zama naji bisa dan turmin dakar inna da ke kife a gefe na,
Kaina nakama jin ya na wani juya min a lokacin dan haka sai nadan dafe kan da hannu na guda,
Mariya ce tazo da saurin ta ,ta dan dafani tana fadin anty fadima may ya samay ki pls
Har yanzu na kasa magana sai ido nake dan binsu dashi cikin mamaki da fargaba,
A hankali duk suka karaso inda nake daidai lokacin innar mu tasa mariya tafito da tabarmar a waje,
Cikin damuwa nadan daga kaina da kamar wacce zatai magana sai kuma na kasa na kara dukar da kaina kasa,
Inna tace wa mariya ke maza kuna sunka taho,
Sai mariya ta washe baki saboda jin dadin zancen inna
Tace Allah mungode ma,
Da na rasa abinda zanyi sai kawai nasa masu kuka kamar yadda Aisha tayi,
Sheriff yace min cikin larabci Fatima may yasa kika barni may yasa kikai min haka,
May zai sa ki wahal da kanki da baby na,
Fatima ba kya gudun wani mugun abu yasamay a hanya
Kin ko san irin kasadar da ki kayo haba Fatima,
Sai na kara sautin kukan da nakeyi,
Sunana yakira a hankali,
Yace min ya rokeni Allah indaina wanan kukan
Kada mutane na su dauka ko wani mugun hali yake min acan,.
Yadan langabe kan shi alamar maganar shi ba wasa acinkinta,
Batare da kalle shi ba na mike a hankali da niyar in shige dakin mu,
Duk wanan drama a gaban su inna da kawu har da tumba wace ta shigo gidan da niyar gulma
Batare da yadamu da mutanen da ke wajen ba ya dan jawoni kadan zuwa jikin shi
Nai sauri na gwauce da ga rikon da yai min,
Yace haba fatima aiko doctor dai kya tsaya ku gaisa da shi ko
Ga kuma Almustapha da salim a waje har da Shehi,
Da sauri na waiga dan in gaskanta zancen shi aiko Shehi ne tare su
Suna shigowa cikin gidan mu,
Da sauri na mike zuwa wurin shehi mutumi da nake jin shi kamar mahaifina
Kuka kawai nasa mai agaban shi kamar wata yar karamar yarinya,
Yace fadima bana son inga kin kara wanan kukan ,
Ba kuka yakamata kiyi godewa Allah yakamata kiyi,
Duk yadda na so inyi shiru abin ya faskara kukan kamar kara min shi ake yi,
Nakasa yin magana dakowa daga cikin su,
Har nadan wani lokaci,
Bashir ne ya fita tare da su almustapha da salim da niyar zasu tafi cikin garin sokoto don suyi booking din hotel
Inda zasu sauka gaba dayan su, anjima, saidai sun bidi taimakon wanda zai masu jagora hakan,
Mariya ce tasa aka kira malam basiru wanda dama yana kofa atare da sauran securities din da suka zo da su,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
[12/3, 9:43 PM] ‪+234 706 078 6258‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,
Chapter 114 · 0% Book details