← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 139

Sashe 80

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali nafito da ga dakin likitan jiki ba kwari, Aziza tana ganina ta taso cikin sauri ta tare ni ta na fadin sannu fadima ya jikin naki,
Sheriff na tsaye gefe guda ya tsura min ido babu ko kiftawa, hannayen shi zube a cikin aljihun ,shiru yayi kawai yana kallon mu,
Wani dan takarda da doctor yace zai bani na magani , shine doctor yasa akawo muna don aje asiya maganin
Sheriff ne yakamata yatafi amma sai aziza ta caraf ta karbe takarda tace in zauna taje tadawo tana mai kashe min ido alamar kada in fada ma sheriff komai
Mamaki tabashi na rawan kan da yaga tana yi da ni,
Kofar dakin likitan ya duba inda sunan shi da phone number doctor ke rubuce,
Ya kwashe a wayan shi,
Saida yagama ruburun shi kaina na duke kasa alamar dai bana jin dadi ajikina, sam yasa na bashi tausayi,
Ya dan matso kadan kusa dani yace min mai ke da mun ke ne fatima,
Nai narai narai da idona wanda ya nuna alamar hawaye aciki nace mai nima ban sani ba fa
Aziza ta dawo dauke da ledar magani a hannu ta, tun anan cikin asibitin ta balla min tace min Insha,
Kwanan mu biyu a indiya muka dawo straight zuwa saudiya,
Hankalina gurin karatuna don haka ban ko huta ba na kama ha yar madina tare da Yusuf driver,
Saidai kafin in wuce Aziza taja min kunne sosai akan in bi a hankali dan Allah kada in yi garaje,
Kamar ince mata nifa likita bai min komai ba dan injin kawai yadora min a mara yace min sauka in fita,
Saidai kuma ina tunanen cewa kodai haka din ne dashen cikin da tace za,ai min,
Tunda nadawo Amal take ganin kamar na canza mata, sosai don ta lura da cewa ban son yawan magana kamar da
Sai kuma nida ke yawan cewa muji masallaci yanzu sam ban zuwa saidai in kwanta in ta barci, kawai,
Salimat tadawo da yar diyar tayi wayo sosai yanzu tazama big girl,,
Karatu nakeyi mai wahala yanzu sosai don dai duk inda na zauna sai kawai inta zuba gyangyadi,
Banda wani aiki sai barci,
Zaune muke falo muna hira da Salimat da ta kawo muna yini yau agidan mu kasan cewa yau ba karatu,
Duk irin abinda muka aje na ciye ciye a falon fruit kawai nadan dauka na sha,
Hira muke yi duk kan mu amma ni sai jefi jefi nake basu ansa daga inda nake zaune nadan dunkule wuri guda,
Salim yafito da shigar yan RACE don yana yawan zuwa wurin wasan race,
Gab da inda nake dun kule yazo ya dan zauna,
Wani irin kamshin turen dayasa yadaki hannci na,
Sai naji wani irin a,mai, yazo min a gigice natashi da sauri na
Wani irin kallo duk kan su suka bini dashi, sai kuma suka kalli junan su cikin mamaki ,,,
Ina shiga, dakin na nufi toilet nafara sharara amai saida nayi kamar zan amaye hanji na duk ka,
Amal ce tsaye bayana ta kura min idon mai nuna kallon mamaki,
Gado na fada nadan kwanta don inda huta saboda jikina duk yasake min,
Tunda muka dawo saudiya sheriff ke kula da yadda aziza ke wani farin ciki tana nadewa wuri guda,
Hakan yasa ya maida hankalin shi sosai gurin ta don yana son ya fahinci ko may ke faruwa da i ta hakana,
Saidai bai fahinci komai daga gareta ba,,amma hakan baisa ya daina sa mata ido ba,
Tare suke shi, da Aziza a cikin motar shi ke tukawa yau ba driver ba zai kaita wani shagon saida kayan shafa,
Saboda yasan cewa shagon na matane, yasa yacewa Aziza ta shiga ta fito
Aziza ta dauki yar poss din ta data sa kudi a ciki tabar babban jakar nata acikin mota saboda nauyi, ciki harda wayan ta,
Tana shiga sai ya dan gyara zaman shi a kujerar ta, a hankali,
Wani dan farin takarda yaga zai fito daga cikin jakar nata,
Sai yai zaton cewa kila wurin sauri ne ta jawo takardan gashi har zai fadi kasa,
Abinda yagani shiyasa shi gyara zama cikin firgita, takarda ne risit, na Artificial Insemination pregnant, mai dauke da sunan hajiya dakuma wata,
Yarinya yar kimanin shekara sha takwas da haihuwa,
Date ya diba sai gaban shi ya fadi, ras, saboda daidai ne da kwanan watan da Aziza tace tace mai likita yace ya na bukatar suje tare da shi a gwada sperm din su agani ko zai iya produced din baby acikin sauki,
Tabbas kuma sunje din har an debi sperm din nasu shida ita, an je gwadawa,
Fatima what ya mike zaune da inda yake zaune ya bude ganbun motar shi cikin tashin hankali,
A haukace yake kamar ya cin ma Aziza ciki ya shaketa, don ya matsu ta fito yaji may yasa akai artificial insemination don ya hana ya fada mata yace bai so don shi ba jahili bane,
Kuma wace ce akai ma dashen don risit yanuna cewa ba, Azizar bace,,
FATIMA zuciyan shi takara nanatawa sai yace ina yasan fadima da kaifin hankali da sanin ya kamata,
Kafin yai wani abu sai yaji karar wayan Aziza da tabari acikin jakarta yana ruri,
Kamar ya share sai kawai yasa hannu ya dauko wayar yadan na daukar kira batare da yai magana ba
Yaji murya Hindu ta,na fadin Aziza kina ko kula da time din komawar ku asibiti da yariyar nan don a binciki ko cikin na cikin koshin lafiya,
Bai karasa jin zancen ba ya kashe wayan cikin tashin hankali,
Idon shi ya kade ya komar kamar garwa shi, wuta, don bacin rai,
Aziza ce ya hango tafe tana tafiyan ta na kasaita ta nufo motar su,
Kafin ta iso yayi kokarin gyara motion din shi saboda dan nazarin da yayi akan maganar,
Bayan an gama sa mata kayanta a,buth din motar su tashigo motar tana fadin wassh Allah na duk na gaji tana mai kokarin dauko jakarta tana sa poss din ta ciki,
Fuskan shi ta dan kalla sai taga duk yanayin shi yacan za,
A hankali takara diban shi tace mai may yafaru taga duk ya can za lokaci guda,
Saida yasa hannu ya ahafa sumar kan shi yadan lashi busashen laben shi da yake ji kamar ba miyau,a bakin shi,
Yadan ce mata may kika gani halan tace haba dai sweet habibi, ai ba haka na barka ba
Dan murmushin yake yayi yace mata, kawai waya nayi da masu sauke muna injin din da mukayo oda yau wai kuma sun fasa sai nan da sati biyu killa,
Taidan dariya maikama da fito tace to ai ka huta, kai kenan kullun cikin aiki baka da hutu,
Har suka isa gida ita kadai ce keta zuban ta, bai ce mata komai
Sai tunane yakeyi yadda zai bullo mata idan ya kare binciken shi,
Tsaye yake da waya a hannu shi,yan saye da farar jallabi mai dan yagwai a gabn rigar anyi kamar anyi saka ajikin shi,
Noban Salim yake kira don ya fara tambayar shi,
Bayan salim din yadauki waya sun gaisa ne,
Ya danyi shiru jin kadan can yace ma Salim duk lafiya kuke ko Salim ya ansa da eh,
Yace, kowa na zuwa makaranta kamar yadda yadace ko suka ce mai eh,
Can yace to ita Fatima fa lafiya take, yakara ansa mai da eh Salim din yadan daga wayan yakamar yayan nashi yana ganin shi,
Sai kuma yakara maida wayan a kunnen shi ,,yacigaba da sauraren dan uwan nashi,,,,,,
Kashe wayan yayi cikin damuwa yasa hannayen shi biyu ya tokare su ga karfen da ke kofar su,
Yai shiru, tare da yin tunane kala kala azuciyar shi,

