← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 139

Sashe 21

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinci muka gabatar masu dashi suna gamawa,sai wurin kwana,muka kai kowan su yaga inda zai sauka,, agidan mu mata mu muka taimaka wa su matan zuwa masaukin su,,,,,,,
Duk wanan dawainiyar da mukeyi, da baki maigidan yana zaune a gaban wani desktop din shi dake falon kamar bashi keda bakin ba,,, yana kallon movement din kowa har mu yan aiki ,, amma azahiri zakadauka aiki yakeyi daga zaunen,,,,
Ba abinda da yafi bani sha,awa kamar yar tsohuwar da aka so da ita ,, wace zata iya kai shekara kusan,,, tamanin da hayi ,aduniyar kila,
Duk abinda takeyi hankalina yana gurin ta duk wani motsin da zatayi sha,awa yake bani wlh,,, gata da fada irin na tsofi,,,,
Zuwa nayi nakira Rugaiyya don tazo, ita,ma taga yar tsohuwar mai ko,kari, kamila mai yawan ibada,, ,,,,,
Muka dan labe gefen labule muna lekenta
Zaune take a dakin da akai mata masauki agidan da ,alama tasbihi takeyi a zaunen don bakinta nata motsi ga tasbaha a hannu ta,,,,
muna nan labe bayan dan labulen da muke leken ta,,,Dan hira mukeyi,,,. muna dariya a hankali komai nata yana burgeni
Nace dama ace wanan tsohuwar kakatace,,,wlh Rugaiyya da naji dadi so sai naso ace nima ina da yan uwa haka har da kaka,,,, da kullun ina tare da abina ina bata kulawa,,,

Koda ban waiga ba,naji kamshin turaren shi ya bure muna hancin mun hakan ya nuna muna cewa maigidan ya gurin,da muke labe,,,,,,
Da sauri na sake labulen da na dan hankade muna leke.
Nayo baya daniyar gudu sai kawai na,ji na yi karo da kafa, shi,,,
Ahankali, nadago kaina nakai dibana gare shi,,, fuskan shi a daure murtun,,,
Muka dan zagaya ta bayan shu muka wuce sim sim da mu,,,
A,she duk abin da muke fadi yana tsaye bayan mu hannayen shi cikin aljuhun wandon shi,,, ido ya zubu muna, har muka bace mai,,,,,,

Bayan su yabi da kallon mamaki ,, azuciyar shi yace may wa,"yan nan yaran ke nufi ,,,,
Suna nufin basu da kowa ko may ,, lalai sai na samu time inji labarin su,,, yadan leka don yaga may muke kallo wurin tsohuwa,, yaga ai zaune take tana ibada,,,
Murmushi yayi yace mai ran karfe ke nan hajiya tsohuwa ,,,,
Ba ita ba ba mai iyawa da hjy mama,,
Don yasan ko wanan zuwan da akayi da ita don shine tazo,,
Tunda Abba bai fada mai da ita za,azo bada fari,,,,

Saboda aiki yau mun makara sosai bamuje gida da wuri ba,,,
Almustapha yasa driver ya kai mu gida , don dare yayi. Ana iya kama mu,,,

A , hankali muka shiga gidan namu gami da sallama,
Mun iske kowa na harkan gaban shi , takalmana tomy na cire na wurgat gefen da muke aje takalmi,
Sai niliyata danake warware a hankali, don indan ji iska ajikina , dagani sai yar wando da riga da suka dan matse min jiki kamar wata diyar larabawa kaina dana kule da ribon shima na dan walwale shi don in samu saida agida,,,,
Nakai kallona ga sukaina ina tambayar ta hajiya fa,,
Tace min ita ma bata ganta ba tunda tadawo, ido waje nake kallon Sukaina Don ai wanan rashin imani ne,,,,, aiko banza hajiyace silar zuwan mu nan,,,
Inga mutunci aidole mu mutun ta,ta,,,,,

Daki na fada da sauri na,,,
Kwance na samu,hajiya jiki ba kwari
Cikin tashin hankali nake tambayar ta ko tasha maganin ta,,, ban tsaya jin ansar taba nafita waje da sauri na,,,
Tea na hada mata mai kauri sai ruwan dumi da na jona mata tai,wanka nabata maganin ta, sha,,,,,

