← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 139

Sashe 95

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jirgi dare ya biyo zuwa saudiya, A, Riyadh ya sauka ,
Daga Riyadh, shiga mota sai madina,
A madina safiya tai ma shi,,a cikin gidan mu,,
Mudai mun tashi munga bako don mun san cewa saura kusan sati guda ko kwana goma yadawo,
Tsaye nake bakin dressing mirrow dina ina dan gyaran jikina saboda ina son inyi samako zuwa wurin salimat inci abinci,. Don yau natashi ina jin yunwa sosai,
A, hankali yaturo kofar dakin cort din shi na sagale a kafadan shi, hanaye shi zube a cikin aljihuwaye shi,.
Waigowa nayi don inga kowaye yashigo min daki a lokacin,
Kafin ma in karasa juyawa hanncina ya isar min da sakon sheriff ne,
Mamakin gani shi na yi a wanan lokacin da safe haka,
Don nasan cewa badai ta madina yai landing ba don da Salim ya tafi dauko shi,komai dare
A hankali yatako har inda nake tsaye yazo ya rugumay ni ta baya,
Yana kokarin juyo dani don in yi facing din shi da kyau,
Cikin yar siririyar murya nace mai sannu da zuwa ya hanya a lokaci guda,
Dan murshi yayi dai, dai lokacin da ya man na bakin shi cikin nawa yana fadi a hankali wani zan ansa maki cikin gaisuwar,
,Alokacin kuma maman Umar ta turo dakin don ta kawo min abin breat fast,
Takoma da baya cikin sauri tana fadin muyi hakkuri batasan cewa yana a ciki ba,
Asalima dai batasan yadawo ba, daga tafiyan , ganin ta baisa ya sake ni ba niko duk nauyi da kunya ya rufe ni,
Ta koma da baya baya, tana mai bada hakkuri tajawo kofar dakin,
A lokacin yakara dan matse ni cikin jikin shi sosai, ya dan sun sunan kamshina yana wani lunshe ido,
Amma sai na dan jaye jikina dagana nashi a hannkali, cikin hikima
Sai yadan tsaya tsaye sororo yana kallo na,
Najuya da niyar indan gusa daga gare shi kadan,
Sainaji ya riko min hannu na ta yadda bazan iya juya wa ba da kyau,
Kokari yayi mu hada ido amma sai na kasa saboda gaskiya bazan iya ba don har yanzu mugun nauyi da kun yar sheriff nake ji,
Murmushi yayi yadan kalleni cikin tausayi yace min,
Fatima bakiyi murnan dawo wana bane,
Nadan dago da sauri na kalle shi nace saboda may,
Sai yaji kawai na bashi tausayi, don ko ba komai yasan cewa ina bukatar kulawa so sai a yanzu, da cikina yafara girma sosai
Kuma gashi wana yar ballija,un ta zo ta takuramin,
Sai a lokacin yakare wa dakin da nake ciki kallon a hankali,
Sai yaji wani mugun tausayina yakara shigarshi,
A lokaci guda yaji sam bai kyauta min ba ,
Saiya dan tsaya jin yana dan tunane da nazari,
Yarasa abinda zaice min sai ya sakar min hannu, a hankali,
Wanan lokacin ne rana na farko da yaji yaji kunya na da nauyi na sosai, aran shi
Ada kam baidauki wai don ya aureni zai sa yaji wani abuba akaina, ba
Sai gashi yar karamar yarinyar da yake ji yake kuma gani kamar bata da wayyo , tana batun wuce wa da lissafin shi,
Yau yana jin kunyarta da nauyin ta, sosai
Don yasan cewa an raina mata hankali da yawa kuma baisa tace zata dauki mataki ba, akai,
Ko ta kirashi ta fada mai abinda ke faruwa, ko da a waya ne,
Kenan ta bar mai hukunci a hannun shi, sai yaji wani iri a ranshi yace kada Allah ya kamani da laifin hakkin wanan yariyar fa,,
Bakin mirrow yasa mu yadan zauna kadan, yana facing di na,
Cikin son mu hada ido yake har yanzu , duk na gane nufin shi sai naki daga kaina
Niko sai kokarin gyara Nafal dina kawai, nakeyi batare da na kalle shi ba,
