← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 139

Sashe 136

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Doctor kamal nakira batare da na sheda wa sheriff ba wanda nasan cewa yanzun ma koda zamu kirashi ba,za mu samay shi ba ma,
Doctor ya iso cikin wani dan lokacin da ba mai tsawo ba ,
Sun gaisa da su Abba da kuma tanbayar su gajiyar hanya,,
Tashi nayi dan inbasu guri saboda doctor ya gana dasu,
Inda nake zaune mariya ta fito cikin kwaliyar ta kamar wace zata unguwa,
Kujerar da nake zaune tazo ta zauna a gefen hannun kujerar tadan rankufo da ka ta tana kokarin daukar mu photo da wayan ta,
Tureta nakamayi ina fadin wallahi mariya zan bata maki rai fa,
Doctor na tsaye daga kofa dakin da yafito yana muna kallon cikin murmushi,
Ni na fara ganin shi a inda yake tsaye nace mata tadiba ga doctor yana kallon mu fa,
Karasowa yayi yasa mu daya daga cikin kujeran inda muke zaune,
Mikewa tayi tadauko may abin sha takai mai har inda yake zaune,
Magana mu keyi dashi amma hankalinshi na gurin mariya wace ke duke tana zuba mai drink a cup
Tana gamawa ta mike tana fadin anty zan tafi gurin su mama, ta wuce abinta,
Tana bacewa sai na ji yai wani irin ajiyar zuciya ya waigo yana mai shafar kan shi daidai lokacin da ya kwakwadi drink din ya aje cup din a saman stol din yace, min,,
Fadima ki bani wanan kaunar taki mana pls,,,,
Jin maganar nayi kamar a mafarki dan ban taba zaton mutum kamar doctor kamal har zai tsaya yace wai yana son mariya ba,
Kamar yasan abinda nake tuna ne sai ji nayi ya katse ni da fadin,
Ko nai mata tsufa ko fadima, murmushi nayi nace mai ,a a ni bance ba,
Ai,gata nan ga ka sai ku shirya a tsakanin ku, ni ba magana ta bace,
Ido yadan tsura min don ya tabbatar da magana ta ko da gaskiya ce,
Can ya, mike ya na fadin shi ke nan insha Allah zan gwada sa,a ta, in gani
Amma sai kin bani nobar ta dan in fara tanan in gani,
Ina dariya na fara karanto mai noban nata yana loading a wayar shi,
Yai min sallama tare da fada min gobe insha Allah za,a kawo Abba asibitin su,
Godiya sosai naima akan zuwan da yayi cikin lokaci yace haba ai nima mahaifina ne ko,
Sai bayan da mukayi sallah magrib nakoma shiyan da su Abba suke dan mu kara gaisawa da su,
Cikin ladabi na gaishe su amna sai Abba ne kawai ya karba min gaisuwar tawa, a lokacin,
Jin shirun da yayi mama bata karba yasa Abba fadin ana gaishe ki fa
Sai cewa tayi aina karba ko indai kuwa zan ma yar mulkin naku ba,
Murmushi nayi kawai dan dama nasan cewa za,a rina
Don tunda nashigo dakin take watso min harara,
Nakara yiwa Abba bayanin akan yadda doctor kamal yai min na cewa tun da safe kada ya karya akai shi asibiti don awo,
Cikun murya kamar mai masifa mama tace ba yariga yai muna bayani ba
Ko aiko ki yayi kikara fada muna,
Abba ne ya tare da fadin nagode kin ji fadima Allah yai maki albarka keda zuri,ar ki,
Na ansa da fadin Ameen Abba na gode Allah yaba ka lafiya,
Yai dan murmushi yagyara daga shingidar da yayi kadan yace kayya fadima Allah dai ya kyauta kawai kin ji,
Daga haka bayan Ameen din da nace na mike jiki ba kwari na bar dakin ina mai masu saida safe,
Wayan sheriff ne ke kirana a lokacin,
Bayan mun gaisa ne nake sheda mai zuwan su Abba,
Har yaso yatayar da hankalin shi sai nake sheda mai cewa ai doctor kamal yazo diba shi , dazun nan,
Yaji dafin hakan so sai dan har da godiyan yaso yai min na ce mai bana son haka na pls,
Mukayi sallama bayan mun dan taba hira dashi,ina zaune lokacin a daki na,
Mikewa nayi tare da kulle kofar shiga dakina,
Nafito nafara zuwa gurin su, mama da Tumba don indiba yaran,
Sai na iske har mama ta basu abinci tai,masu wanka har sunyi barci, ko, daga can bayan mun dan taba hira kadan, dasu,
Dakin mariya nafada kuma,don duk dare kafin in kwanta sai na bisu naga halin da suke ciki, zaune suke ita da Aisha har da maman Umar suna hira ga wayar ta na wakar hausa, a gefe,
Direct wajen wayar na nufa nakashe ta dariya takama yi min tana fadin ai dama tun da na shigo tasan zan kashe wayar ne,
Zama nayi a bakin gado muka fara hira da su hiran ,bukin Amal suke muna na zuwan su, Sudan kai amarya,
A cikin gatse na ce masu saura mukai wa yan Niger tasu amarya su kuma muga yadda za suyi muna ko,,