Tunda safe kuma na tashi na kara hada mata abin kari , nabata maganin ta,sha,,
Nacewa Rugaiyya ta tafi,ni bazanje ba ,yau,,,,,
Hajiya ce tace min in tafi ai taji sauki yau sosai,,,
Hakana natafi badon raina yaso ba, don gaskiya naso in kula da hajiyan mu sosai,,,saboda tausayi take bani don ni har a raina kamar inna nake daukar ta,,,

Muna isa tun da safen nan muka hada masu abin karyawa ,,,kamar irin na mutanen Nigeria mu,,,
Bayan komai ya kam,mala mun jera masu a, dining table ,,,
Daya daga cikin yan matan nan tafito tace muna, wai baza ta iya cin abincin mu ba, wai akwai warin tafarnuwa aciki da yawa,,,
Duk da nasan cewa bamu sa tafarnuwa ba acikin girkin mu,,,
Saboda wanan dattijuwar matar da muke aiki tafada muna yan Nigeria basu son tafarnuwa don haka kada muyi masu girki da shi,,,
Jiki ba kwari muka kwashi kayan da niyar mukara zuwa mu dafa wani,,,

Muryan maigidan mukaji abayan mu ya na fada, muna cikin larabci mu ,maida komai inda yake mu wuce kuma kada mu dafa abinci rana dasu,,,
Zasu tafi haram masijid yin dawafi daga can zai su wuce asibiti da hjy mama,,,
Yana ma matar da muke aiki tare bayani,,,

Ya juya wurin yarinyar da yakira da mairo, idan abincin baiyi maki ba kina iya shiga kitchen ki dafa abinda kike so,,,
Aikin dafa abinci sau biyu kawai nai alkawari dasu , ba,kowani lokaci suka ga dama suke aikin ,ba
Amma in,kinga zaki iya biyan su hakin aikin da zasuyi maki sai su je suyi maki, wani irin wanda kike ra,ayi ko yafada cikin nuna serious,,,,,alamar ba wasa ga zancen shi,,,
Tsohuwan nan ce abaya shi,ta karbe zancen da cewa ai basu san darajan mutum ba su ,
Sun dauka kowa za,su iya takawa don su na da kudin hakan ,,,
Saboda irin rashin tarbiyan da ba,a , nuna masuba, agidan su,,,
Kasan cewa agida yan aikin su kamar bayin su suke,,,
Sabanin nan da komai a,ka,ida akeyin shi,,,,

Daidai lokacin na iso bakin taburin cin abincin ina kokarin taimaka ma tsohuwar don ta zauna,,,
Plate nadauko mata ,sai kuma tambayar ta da nakeyi cikin hausa may za,a zuba mata,,,
Kallon gefen da Ahmad yake tayi, tace mai,, kai nifa banjin larabcin da wanan yariyar ke min,,,
Tsohuwa ai hausa take maki ita madin, inji Ahmad,,,
Cewa tayi may zakici azuba maki,,,,
Murmushi nadan yi kadan har fararen hakorana suka dan baiyana waje,,,bayan na zuba mata sai na bar dinning area din don in,cigaba da aikina dama don in,danji dumin tsohuwar naje kusa da ita,,, kalon mamaki yabini da shi ,,,,
Ina wucewa naji tana fadin ita wanan min ma yar aiki ce hakan ,,,
Bai bata ansa ba sai mairo ce tace ai tunda kika ganta tana aiki nan kema kin san yar aiki ce
Wata kila anan aka haifeta , ma,,

Dakin yar tsohuwar nan nashiga na gyara mata komai tsab kamar ba,a bata ba,,,
Na kun na kayan kamshi ko ina gidan yadauki kamshi na musan man,,,
Sai sanyin AC da ya karade ko ina na gidan,,,

Ahmad ne yafito daki cikin shirin shi nafita, jallabiya yasa fara tas ma laushi da sulbi kan shi da yar karamar hula fara sol itama, sajen shi ya kwanta lub a fuskan shi kamar shiyayi kansa,,,

