Sashe 137
Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah yadawo da su Amal saudiya lafiya daga hutun da Almustapha yatafi na aure a garin sudan Tana sanye cikin lafaya duk ta rufe jikin ta lif da shi, Dama sa lafaya ba bakon abu bane agurin ta don su ma garin su shi suke sawa saidai ace ba dukka ba, Kallon ta nayi sai na tuntsire da dariya duka takai mun a baya Sheriff dake kawo wa ya ce cikin daga murya Ke kina da hankali kuwa, Tace yayan mu baka ganin itace ke min dariya dariyar naci gaba dayi nace ashe ba dadi ko, Kin manta a madina lokacin ,,,,, Bankarasa ba tace min ai wancan ya wuce kamata yayi ki tausaya min fadima, Ina can kasan mutane ina ta kewan ku, ashe ke ba ki ma damu dani ba, Nace mata ni na isa acan ban kewar yar uwata Auren ne kawai naga yai maki kyau shi yasa nake dariya kai, Bayan mundan zauna na gabatar mata da abin rabawa a baki, ne sai fira yaushe rabo ya fara a tsakanin mu, Take sheda min cewa tawuce da mutuwar hjy tsohuwa a cikin zuciyar ta fam,, Nace to ya za,a yi sai hakkuri dan hanyar kowa ne mutuwa, Sai zuwa rana kadan lokacin da zan kaiwa Abba abinci Amal tabini zuwa gaida su, Kamar yadda hjy mama tasaba yi wa duk wani wanda ya shafi fanin Sheriff ko Abba wulakanci, Yanzuma da Amal tashigo hakan ne yafaru da ita, Don ko kallon inda Amal din take hjy batayi ba , Abba ke yar hira da Amal din yana tambayar ta labarin mutanen saudiya, Cikin takaici Amal ta kali gefen inda hjy take zaune tana faman wayar karya tace, Tace Allah dai ya kyauta Abba Allah yakare muna kai daga sherin masheranta har kullun, Hjy ta dago idon ta jajaye ta kalli Amal dasu wace a lokacin take shirin tashi, Dakina muka koma muka kara bajewa saman gado muka hau sabon fira, Acikin firar tane na fahinci cewa Almustaph mutum ne wanda bai dagawa mace kafa ko kadan Ita kuma Amal din wanan abin yana damun ta so sai alokacin, Saida nadan nisa nace mata cikin nuna maganar da zanyi mai ma,anace Amal yanzu duk yadda kika samu Almustapha dole ne ki daure da halinsa Saboda rashin sabo ne ke damun ki ke kin a sannu idan har kin saba bazakiyi wanan korafin ba, ai, Shiru tayi tana nazarin zance na can ta nisa tace amma gaskiya duk yadda naso in daure na kasa daurewa fadima, Tunda har ki kaji nai maki complaint kin,san abin nadamu na, Tausayi tabani a cikin zuciya ta, dan nasan cewa ta hadu da wani sabon yanayi ke nan, Zuciya tace to amma ko ai mustapha bai yi kama da masiffafun maza ba, Nace ma kaina kajini da wani zance taya dama ake gane namiji mai wanan irin rayuwar, Hakana dai nai ta bata hakkuri da yan shawar,wari yadda za,tayi, Nakara mata da nuni da yarda da kaddara komai kan,kantar shi ko girma, Addu,a tana rage girman mumunar kaddara ga bawa, akoyau she kamar yadda sadaka yake riga kafi ga mumuni, Abinda duk kagani arayuwar ka mukaddarine ka dogara ga ubanginin ka kar kayarda zuciyar ka ta, raya maka abin da ba daidai ba, Wata nacan tana neman kwatan kwancin wanan rayuwar bata sanu ba, Hakan da ubangiji yai maki shine mafi alherin da koyau she iyayyen mu ke rokar muna ga uban gijin mu, Ranan mun kai wani lokaci munata hiran duniya , Har zuwa lokacin da Almustapha yazo daukan ta don su tafi, Bawani nisa bane sosai a tsakanin mu da su,don kusan unguwa guda muke, Har kusan fita gida na raka ta nida mariya da Aisha, Ina dawo,wa na shige wanka dan ko zanji dan dama ajikina, Tare da alwala nadauro nazo nagabatar da sallah, Ina idar wa marita tashi dakin dauke da Abba zannah a hannu ta Gefen gado ta samu ta zauna sai faman murmushi take min Ina kokarin gyara pillow na ne nake ce mata, wai may ye naga kamar bakin ki akwai zance , Yar dariya tai min tace may kikagani halan? nace sanin halin ki mana, Tace Anty ke nan sai ina da magana zan yi irin haka , Daidai lokacin nakai bayana saman gado ina mai kiran sunan Allah tare da neman tsari ga shedan, Nace mata to nikan sai kuban guri indan rintsa ko kadan ne pls, Wani kallo taimin cikin shagwaba tace zuwa na fa biyu da niyar in fada maki sai na iske ki kuna magana da anty Amal, in koma, Nadan kalle ta nace mata, ainace kina da magana kince min tak, Tayi ma,za tadan gyara zaman ta kamar mai rada tace dama nazo in fada maki ,, Yau kwana biyu ke nan doctor kamal ya na bugo min waya ,, Ido nazaro nace waya fa,? mariya ina dai lafiya ko, Tace a,a fa anty dama wai ya na son zaizo gurinane, Kallon tanayi cikin tuhuma sai tai saurin cewa ,aa fa bani nace yazo ba, Shiru nayi kamar may nazari nace mata toke may kikace sai tace min, ce