Sashe 138
Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
abakina, Duk sai naji tausayin Abba ya kamani ace yara uku sun zama bala,i alokaci guda, Allah ka shirya muna kai muna jagora mafi alheri, Daki na nakoma nasamu guri na kwanta jiki ba kwari, Har sheriff ya shigo dakin yasamay ni a kwance haka,nan cikin damuwa, Hannu shi yasa saitin fuskana yana dan waven kamar mai maganar kuramay, Yana shirin zamane yake ce min yana son muje shopping a kasar Turkish, Banko bari yakarasa zancen shi ba nace mai gaskiya ba,zan je ba , Cikin mamaki yake kallona nace mai gaskiya duk abinda zamu bukata za,a samay shi a nan saudiya insha Allah, Nakarasa da fadin kaga sauran kudin sai kakara ma masu zuwa sauke farali a wanan shekarar ko, Yaji dadin wanan maganar tawa so sai don ido kawai ya zura min yana min kallo cikin sha,awa, Bayan kwana biyu sai ga masu dicoretion din gida sun zo a wanan lokacin muka koma wanan can gidan mu na farko, Kafin sati guda, har sun gyara ko ina sun kuma kwashe nafarkon sun tafi da shi, Subawa mabukata don bamu da yan uwa da zamu bawa anan, Tundaga get din gidan har zuwa cikin shi an gyara muna komai gwanin ban sha,awa,, Kwanan mu guda da komawa gidan muna cikin murna sai ga kiran Abba cikin gagawa yake bidan Sheriff, Duk da Alwashin dayayi cewa bazai kara fita waje ba sai bayan na hai hu , Wanan karon sai gashi yaza mai dole yafita, zuwa ansa kiran Abba, Don a yadda yaji muryan Abban a waya hankalin shi ya tashi sosai gaskiya Allah Allah yake yi gari ya waye yai process din tafiyan shi, Ina tsaye daidai lokacin da nagama rufe mai, zip din yar traveling bag din shi , Ya na tsaye ya na waya cikin fada, fada saidai da harshen turanci yake wayar Hankali a tashe yazo inda nake tsaye cikin damuwa yai dan hugging dina yakai min sun bata daidai tsakiyar goshina ya ce min take care of ur selves pls, Kafin duk in sauko in biyo shi har yakai bakin kofa dan gudu gudu yake tafiya, Tsayawa nayi ina mai addu,a daga inda nake ina mai fatan Allah yadawo dashi lafiya, Tashin hankali ya iske agidan don dai gida babu dadi Saboda yaran mama sun sayar da duk wani abin da Abba ke tunkaho dashi , Ashe tun zuwan da kamal yayi sa,an shiga har cikin turakar Abba ranan jumma,a lokacin Abba na massalaci ya kwashe duk ka documents din yatafi dasu, Abba yana hawaye yake sheda wa sheriff, wanda alokacin shima hawaye yake yi dan ganin hawaye tab a idon mahaifin shi, Cikin kuka Abba keba sheriff hakuri murmushi sheriff yayi duk da hawayen dake idon shi ya ce ma Abba ai shi yadade da sanin haka Yadaiki fada wa Abban ne kada ran shi ya baci, amma Abban yayi hakkuri dan Allah yabar su da duniya kawai itace zata koya masu darasi, Abba na kuka yace duk sun wawashe komai Ahmad may zan bar maka kaida iyalinka nan gaba, Murmushi yayi yagyara zaman shi yace ma Abba shikan Alhamdullahi gaskiya don ko ayanzu yana da abinda iyalin shi har ma da yan uwa zasu amfana, Yakumace yana ma Allah godiya da yabashi Abba a matsayin mahaifi har ya tsaya mai yaga cewa yai karatu wanda zai amfane shi, Kuka mai tsuma zuciya Abba yasa dan jin kalaman sheriff zuwa gare shi, Yana mai bidan yafiya ga dan nashi wanda ada yamayar kamar bashi yahaife shi ba, Hjy mama tana daga waje tana jin maganar su babu dama tashigo saboda warning din da Abba yai mata da dakin shi ,