← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 139

Sashe 108

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau zaune nake ba abinda ke damuna sai kewar su Amal da Salim tunda nazo nasan cewa nakan dan tuna da su wani lokaci,
Saidai gaskiya na yau yafi don tun da na tashi da safe nake yawar tuna nen su, a,raina,
Wayana nadauko a hankali na kunna photos din da mukayi boye su nayi can cikin wani wurin storing yadda ba kowane zai san da akwai photo a ciki ba,
Ban karasa kallo ba sai ga inna ta shi hannu ta dauke da ganyen zogalar da nace ina son ci ,
Sai nabar wayar nan natashi zuwa gyara ganye na,
Mariya ce ta dauki wayan tana kunnawa sai kawai ta dinga cin karo da picture's din da nake kallo har da wanda nayi da Sheriff lokacin da muka tafi Kasa shen waje tare da kuma Dubai,
Tadan dade tana nazari hotuna duk da rubutun arabic ne a ciki, wayar tawa,
Sai lokacin da na kula da itane nakuma tuna cewa ban kashe wayar ba nadaka mata tsawa har saida ta firgita,
Don tunda nazo ban taba ko da hararar ta ba balle tsawa,
Cikin sanyin jiki tai saurin aje wayar saida nakawar da gurin picture's din na mika mata wayar , kamar baza ta karba sai kuma ta karba,
Malam Basiru sannu a hankali ya fara dan shige muna a gida, don lokaci da dama shike dawo da Abdull daga school, saman babur din shi,
Bayan kamar sati guda da tafiyan su Rugaiyya da mijinta sai kuma nai baki daga garin kano,
Bakin da mamaki da kuma karin imani yasa na kasa koda yin wani kwakawaran motsi,
Saboda sam ban taba tsan manin zuwan su kauyen ba ,
Hjy umma ce tare da yan matan ta su biyu, sai Abu driver da yajawo su, zuwa garin namu,
Nai farin ciki matuka da ganin su, sun yi sa,a ranan munyi tunwon shinkafa da miyar shuwaka ba su nuna wani kyamar ci ba ci sukayi sosai har suna karin miyar,
Innar mu, ce zaune da tare da hjy umma suna kara gaisawa kamar yadda manya suka saba yi,
Cikin gaisuwar hjy umma take tambayar innar mu cewa har yanzu dai mijin wanan yariyae bai biyo sawunta ba dai ko,
Cikin mamaki innar mu tace wace yariyar kenan hjy sai hjy umma tace fadimar mana,
Ai kurciyane yasa ta, wutowa Nigeria baya a gari,
Jin maganar innar mu keyi kamar a mafarki ,
Shin murna zatayi kokuwa kuka,
Sai kawai ta dan sa kuka, saida hankalin hjy umma ya daga daga sosai don ta rasa ko may inana kewa kuka,
A hankali ta rarashi innar mu ,don kada hankalin mu yadawo gurin su,
Abdull inna ta tura don yakira mata kawu,salihu, ba,adauki wani lokaci ba sai ga su tare cikin sauri,
Bayan sun gaisa da kawune sai inna tace ma hjy
Hjy inna son maganar da kika fada min cewa fadima tana da aure ki kara fada a gaban kawun ta, yaji,
Mamaki ne ya kama hjy cikin mamaki take tambayar inna mu wai ko lafiya maganar ya tayar mata da hankali,
Cikin natsuwa inna tace a gaskiya hjy tunda fadima ta dawo bata taba fada muna cewa wai tana da aure ba,
Asalima ko cikin jikin ta saida mutanen gari suka gane, cewa tana dashi don, bata fadi da bakinta ba,
Cikin mamakin wanan irin hali nawa yasa hjy umma ta jiwani irin bugun zuciya a lokacin,
Cikin ranta tace ko dai fadima karya take yi ba aure ke gareta ba,
Can kuma tace to in ko har karya takeyi ai da ta boye min zancen cikin kamar yadda ta iya boyewa mahaifiyar ta, tace kai akwai dai ,
