← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 139

Sashe 32

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kowa yasan yadda garin makka ake kwantsama rana kamar kace wayyo Allah
Yau rana a,keyi sosai don haka mutane sun samu wuri sundan lalabe
Duk da zafin ranan da akeyi bai hana masu niyar fita wurin ibada yi ibadarsu ba,,,
Saboda kowa yasan cewa kulun cikin baki garin yake masu zuwa ziyara,
Da wuya ai ruwan saman da yakai sau biyar a shekara cikin makka,,,
Zafin ranan yai yawa da alamar yau akwai rabon ruwar sama ke nan agarin,,,,,
Iska ce a,kafara masu kaya nata har,harada kayan su ,don kada ruwan ya samay su,,,
Daidai wànan lokacin muma muna saman titin,57up ,,
Almustapha ne ke jan mu yau sai nida ke gefen, driver
Amaryan sheriffudeen din, mu tana baya zaune tana ta latsan wayan da,ke hannun ta,
Yau,ce ranan farko da muka fara fita da ita,
Itamadin inga fitar ta kenan na farko,
Taso fita ita daya amma sheriff yace baiyar da ba dole duk inda zata saidani,
Wanan dokan yai mata zafi sosai,
Don agabana akai case din ,
Tafito cikin shirinta tasa wasu kananan kaya tana tako daidai ,
Shikuma yana zaune falo gaban laptop din shi wanda zance shine abokin hiran shi koyau she,
Daga waya sai laptop zaka ganshi da su yana latsawa,
Karan takalmanta dayaji yasa shi dan dago kan shi a,hankali ya kalli inda take saukowa a,step din,
Kan shi ya kawar daga, kallonta ,, sai kuma ya cigaba da abin da yakeyi, batare da ya,waigo ta, ba,,
Ita ko azatonta ta burgeshi ne hakan da take yi,,,
Saida ya bari ta karaso kusa da shi cikin rausaya da rangwada irin na yan bariki,,
Habibi na shirya fa, zantafi,
Batare da ya kalli gefen da take tsaye ba yace mata,
Ina fa tace mai wurin gyaran kan da nace ma da kuma , yin wasu yan sayaya,
Still kanshi na ,a duke yace a,hakan ko kuwa da sauran shirinki ,
Tadan dibi shigan da tayi yace ,ahakali taga ai,baida wani illa, yar dogon riga ce sai dan gyalen da ta yane kanta dashi,
Batare da yakaleta ba yace,,kitunafa nan saudiya ne ba turai ba,
Ko ba komai kina gaban tushen musuluncin ki,
Duk da nasan ba,arasa masu irin al,adan ki amma nidai ba,agida na ba gaskiya,,
Kamar yada , dama na fada maki sharudan zamanki a gidan nan,,
Gaskiya bazan iya lamuntar wanan irin shigar ba,
Sanan ki sani fita daga yau ,bake da driver zaku din ga fita ba dolene, kifita, ke da wanan yarinyar mai kula da duk har kokin gidan nan,
Zamanto duk inda zaki tasani kuma kuje tare da ita,
Saboda haka na,dauketa wanan aikin
Ita wanan yarinyar wace wai da za,adinga hadani da ita,,,
Alamar oho yanuna mata da hannun shi saidai hankalinshi naga laptop dinshi kamar bada ita yake zancen ba
Yadan dago kai yace mata, idan kuma kin ga hakan nada matsala, zaki iya fita ,din fine,,,
Fuskanta ya nuna alamar bacin rai karara, ,azuciyan ta ji takeyi kamar tace ta fasa,,,
saidai kuma har in ta fasa din kanta da yadamayta da kaikayin rashin wankewa ya,zatayi,,,
Dole jiki ba kwari ta zauna ga dayan kujeran dake falon tana cewa,
Ina yarinyar da zamu tafi,
Waya yadauka daniyar akirani sai ya hangoni kusa da su ,nida mai goge gogen falon ina nuna mata, wani aikin da baiyi kyau ba,
Dayake akwai dan nisa a tsakanin mu dasu, sai yai min alamar inzo da hannu ,nai kamar ban ganshi ba sai matar da muke tare ce ke fada min ana magana dani,,,
Cikin ladabi na isa gurin da suke,,, batare da yakalleni ba yake min bayani zamu fita tare da matar shine ,zan kaita wurin gyaran kai .
Cikin ladabu na ansa tare da dan kallon gefen da take ,
Ko kallon arziki ban samu ba,
Muje kawai nace mata,
Kanshi yadan dago dan
bini da kallon mamaki
don baiga ko na dan shiga ciki ba, don indan gyara yadda yaga wasu mata na yawan yi,idan zasu fita,,,,,,,
Tun fitar mu ko kallo na batayi ba, balle muko danyi wani maganar arziki, da ita,
Almustapha ke tanbaya ina zai kaimu,
Atakaice na bashi ansa nace mai nabililabilah,
Batare da na kali inda yake ba
Nikaina ansar bata bani ma,ana ba,akune na ba,sam daurewa kawai nayi nafada mai,
Don ban son yiwa nagabana rashin mutunci sam,,
Amma hakan dai naga damar fada don in fanshe haushi na,,,
Kanshi kawai ya girgiza cikin wayancewa,gamida basar da disgashin da nayi,
Shiya dan daure yace min wani road zamu nakara fada mai a tsiwan ce,
Gaskiya wurin ba laifi don wani kilantacen wurine wanda matane kawai ke zuwa wurin manya da yara,
mun samu mata da dan dama suna jiran layi,
Kasan cewan mun dan san juna da wasu daga cikin yaran aiki yasa na danyi muna hanya wata dabata fito aikin ba ta gyara mata kan,
Aka wanke mata,kafan ta, da gyaran kunbar hannayen ta,
Muja futo zuwa wani dan babban shago tasai wasu yan kayayaki bukatar ta,
Kadan,Pad kawai nadauka a shagon kasan cewa lokacin period dina ya kusa zowa,

