← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 139

Sashe 76

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har kusan karfe shida sheriff baigan ni ba kuma baiga, na fito waje ba koda ko falon gidan ne,
Duk iya kannewar da zaiyi yayi har dai yakai ga tambayar Amal cewa yau bai gana fito ba koda sau dayane waje, ko lafiya nake,
Sai wannan lokacin Amal ke mai bayanin cewa tunda safe natafi masjidul
Kuma dama nace zan dan dade yau ban dawo ba,
Don haka lokacin da na iso gida suna zaune shida Aziza saman dinning table suna cin abin dinner,
A hankali nayi sallama cikin katafaren falon gidan namu wanda ba lalai bane wanda ke ciki yaji muryan mutun da ga kofar shiga,
Ganin da nayi masu zaune su biyu suna cin abinci yasa nayi niyar wucewa batare da na gaishe suba,
Aziza ce tafara gani ,wanda a zahiri ba haka abin yake ba, sheriff yarigata gani na sai yai wani irin sanyayan ajiyar zuciya,,,
yadai daure ne yai kamar bai gan ni ba , don alokacin inda ban dawo ba da saura kiris yaja almustapha suje bida na,
Aziza ce ke min fadima yau ina kika shigane haka tunda safe naje dakinki yafi sau biyu ban ganki ba,
Naso mudan fita zuwa cikin gari kadan,
Saina dan yi mata murmushi yake kawai badon komai ba sai wanda ke gefenta dake min wani kallo
Da ban iya cewa ga irin shi ko ma,anar shi,
Bangaren da nake tsaye yadan kalla yace min ina tafi ,
A marairaice kamar mai shirin kuka nace mai masjid natafi,
Yar karaman harara yasakar min yana kada spoon a plate yace,
Oho ashe yanzu duk inda kiga dama saiki sa kai kawai ki tafi batare da sanin kowa ba,
Nankan shiru nayi masa don banda ansan da zance duk da dai na fada ma Amal cewa zan fita,
Yace je ki duk abin da kiga yafi maki je ki yi tunda ba ki under control din kowa,
Jiki ba kwari batare da kuma na iya cewa yayi hakkuri ba na shige ciki, abina,
Tunda dai nasan cewa ba wani mugu wuri naje ba,
Ina shiga daki,na Ko Nanfal dina ban cire ba,Amal tashigo dakin tana cewa
Gaskiya yau fadima baki kyauta tun safe fa kika fita duk da nasan cewa ga inda kika tafi ai bai kamata ki kai har dare haka ba,
Don nagajarce zancen ko zan samu saukin bacin ran da naji nace,
Amma dai Amal na fada maki ai kafin in fita ko,
Kafin Amal tace wani abu sai naji murywn sheriff yana cewa
Don kin fada ma Amal ni kin fada min ne ko,ko zaman Amal ki keyi a nan,
Kaina yana kasa don ganin da nai wa sheriff tsaye a tsakiyar dakina
Yacigaba da fadin idan wani abin yaje yasa may ki can fa ya kike son muyi
Ace tun safe mutum yabar gida sai yanzu yana mai diban agogon hannun shi,
Acikin sanyin murya nace mai dan Allah kayi hakkuri bazan sake irin haka ba insha Allah,
Ido yadan kura min nadan wani lokaci kamar mai nazari na tukun sai kuma ya juya yabar dakin batare da yakara magana ba,
Dagani har Amal wani irin ajiyan zuciya mukayi na fargaba,
Amal takai zaune saman gadona tace min gaskiya Fadima yau kin batawa yayan mu rai sosai wlh,
Yayi fadan fitar ki ke kadai batare da kowa ba yace wai laifina ne da nabari kika fita kedaya ban hanaki ba,
Murmushi nayi nakai zaune ina cewa haba dai sakace wata bakuwar gari ,
Bace wa zan yi halan,
Kada dai ki kara irin wanan halin pls,
Kofar dakin aka turo maman Umar ne dauke da abinci kala kala cikin wani dan keken tura abinci zuwa dakuna,
Cikin mamaki naje cewa may yasa takawo min abinci har daki aida tabari infita waje in diba ko,
Dukawa tayi tafara zuba abincin tace min sheriff yace mata ta tabbatar da naci abinci kafin in kwanta,
Amal dake zaune gefe na tadan tabe baki tace kaji yar gatan yaya ko har da abincin ma sai yasa a,yi gadinki har ki ci ko,
Maman Umar tace ai hakan yana da kyau don kinsan cewa fadima ai zaman amana take gare shi kin ga ai dole ya kulata,
Taciki abinci kala kala aplate tamiko min daga inda nake zaune a bakin gado na,
Kawai don tace min ance mata sai naci shiyasa nadan tsakuri abincin kadan,
Nace mata na koshi saidai fruit salad din duk munsha har Amal din,