mai nayi sai na fada maki tukun, Nace o kika daure ni ko mariya, Tana yar dariyar kunya tace a,a wallahi nace ne kawai sai in anyardar min , Na nisa a hankali daidai lokacin nagyara hular kaina nace mata, sai ki bari har in fadawa yayan ki ko, Tai maza tamike tsaye tana daukar yaron tace shike nan zan fada mai idan ya bugo, Bayan ta nabi da kallo ina mamakin karfin hali irin na mariya kamar ta har zata tsaya kula kamar doctor kamal wanda kilama ya kusa haihuwan ta in har za,a bibiya, Amma wai shine har take tsayawa dashi hirar soyayya , Naiwa sheriff bayanin duk yadda mukayi da doctor kamal tun farko , Da kuma yadda muka yi da ita mariyan yau, Batare da ya kalleni ba yai yar murmushi kawai yace Allah sa alheri a ciki na kuma yiwa mariya murnan dace da mutun nagari kamar kamal,,, Mariya wace ke Allah Allah taji ko sheriff ya amince saidai bata da yadda zatayi ne tai shiru, A daki nasamay ta nai mata bayanin abinda yace kasa boye murnan ta tayi a gabana, Tun wanan lokacin doctor kamal ya fara zuwa zance gurin mariya, Don haka duk wani plan na sheriff akan karatun mariya ya tsaya, Cikina yanzu ya shiga wata na takwas kenan, saboda haka yai min dan tsawo a gaba duk wanda ya ganni sai ya tausaya min, Sheriff zaune akan saman wata yar kujer office irin mai juyawan nan, , hankalinshi na gurin system din shi Da alamar duk abin da yakeyi mai muhin manci ne so sai don harda Ummibanan taso yadauke ta amma yadan lalashe ta tai barci, Doguwar rigace fara,kal,ajikina mai shara,shara mara nauyi, sai hular da nasa akaina , Duk jikina kamshin turaren alrahab ke tashi, sai yar lipstick dana dan zizara a bakina, Fresh milk na dauko mai sanyi kasancewar zafin da akeyi a yau din, Komai sanyin A,C sai kaji dan dum kadan zaune yake na nufi gefe nadan aje mai milk din duk cikin rashin sanin na iso gurin, Kamshin turare na ya shaka hakan ya nu a mai cewa ina kusa da shi, Daidai lokacin da zai dan juyo a lokacin na kwanto mai a bayan shi, Wani irin sanyayyan ajiyar zuciya yayi har sai da na dan daga mai ajikin shi, Aje aikin yayi ya juyo inda nake muna fuskantar juna nida shi, Hannu na namika najawo mai cup din milk din na nufi bakin shi dashi, Babu musu ya bude bakin nafara bashi yana kurba a hankali yana mai lunshe idon shi, Saida ya kusa shanye cup din milk din yai min alama da kai ,ya ishe shi hakana, Namaida cup din sama dan stol din na aje, Zama nayi wanan karon a saman ciyar shi ina mai wasa da sumar kan shi, Hannun shi yadauka yasa daidai saitin cikina kamar mai son jin motsin baby alokacin, Aiko bai kai ga cire hannun shiba yaji wani bul,bul alamar motsi a cikin, Cikin razana yai saurin ya cire hannun shi kamar wanda za,a rike, A hankali yadan dago kai yakalle lokacin ina mai dariyar irin reaction din da yayi, Na kalle shi cikin natsuwa, nace mai nifa wanan karon jinake kamar ma banda ciki pa, Da sauri yace min a hakan na dan rausaya kaina nace mai kwarai ma, kuwa, Kowancan ma nasu twins sai da na kusa haihuwa ne kafin intafi Nigeria yafara dan damuna, Yadan sasauta murya kamar mai rada yace min ashe sai in ci gaba da,,,,,,, Cikin sauri na rufe mai baki yadan kai min cizo kadan a hannu, cikin sauri na cire, Namike da kyat ina fadin barin barka ka karass aikin ka kada in damay ka da surutu, Yace kamar kin san bincike nakeyi akan wasu kaya na Abba wa yanda suka bace , Ashe su, Suraj ne suka saidasu ba tare da sanin Abba ba, Har da wasu daga cikin filayen shi da gidan jeshi, Suna sayarwa suka gudu suka koma inda suka fito batare da sanin Abban ba, Hankalina na mayar dan jin wanan labarin mai cike da tashin hankali, Batare da natashiba saman jikin shi yaci gabada fada min cewa, Ai,yau babu komai don duk sun kashe kudin har sun fada cikin rikici, Yace yanzu haka shi babba an harbe shi a kafa agidan rawa yana jinyar kafar ne, Shiyasa uwar tace ma Abba yazo nan don kada su tagi can yagani hat yaji ba,asin hakan, Shiko suraj ya auri wata baturi wace suka dade tare har sun ma haifi diya buyu kafin ai auren, Ido na waro waje kamar mai shirin ihu, Yace yes, yanzu nasa aimin bincike akai in har yayi auren ta yadda yadace zan yi kokari in tallafa mai, Nace mai to shi gudan fa,ya ce min yana can wata kasa suna waka a Jamaica, Innalillahi kawai na kama maimaitawa ina cewa subbahanallah Allah ubangiji ya shirya muna su, Yace min Ameen Fatima, nace ya Allah ka shirya muna zuriar mu ta hanyar alheri, Duk sai naji banji dadiba wallahi jiki ba kwari natashi daga jikin shi ina mai yin addu,a