Sashe 97
Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gidane ginan laka irin na kauye duk da gidan tsohon gidane bazaka gane ba saboda sabon yaben da akaiwa gina ga sabon jinka asa asaman rufin dakin ya koma kamar sabo,
Ta kofar dakin ayin mai sabon shafe irin na kauye laka laka,siminti ,siminti,
Darni gidan na subur karan dawa ne akayi amfani da shi,
Ga icen zogala da na durumi an zagaye darnin gidan da su gefe tulun na ruwa ne da babban randar ruwa suma sabbi fil da su,
Daga can gefe han yar zuwa yauce (makewayi) turke ne na raguna manya manya sai wani fasashe rada inda ake zuba ma dabbobin abinci,,
Ga kaji nan sunkai goma irin na gargajiya suna ta kiwo atsakar gidan,
Tafito dakin da tana gyara daurin zanin ta da ke kokarin banyewa irin daurin zanin yan kauye da ake tankwahewa gefe guda,
Hannu guda na dauke wani dan karamin kwarya,
Cikin kwaryan gumba ne wanda zata dama kunu dashi don karin kumallin su na safe,
Inna yar Kulu ke nan mahaifiyar Fadima,da ke zaune a garin dogon daji mai rijiyar biri,zam,zam dake acikin jahar sokoto,
Duk da mutanen kauyen nawa inna yar kulu kallo wata wacce ta ke cikin wani irin daula ,
Ga kiwon tumakai da akuyoyi da takeyi, ga kuma shanu har biyu da ta turke gefe guda,
Duk cikin kudin da Ruggaiya ta kawo masu ne, duk da inna taki karban kudin duka a hannunta,
Bakin murhu ta zauna tana dan gyara iccen da ke kama da kara sai tarin hayaki da ya bude gidan dashi wanda har makwabta a na iya hagen shi,
Alamar cewa ke nan ta hura wuta a gidan ta kasan cewa bakowani gida ake dama kunu ko yin wani abin kari ba,da safe,
Saidai fura da za,a aje a cikin wata r langa ko kwarya ko fanteka,
Wanda aka dama tun jiya ko kuma an kirba shi tunjiya, yayi tsami har yagaji,
Shiza asama ruwa a motsa kowa yazo yadinga diba, a yar korya ko roba ana sha,kamar yadda kowa yasan kowani kauyen hausa sukeyi,
Abinci sai ranan jumma,a ake dan yin tuwon shikafa ko na dawa, yara su dinga murna suna fadawa junan su cewa yau jumma,a
Kowani gida za,ai girki tuwo da miyar yakuwa da alaihu, da kabewa,
Wasu kuma tuwon kullun dawa da miyar danyar kubewa ,,ko kuka, fara fat da ita,
Hakan yasa suke ganin cewa inna ita tanajin dadin ta sosai don tun filazan ita gidanta tana dafawa yaranta abinci ko ba dadi sai sunyi shi sau ukun nan,,,
Gidan inna ko yaushe tsab yake da shara, duk da kiwon da takeyi bai hanna ka gane cewa tayi shara, a rana,
Saida ta gama dama kunun ta sa ma mariya kira wacce ke daki tana shirin zuwa makaranta boko ita da dan autar inna Abdul wanda suke cewa datti,
Mariya tafi cikin kayan makarantan ta tazo inda inna ke dan motsa mata koko a cikin wata yar roba mai fadi,
Inna tace mata ta koma daki ta dauko sukari a cikin leda wanda suka siyo jiya ya rage,
Alokacin Datti ya shigo gida da yar leda baka a hanun shi wanda ya sayo kosai da shi,
Ya mika wa inna laidar tadan jawo wani dan plate din silver ta kasa masu kosan kashi uku ,kowa guda guda,
Saida Datti ya fara shan kokon ne yace inna ai na manta ban hwda maki ba,