To a,hanyar mu ta dawowa gidane wanan hadarin yatare mu,
Sararin samaniya nakare wa kallo yadda lokaci guda yanayi ya canza gari yayi duhu,
Almustapha jan motar shi yakeyi hankali kwance abinshi,,,
A,hankali na mayarda diba na kan matar sheriff ta gefen idona, dai lokacin tai magana tun fitar mu, dani tace Allah ya taimake mu wanan yariyar tasan, wasu, tana magana da almustapha
Tana dan kara leka window motar tace haka ake iska agarin nan,
Kafin ta rufe baki wata irin iska kamar guguwa ce ta taso tuni wuri ya turnike da kura,
Cikin sauri duk muka daga glass din motar don kurar ya mamaye ko ina,,
A, hankali Almustapne,,, yake tuka motar don ko ganin hanya ba,ayi sosai,

Matar sherriff duk ta tsorata tace don Allah mudan tsaya har kuran ya lafa, mukara sa gida don gaskiya tana ganin tafiyar mu a haka hatsari ne
Ganin da nayi zai tsaya yasa nai mai magana cikin larabci,
Nace mai yasan sheriff yace kada mudade ko ,kuma gashu mun kusa kawo wa gida,
Umurnina yabi ya ja motar ahankali,, har muka isa gida lafiya,,,
Daidai isar mu gidan wata iska mai karfi ta kara gwaucewa da ruwa mai karfi yabiyo iskan,
Hakana balle murfin motar nafuto cikin sauri zuwa cikin gida,
Iska na kwasar kayan mu duk tsirangalin kafar mu yana baiyana asarari saboda kada kayan mu da iska keyi,
Atare muka fada falon gidan nida matar sheriff wace ban san ma tana bayana ba,,,
Don nadauka zata zauna amotane har ruwan ya lafa,
Wata ajiyar zuciya na saukar yayin da naji rufewar kofar falon,
Sheriff ne tsaye a tsakiyan falon yana muna wani irin mugun kallo,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
[10/4, 14:28] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Al most true life story,,,

Fuska a a daure yake kallon mu, cikin tsawa tsawa yake magana ,
Ku wasu irin mara hankaline kuna ganin yadda gari ya canza kala ,
Yanayin da kowa ke gudun shiga cikin sa saboda kariyan lafiyan mutum,
Shine ku ka biyo cikin shi haka don rashin sanin ciwon kai,
Cikin hausa yake fadan duk da hausan ba wai nuna tayi masa ba,
Sau,biyo muna hada ido dashi lokacin da yake ta faman fadan,,.
Ina noke kaina a,kasa kamar badani yakeyi ba,
Duk da Cikin fada yake magana sai naga kamar lalashin mu yakeyi ba fada bane yakeyi,
Sulalewa nayi zuwa cikin gida don rigar da ke jikina ya fara jikewa ,don haka sanyi ya fara bimin jiki ko,,
Ido yabini da shi yana mamakin irin girman da ya hango nadan kara yanzu, kafin mu shigo,
Ashe tunda yaga hadari yakasa zaune ya kasa tsaye, hankali a tashe, don baisan halin da muke ciki ba,
Saidai yayi amanan cewa baza mu biyo wanan iskan ba,
Saman dakin shi ya tsaya, dai inda zai iya hango ta,waje yana yi yana dan leken hanya,
Aiko sai gamu cikin wanan uban iskan mun doso gida,,
Mamaki ne ya kamashi haikan ta yadda muka iya kasadan biyo hanyan hakana ba wani fargaba ko tashin hankali
Har fitowan mu yana kallon mu da yadda iska ke kwasan mu kafin mu shigo gidan
Cikin sauri yarigamu isowa falon bayan yariga ya kare muna kallon mamaki ko rashin hankali,
Itama wucewa tayi batare da tabashi hakkuri ba, don gani take gaskiya ya fara takura mata,,
Chapter 32 · 0% Book details