Har suna saurin hada baki suna fadin cewa wace ce za,a kai Niger kuma,
Ce masu nayi watace nan makwabciyar mu ce ,
Maman Umar ta kalleni tana dariya tace min ai ina ga kamar bukin suna za mu fara sha kafin na makwabtar ko,
Dan murmushi na yi na ce mata har da ke cikin yi min sheri ko,
Washegari duk yadda naso Abba yai sakko hakan bai yu,yuba saboda kofar dakin su yana a rufe alamar basu tashi ba ke nan gashi rana, har ya soma fitowa a lokacin,
Sau biyu sheriff yana bugo min waya don yaji ko an tafi asibitin,
Saida taga dama don kanta ta bude side din, kafin su fito sai da aka dauki wani dan lokaci,
A raina nace lalai wanan matar takai muguwar gaske, dan ciwon ba a jikin ta yake ba, shi yasa tai haka ko,
Tana fitowa tazauna cin abinci Abba yana zaune cikin jallabiyar shi fara,
Na,zo har inda yake na gaishe shi da kwana tare da sheda, mai cewa driver yana jiran shi tun dazu doctor kamal ya kira waya, tundazu,,
Bayan fitan su na bi bayan su dakallo cikin tausayin Abba wanda sai yadda hjy mama tayi da shi saboda hakkurin shi,
Babu abinda ke damun Abba sai hawan jinin da yai mai kamun kwarai ,,,
Gashi kuma ba wani kulawa yake samu a gurin hjy mama ba
Wace ita ta kanta takeyi yanzu duk karfin haline kawai ya rage mata,
Tare suka dawo da doctor kamal , yazo dauke da maganin da yake son adora Abba akai
Mariya ce yakira yace itace yake son ta dinga ba Abba maganin har kwana uku,
Kafin akara yi mai wani awon, fuskan hjy mama na kalla dan ganin ko zata yarda da abin da doctor yace ,
Ya tsunar fuskan take yi kamar mai jin kashi ko warin mutane,
Wasu takardu doctor ya miko min ina dibawa nai dariya a lokacin ina biye a bayan doctor nace mai,African people's
Takardun shedar haihuwan su twins ne akayi da sunar a saudiya aka haife su,
Da yamman ranan su sheriff suka dawo daga US
Direct gurin Abba ya nufa dan gane ma idon shi halin da Abban yake ciki,
Sai da yagama tambayar Abba lafiyan jikin shi tukun sannan ta juyo ya gaida hjy mama,
Ta ansa mai cike da basarwa, da kuma takaici a zuciyar ta dan ganin yadda Sheriff yakoma cikakken mutun mai fada aji,
Yana shiga side din shi ya samu har na hada mai ruwan wanka ko,
Saida yadan rungumay ni na dan wani lokaci tukun sanan ya sake ni ya fada bayi,
Abinci yaci daidai lokacin da yake gamawa doctor yakira shi dan jin ko ya iso lafiya,
Saida na kwashe duk kayan da yaci abinci na gyara gurin
Lokacin yana yar dakilar system din shi, saidai duk rabin hankalin shi na akaina,
Yana ganin na gama muka wuce bedroom lokaci guda,
Saida na koma side dina na gyara jikina da kyau,
Sannan na isa gurin maigidan ,
Duk da bawani dadewa yayi ba acan din duk da haka duk kan mu kowa na kokarin nunawa dan uwansa yadda yai missing din sa,
Bakaramin soyayya sheriff ya nuna min ba aranan kamar wanda yai shekara baya tare da ni,
Saida koma ya kamamala a tsakanin mu yadan jawo ni zuwa jikin shi kamar mai min awo, yace,
Kin ko tafi awo, fatima, saida naji wani dam don sam ni ban son harkar awon nan ,
Kaina nadan kwantar a saman kirjin si sannan nace mai a,a banjeba gaskiya,
Saboda may tafadi cikin karaji,
Nace kai nake jira kadawo mutafi tare, hanci na ya ja min yace ban san may yasa bakya son zuwa asibiti ba fadima,
Gaskiya gaskiya hakan zai iya kawo muna matsala tunda naga ke baki damu da lafiyan ku ba ke da baby,
Dan haka gobe indan Allah ya kaimu ki shirya tunda safe, mutafi ki ga likita,,
Hakan akayi dan wanan karon har E,D,D an rubutamin ko,
Don yanzu watana bakwai ke nan nake ciki, ina kallon yadda sheriff ke jin dadi a ranshi, har saida ya baiyyana afili,
A hankali nadan sasauta murya na na ce sai a rage bani wahala pls,
Yar dariya yayi yakamo hannu na ya matse acikin nashi gam,
Ce ai likita bai ce haka ba kin ga kenan likita ma kila so yake in kara kaimi fiye da da,
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

🐎ZEEE. MAKAWA🐎
[12/15, 9:59 PM] ‪+234 808 968 1079‬: .✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣9⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAW🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Life Story,,,,,
Chapter 136 · 0% Book details