Duk irin abin cin da salimat tasan cewa ina yawan ci su tagabatar min a gabana
Kassh amma yau kamar ta aje min guba nake ganin abincin,
Zargin salimat yafito daidai lokacin da na toshe baki har hanci na saboda wani amai da nake ji, yana taso min,
Sai bayan nagama aman nadawo falon ta, na zauna hankali,
Salimat ce naji ta dafamin kafada, ahankali nadago idona na kalle ta,,
Saida, ta zana kusa dani har takai muna iya jin hucin juna tace min fadima may yasa may ki,
Da sauri nadago nace mata may kika gani halan Salimat,
Nadan gyara daurin dake kaina kadan nace mata kawai ina ganin cikina yai min dadti ne kawai,
Ido ta kura min tace look fadima kisani cewa ba wai daukar wasa nai maki ba jinki nakeyi tamkar yar uwata taji kaunata wacce muka fito ciki daya da ita,
A hankali nadan dago kaina kalli Salimat sai kuma na dukar da kaina kasa,
Tabbas nasan cewa ban jin dadi jikina duk kwanakin nan, ba abinda ke min dadi gashi sam bana son jin koda kamshin ture na hatta sabulu wanka idan naji kamshin shi zuciyana duk sai ya tashi,
Indinga jin amai na taso min
Wanan karon hannu na biyu duk ta hada wuri guda tadan kara matsowa gab dani ta kalleni da kya sai naga wasu hawaye suna fitowa daga cikin idon ta zuwa kumcin ta,,,
Kai muka hada wuri guda nida ita mukayi kuka mai isar mu saida muka gaji,
Can tai karfin hali tace fadima wayai maki wanan abin
Waya cuci rayuwan ki haka
Ya akayi ki ka aikata zina,
Kalman da tasa na zina ciki shiyasani kallonta da sauri ina ce mata la,la,la tunda nake ban taba sha,awar zina ba balle har in aikata ta,ta,,,,,
Ta kalleni da kyau tace min waiyai min ciki toh
Dukar dakai na nayi don bansan ta inda zan fara mata bayani ba,
Kawai sai na dake mata akan lafiyata kalau, kawai dai banajin dadi ne,
Ido kawai tasa min bawai ta yarda da maganar da nai mata ba,
Chapter 80 · 0% Book details