Hannu shi rike da dan makulli motar shi,,,,
A tsakiyar falon ya tsaya yana ba Almustapha umurnin kula da komai yadda ya kamata,,,
Mahaifin shine suka fito tare da hajiya mama,, suma a cikin shirin su ,,,
Tana wani yatsine yatsinen fuskanta kamar wacce gidan bai mata ba,,,
Azuciyar ta kuwa sai mamaki takeyi da irin canjin da tagani ga Ahmad ,,, budi da arziki yataso ma yaro kamar shi yafi kowa iya karatu,,,
Tasan duk yadda Alhaji yai mata rantsuwar cewa baida masaniyar komai gamay da,sana,ar da Ahmad din keyi,,,
Ba wai ta yarda bane jira take yi kawai da su koma gida dole asan yadda za,ayi gaskiya,

Tsohuwa ake jira tafito su tafi tace ita atabau baza taje ko ina ba ,,
Su tafi kawai don ita tagaji sai gobe zata fita,
Haka suka tafi batare da ita ba,,,,
Hakalin maigidan bai kwanta ba da barinta da akayi gida ,,, yasan dai da wata a zuciyar tsohuwa,,,,

Suna wucewa nice tafarko dana fara zuwa wurinta ,,,
Ina dan tambayar ta a hankali take bani ansa nace mata Nigeria akwai nisa ko tace min eh ,,,
Kina son zuwa ne da sauri na bata ansa da eh
Dariya tayi kawai don ita tana dauka ni haihuwar can ne,, bansan Nigeria ba,,,
Kafarta da naga tana dan shafawa almar ciwo nace mata ina zuwa ,,,,
Fita nayi zuwa zuwa wurin mama,mai aiki don naga tana yawan,shafa magani ciwon kafa akafar ta dana tanbaye ta sai tace min man zaki ne da na jimina take shafawa akafar,,
Shina karbo nazo na shafa ma wanan tsohuwar nadinga yi mata masaj din kafar a,hankali ,,,,
Kafin wani lokaci har barci mai nauyi yadauke ta ,narage mata karfin A,C ,,,naja kofa ,ahankali nafita,
Saida tai barcin ta sosai ta tashi na hada mata ruwa maizafi tayi wanka tana fitowa nakawo mata abincin ta har daki ,,,,,,,
Miyar kaza da dankalin turawa sai su kabej da saurasu yanuna sosai dai yadda zata iya ci fresh milk a cup amma ba mai sanyi ba kware,,,
Taji dadin wanan kulan da nai mata aranan so sai,,,
Ahmad basu dawo gida ba saida takwas na dare,,,,
Alokacin kuma hankalina yakoma ga hajiya ina son in koma in diba jikin ta inji inda sauki,,,
Gashi masu gidan basu dawo ba, kuma ban iya wu,cewa inbar tsohuwa ita kadai
Don jinta nakeyi kamar mun saba dadewa,,,
Ita ko sai kallo na takeyi ina bata mamaki ,, azuciyar ta tace wanan yarinyar karama tasan yin komai ,,,
Ga wa,"yan nan manyan yan matan da mama ta dauko ko ruwan shayi basu iya dafawa ba, injita,,, gashi kuma don samun wuri irin na mama ta nace sai anzo da su umurah ,,
Duk da tagane wayon zuwan da kayi dasu don Ahmad din,tane sabod,,,,,, ,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 14:06] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣5⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Recite Hassbunallahu wani,imal wakeel 450 every morning if possible pls,,,,,

Soyayyata gare ku bai karewa yan uwa,,, Hannah Rabiu ,Maman xarah ,Ayheert, Precious Hindu, Miss Ayush, Maman Mu,Allim, Maijiddah Harazami, Anty Aynah ,Salamatu sale maina, sai su big antys Anty mariya sb Anty Hafsat Yusuf,Anty Safiyà Abdullahi, da Maman Fareeda,,, all in Huguma groups novels fatan alheri gare ku kullun,,,,

Almost true life story,,,,
Chapter 21 · 0% Book details