Sai lokacin Yace min fatima lafiya kika dawo wanan dakin da zama,
Cikin mamaki na dago kaina a hannkali na dan kalle shi don tambayar ta zama ta rainin wayo ko hankali,, nake gani,
Yakara nanata tambayar sai na dan dago kadan cikin sanyin murya nace mai ba komai,
Yanayin muryan danayi dole taba mutum tausayi so sai ,,,
Sai yace to may yasa ki ka dawo nan din kuma,
Can fa yafi maki nan, don kinga nan ba wani abin da akasa sosai don jin dadin ki,
Shiru nayi, saikuma na ga kamar ai baisan cewa Aziza tana gidan ba shiyasa,
Yake min mugun tambayar nan, da nake jinta har cikin raina,,,
Ji nayi ya kara riko min hannu karo na biyu,
Yace min ko dakin bai maki bane,,,
Sai nai rau,rau da ido na kamar mai shirin kuka nace
Matar ka fa ke ciki wancan dakin , tayaya zan zauna a ciki tare da ita bayan tace wanan dakin baidace dani ba
Saboda dakin kune kaida ita,
Asalima ita sam bata yarda da cewa ka aure ni ba don bata da wanan tabbacin,
Cikin hasala gami da mikewa ya ce may yasa baki kirani kin fada min cewa Aziza tana gari ba don in dawo ,, cikin lokaci,
Kinsan fa cewa Aziza zata iya maki komai don ba tausayi ke gare ta ba,
Nace banyi zaton cewa zata iya kai har war haka agarin nan ba don baka nan,
Shiyasa ban kiraka ba saboda nadauka cewa zata tafine bayan kwana biyu,
Yaja dogon nun fashi yana kokari cire nicktie din dake a wuyan shi,
Sai a lokacin nadan daga kai na kalleshi nace mai, ai ba komai tunda ita bakuwa ce idan ta gama abinda takeyi, tafiya zatayi,
Wanan kalami da nayi yafi komai nauyi a tare da shi,har wani dan gumi ya ke keto masa ya rasa abinda zai ce min,
Yai dan tagumi ya kura min ido yana nazarin wasu abubuwa, da ga zuciya na
A hankali na ce mai don Allah kayi hakkuri, ina son in karasa shiryawa don zan fita school ne,,
Sheriff yace haba Fatima wanan hakkurin da kike bani yana kara min kunya da nauyin ki,
Ki daina bani hakkuri dan Allah,ke ce yadace in baiwa hakkuri da zalluntar da Aziza tai maki,
Ke da dakin ki da komai na sirin ki a ciki tasa kikafita kikabar mata daki
Kikadawo nan ki zauna saikace wata bakuwa ko wace batada iko da gidan ta,
Wanan gidan naki ne don ki na saya don farin cikin ki da na yan uwana,
Ita na ta gidan na Dubai da Abuja don tace bata iya zama a saudiya saboda zafi da kuma yanayin garin da bai mataba,
Niko kinga zamana anan yake saboda anan Allah ya tsagamin arzikina,
Kinga ko dole in gyarawa iyalina inda zamu zauna cikin don rayuwa tare da yan uwana,
Dan murmushi nayi mai,irin mai, nuna alamar bakin ciki azuciyar mutum,
Nace bam cancanci kabani hakkuri ba sheriff saboda ko da can nasan wanan rayuwar zai biyo baya daga matan ka,
Babu wacce ban san abinda zata iya ba da wanda baza suyi ba,
Don haka don nadawo nan ai ba wani abu bane saboda duk cikin gida gudane kuma dan bambancin dakin kadan ne kawai,
Saboda haka duk wani cin fuska da aziza ko nafisat za suyi min zan hakkura dashi matsayin ba rayuwata ko lafiyata zasu yi kokarin tabawa ba,
Da sauri ya rufe min baki yana fadin ki daina fadin haka Fatima ,
Ya dade rugumay da ni a jikin shi yana dan shafa min baya kamar wacce tai kuka ake lalashi,ta,,
Sai kuma ya sake ni da sauri naga ya wurga da tie din shi saman gado, yafita waje da sauri,
Ina ganin fitar shi nai sauri na suri yar jakata na fita cikin sauri nabar gidan,
Chapter 95 · 0% Book details