Nasan cewa yanzu sheriff yana falon shi yana tura sakonne a system din shi,
Duk dare sai yayi wanan aiki in da duk yake
Hakan yabani damar fitowa don in kara bashi hakkuri kamar yadda Amal da maman Umar suka ce min
Dogon rigace ajiki tunda nafito wanka na sauya ta,
Sai plat shoe's ne akafa na shi ma baki mai photo yar kwakwa karama kamar buzubuzu haka,
Ganawa wautar na manta cewa da ba yanzu bane don haka ko mayafi ban dauka ba , tunda naga cewa ai a cikin gida ne kuma sheriff ne fa wanda yasan ni tun ina yar karamana,
A hankali na tako har inda yake zaune saidai ba sakon yake turawa ba shiru yayi yarike gefen habar shi da hannu guda da alamar tunane yake yi,
Jin motsin da yayi a bayan shi yasa yadago a hankali yadubi gurin da yaji motsin,
Sai mukayi idi biyu dashi, amma sai naga kwayar idon shi ya kada yayi ja sosa,
Da sauri batare da tunanen komai ba nace subbahanallah ,
Barci kakeji ne, nasa mu kaina da tambaryan shi,
Shiru nadan wani lokaci bai ansa min ba,
Saidai yadan girgiza min kai kawai,
Ikon Allah saikuma nakara cewa kana ciwon kai naga idon ka ja,
Murmushi yau sherie din yai min da alamar tambayar nawa ya bashi dariya
Yana mai kura min ido shi ja da suka rine yace, min,
Bawa ni ciwon kai illa keda keson ki tarwatsa min kwakawalwata, fadima har ke zaki fita kibar gida tun safe har dare baki dawo ba,
Cikin sauri nakai durkushe a kasa nace mai kayafe min dan Allah insha Allah bazan sake ba,
Da wata dakusarshiyar murya ya ansa min yace gaskiya baki kyauta min ba fadima,
Kaman zan yi kuka nakara cewa ya yi hakuri pls,
Kafin yai wani mafana sai mukaji muryan Aziza abayan mu tana cewa haba dai habibi,
Ai tunda har ta bada hakkuri takamata ka yafe mata hakana pls,
Tazo inda nake tsugune tadan dagoni tace mai haba dai ai koda laifin da tayi yafi haka yakamata kayi hakuri ,,
Kujeran dake gefen shi ta zainar da ni tana mai dan jan shi da hira irin ta masoya duk da na lura bai son ansa mata sai dai yace eh, ki uhum atakaice,
Saidai takan dan jefani cikin hiran nasu jefi jefi,
Hira sukeyi abin su, cikin kwanciyar hankali, a,takure nake a cikin su kamar wace a ka tsure,
Amal ce tafi daukan cup a kitchen tagan ni zaune acimin su,
Daman hanyar gudu nake bida,
Aiko ina ganin ta na mike ina mai yi masu saida safe ,
Aziza ce ke ce min kin gudu ke nan fadima baza ki zauna muyi fira ba ke nan,
Kada ki manta cewa gobe tunda safe nake son mi fita,
Kafin ta kai karshen zancen yatare da fadi ba inda zan fita kuma, tunda nafita yau,
Da mamaki take kallon shi tace mai ai guri. Gyaran kai kawai zamu tafi
Nidai ban san ya suka karasa ba na wuce nabar su, abina,
Washe gari ina son indan motsa jikina sai na fada kitchen wurin masu aiki tare mukai aikin da su
Najera komai a dinning table din falon ,kamar yadda nassba yi da kafin intafi school,
Lokacin da sheriff yadawo gida shida almustapha, direct sashen shi yanufa
Saida yan gyara jikin shi yarage yawan jayan dake jikin nadhi bayan ya watsa ruwa,
Sai yafito ,wurin abinci ya nufa don shi baya cin abin a waje ko ya ya kyau abu yake sai dai wanda aka girka agidan shi,
Don haka da yadawo yai wanka yadan kintsa kafin yai komai sai ya fara cin abinci tukun
Zaune suke da Aziza sai salim da ke tare dasu Amal tunda aziza tazo takaurace ma yawan zama falon sam,
Acewar ta wai aziza batai mata ma,
Wai ruwan yan duniya ke ga aziza,
Don hakane ma bata son irin yadda taga inayi da aziza din,
Cibin farko da yakai bakin shi sai ya tsaya cak ,
Duk wanda ke table din sai ya bishi da kallon mamaki komai yasa ya dakatar da cin abincin ,
Fadima ya furta a hankali Aziza ta ce fadima ya ce na,am sai tadan fara waigawa kozatagan ni afalon,
Ga mamakinta batagan ni saitace mai yafaru da ira,
Cikin murmushi yace mata ya akagi tashi kitchen ai muna girki,
Aziza tace kamar ya don ban fahinta ba sai yace mata, wana girkin nata ne,
Har suka kare cin abincin tana mamakin shi,
Wani irin shakuwane a tsakanin mu haka ace har da girki in nayi zai gane,
Dan murmushi tayi maikama da na mugunta,
Batayarda ba sai da taje kitchen din ta tambaya suka ce mata tabbas nice nayi girkin
Dakina ke ina kokarin jona waya a cikin chaji naci kam shin turan sheriff a dakina ko ban diba din ba shi,
Ya saye da jallabiya mai ruwa assh colour,
A bakin kofar dakin ya tsaya yana karewa dakin kallo kamar yau ya fara shigo,
Tambaya ya jefo min da ga inda nake tsaye,
Ya akayi nai,cooking yau agidan nan,
Cikin mamaki na dan kallo shi nace mai cinkin han kali
Kawai dai nayi ra,ayin yin hakane,
Saida yadan dade tsaye yana min wani irin kallo mai kama da kallon sha,awa, sai nai sauri nadan waiga in ko may yake kallo a jimina hakana,
Hakan da yagani sai yai saiuri ya juya yabar dakin,
Mamaki wanan sauyin na sheriff nake ji saidai gaskiya ban wo komai araina ba,
Sai kawai na shere zan ce,,,naci gaba da aikina
Waje muke kusan duk kn mu gidan muna shan iska ne saboda mudan shakata,
Chapter 76 · 0% Book details