Sai kawai ta daga murya ta kirani inda suke, jinkiran da tai min kuma sai a lokacin nasan cewa kawu na cikin gidar mu,
Gabana ne ya dinga haihuwa kamar zai fashe don fargaba,
Jiki ba kwari na isa har gurin da suke zazaune, na samu gefe guda nadan tsuguna, nesa da su kadan,
Kawu salihu ne yai gyaran murya yakira suna na cikin murya mai ban tausayi yace min,
Fadima kiwa Allah ki ji tsoran sa ki fada muna gaskiyar maganar da wagga boyar Allah ta taho da shi mu jiya,
Shin da gaskiya na fadima da amre kin ka gudu nan kokuwa dai hwadi dai na kinkayi,
Shiru nayi nadan wani lokaci sai hawaye yafara sintiri a fuska na,
Can naji murya hjy umma tana cewa fatima mai yasa kika boye wa mahaifiyar ki gaskiyar maganar da ke tafe da ke,
Shiru nakara yi sai kukan da na kara sautin shi kawai ina fadin dan Allah inna ki yafe min wlh nima bada sani na aka daura min aure ba,
Asalima haka wanan cikin da ke a jikina Allah ne kawai yasan dalili kawo min shi a wanan lokacin,
Kawu ya kara tambayana cikin tsawa tsawa ya ce shin kina da aure ko baki da,
Cikin kuka nace inna da aure akaina kawu kusan shekara uku kenan yanzu,
Maimakon suyi fada kamar yadda nake zato da fargaba sai kawai na ji muryan su suna fadin Alhamdullahi Alhamdullahi,
Kawu yace haba fadima shina kika bari ana sheganta maki da duk gari,
Da da uba nai a nata sheganta shi,
Mi da kikaki hwda ma mutane shin,
Kuka yaci karfina natashi na koma daki ina mai zubda hawaye bakin ciki,
Hjy umma ce tabawa kuwu labari komai kamar yadda na fada mata, tun shigowa na Nigeria,
Ina da taci kuka ta gaji tace tun tahowan ta naso in fahinci haka gare ta a mma sai tace mun wai ita tunda ta tai bata taba aikata zina naba
Ke ashe dole na inshiga cikin kwankwanto,
Hjy ummu tace ma kawu tunda duk gari sun mun mugun fassara kada su fadawa kowa komai sai lokacin da Allah yakawo mijina ai dole yaje gidan mai gari ko
To a wanan lokacin kinga dole kowa yaji cewa ga uban cikin da suka sheganta ya biyo abinsa,
Kawuce kware da gaske haja za,ayi ke yar kulu kija bakinki ki shiru har Allah ya kai mu lokacin,
Sai kusan karfe biyar su hjy sukayi muna sallama suka dauki hanyar zuwa zamfara, don a can zasu kwana,
Tsakanin inna da mariya na rasa wanda yafi wani farincikin jin wanan labarin,
Don ranar kamar su goyani suke ji, inna tai min fada akan may zan boye mata gaskiyar maganar
Maganar da itace yakamata tafara jin sa bawai sai wata tazo ta fidda ita acikin duhu ba,
Tace min fadima am baki san irin halin da ni,shiga cina ba walle da baki boye min komi ba,
Abinda yasa kun kaga ina dakewa don dai kawai Allah yadawo min da ke gida na lahiya,
Nadan sauko kasa nacewa ina dan Allah ta gafar ce ni,
Ni tsoron fada mata cewa nayi aure bada izzinin su bane yasa na boye zancen,
Mariya tace min ai ita tun ranan da nai mata tsawa akan photo da take kallo a wayana yasa ta fara zargin cewa akai wani boyayyen al,amari da nake boye wa,,
Hatta hafsi innar mu ta hana afada mata wanan maganar tace tunda har ta iya nuwa duniya kyamar yar uwata a fili,
Nai sauri nace inna ba laifin hafsi bace ,hafsi tana ko,karin ganin cewa tabi umurnin mijin tane kawai,
Don shine ke kokarin nuna mata cewa yana kyamata kuma baiga kun dauki wani mataki akaina ba,

✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
8⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,,
Chapter 108 · 0% Book details