Kai wai wani irin yarona haka duk sanda kattaho cin abinci sai kayi dumi, (magana)
Waga dabiar banzata koda yaushe ina hwda maka,
Ko ni,an inna ki kasani ko wani sabon batu na yyajiya shina shika son shi,hwda muna,
Ke,ke ke banison shegantaka kejiya,
Mariya dake gefe takalli Abdul tace tadan tausa murya don kada inna taji su tace,
Shin minana kaka son cewa Adullahi,
Ke ko ni an bashi tun da wanda abin yya shahwa tace in bari to ni mi nika hwdi kuma,
Inna dake jin su ta waigo takawai mariya rankwashe akai tace
Kai waga diya anyi yariyar kawai,
Shin kuna sauri kutaizuwa makarantaga ko ko sai kun yi abinda mallam yattabi jikin ku,
Abdull daya tashi yana sa takalmin shi na roba na makaranta saida yakai kusan fita bakin gida ya waigo inda inna ke tsaye ta sance kullin kudin da tayi a gefen zanin ta,wanda zata mariya kudin kashi, haka yara ke kiran irin wanan kudin safen da uwaye ke basu dan sayen dan wani abu,
Ya waigo cikin dan daga murya don inna taji maganan,
Yace mariya ke,
Macen nata wadda akacewa ta sace fadima ita ta naggani jiya ana taratara da inta anka hiddo ta cikin mota wai bata da lahiya ,
Tasamu mutuwar jiki,na shina za,ashiga da ita cikin gidan su dan isah yyacce wallahi tallahi shikam sam bagidane ba tunda yawon dandi ttahito ,
Wassani ko mugunyar ciwona, takkwaso ta taho ta watsa musu duk su mace har ita,
Inna da mariya da ke tsaye suna sauraron shi duk sun maida hankali gare shi,
Cikin karaji inna yar kullu tace , shin wata macce na kaka nuhi,
Badai Gajiye ba ta gidan su Dan isah
Ya awo ita ta mana naka nuhi,
Ko yanzu da natai z duduwa mai kosai maganan na nijjiya suna yi ita da tunba,
Salati inna yar kulu tasa sai da duk yaran suka kallo inda take tana ta rafka salati,
Shinka wa hwda maka wagga mugunyar magana,
Nihw da ijjiyana naggani inda muka warigi dadare nan na motat tatsaya aka tambaye mu gidan su dan isah,
To, to to kutai zuwa inda zakuna dawagga bakar labari dakkatare mu da shi tunda wagga farar sahiyan,
Bayan hita yaran sai duk maganar da Abdull yafadi ya dami inna acikin zuciyar ta duk sai taji bata da sukuni,
Tana gama duk wani dan aiki dake gabanta tashiga daki tadauko hijabin ta tasa tasa ma kofar dakinta kwado padlock,,, kamar yadda takeyi idan zata fita ,,
Gidan su yar Ammo mai masa tafara shiga don jin ko maganar gaskiya na ttajiya,
Aiko tana shiga, cikin gidan su yar Ammo ko gaisauwa bata barin sunyi tace
Tace aho yar kulu, agaishiki,
Inata ingwaiya,
Kun kwan lahiya,
Kedai wagga an ko gaisuwa ban bari munkayi ba,
Shin nicce ko ke jiya
Minana, inji ina,
Batunga da anka hwdi mana Ganiye ta tazaka naniyagga da cutar kabari kusa,
Ke ga dadi yayi kai ke nan,
Ta ballo goro da tadauko daga cikin radan ruwan ta ta balla ta miko wa inna dan guntun balli,
Inna ta ce a,a ha, aini yanzu sam banicin gora, wadda nicci shi hakana zaita wahalsam,
Shina, sa, dai nibari kedai,
To yanzu a,a ankaciki da ita shi,
Kedai bari yar kulu am,
Ance saida maigari yakkiranwo dan isa da kainai yamai hwada
Yanzudai can dakin da suka aje tumakainai da can na yaggyara mata,
Jin haka sai tausayin Gajiye ya kama inna tun bata ganta ba,
Ita da su Yar Ammo suka tahi gaida Gajiye inda suka hadu da wasu mata, yan gulma sunyo turuwa sun gano gajiye zasu fito daga cikin gidan,
Suna gani inna sai suka kama magana cimin tausayi
Allah sarki ke gani ba dakanta ttataho gaisheta,
In, nita wallai banzuwa gaida wagga bakan mace
Wadda taimin sanadin batan "yata ta salwanta cikin duniya,
Sherin tana kacin ta,
Inna dai tabi ta gefen su ta raba ta wuce batare da ta tsaya sunyi wani dogon gaisuwa ba,
Cikin gidan kuma suka iske wasu tsatsaye gefe ana ta maida fadi,
A ho yar kulu inji wata bakar mata yar likutitiya da ita,
Kema ketaho nan niya inda Gajiye kiga wadda Allah yai maisheta,
Jin yar kulun da Gajiye tayi an ambata daga cikin dakin da take kwance cikin ban tausayi, yasa ta dan yin yunkurin dagowa da sauri,
Nan take mata suka sa ihu suna shirin watsewa da gudu, don tsoro ,,
Inna ce tai karfin halin shiga don ta leka taga Gajiye saita ganta kwance cikin, kazanta duk ta bata jikin ta, salati ina tayi tadibi wanan matar tace mata,
Habadai inno a,a kuka barin maralahiya cikin wanga kazanta haka,
Ke yar kulu waka zuwa kusa da ita yakwaso wakainai cutar zamani,,
Cikin karfin hali innata ce abata baho ,
Inno ta ce a,a walla wakabada baho nai a halaka mai,
Dan haka inna ta koma gida dasauri ta dauko bahon ta sabo da hafsi ta aiko mata, dashi lokacin da ta haihu ba goyo,
Wanka inna tai mata ta gyara dakin tas tasa turaren wuta na tsuke sai dakin yadan canza kamshi,
Saida ta gama mata komai saita bata dan sauran kunun da suka sha dazu ita da yara,
Hakan da inna taiwa Gajiye sai kawai ta kama zubda hawaye tana cewa inna ta yafe mata dan Allah,
Dan tasan cewa ta cuce su ita da diyarta,
Dan isah ne ya shigo gida cikin sauri lokacin da yan gulma suka fada mai cewa inna taiwa Gajiye wanka,
Can yadan tsaya ta kofa ya ce ,
Shim ina yar kulu inata ce gani nan ,
Yace mikkai ki wanga kasada, innatace tamay fa dan isah,
Wankafa ankace kin mawagga muguyar bakuwa da tazzaka da cutan zamani,
Ganiye na kuka tana fadin ita ba cutan zamani ke jikinta ba,
Hawan jini ne yakamata,
Yace kaji yan nema bakar mugguya, aniyar ki ta biki,
Lokacin da kike, Gajiyen ki wakika kulawa cikin mu,
Yanzu da ciwi yakam maki shinakin kasan kina da yan uwa nananga ko,
Innata ko ni am dan isa karaga mata ko taji dan dama dama,
Shin dawane zataji,wagga tsiyaye dakaka mata ai shizaisa takara kawai kwance,
Hakana inna tadauki dauniyar Gajiye har abincin ta,
Anna cikin haka watarana Allah yakawo Ruggaiya taxo ganin inna ita da mijinta suka zo ma inna da kayan masarufi kamar yadda takeyi bayan duk wata uku uku saitazo ganinsu takawo masu kayan amfani ,
Inna ta ba Ruggaiya labarin gajiye sai Ruggaiya tace kai inna kusan dai duk halinki ashe fadima ta kwasa ke nan,
Inna tace to maye duniya ai mutum bai wuce gaddaranshi,
Allah ya nufi Gajiye ce sanadiyar rabani da yar diyata
Amma ko kusa ban rike taba don nasan cewa komai mukaddarine,
Rugaiyya ta taimaka ita da mijin ta don akai Gajiye asibitin sokoto dan agane ko may matsalar ta,