← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 139

Sashe 47

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Munje gurare da dama agarin na nuna masu gurare tarihi sosai,
Sai kuma wasu shagunan kaya da muka ziyar ta, da gurare saida kayan abin motsa baki,.
Amal duk ta rude sosai dagani wani katon shago na saida kayan sawa na mata da yara,
Saida naga tagama rudewa ina mata dariya, daga karshe nake fada masu cewa ai shagon Sheriff ne ,.
Na nuna masu wani na saida kayan maza dasu carpet din sallah iri iri
Baki suka sake suna mamaki har cikin mota suna kara tambayana nace masu wlh nashi ne,
Wasu manyan motoci da sukayo loading mutane wanda da,alama baki isowar su kenan motar naga tana ta kallo har tana waige,
Nace mata ai indai wanan garin ne kada kiyi mamaki darin su sushigo kamar haka,
Nace mata gari ne da zaki ga taron bil,adam kamar duk duniya aka tara tundai ranan jumma, ranan da duk yan kauye da kewaye sun shigo ga baki sai kiga garin yazama kamar ba ko isakan shaka,,
Duk da dare yayi saida nakai su wasu shaguna dake cikin kasa inda shagunane sunfi guda dari akarkashi kasa akajera su birjit,
Shagon saida zinare dayafi kowani girma wurin nakaita,
Saida Amal tace min don Allaj fadima mu fita haka sanyin wurin nan ma yai min yawa ga girman wanan shago kada yasani mafarki pls,

Har muka isa gida tana santin shagunar da duk mukaje,
A bakin get mukayi tozali da sheriff wanda yafito da niyar zuwa masallaci sallah cikin jallabiya baka , mai dogon hannu kan shi da "yar fula karama fara, sai Almustapha dake gefen shi shima cikin farar jallabiya,
Tunda na hangoshi sai naji gabana yafadi don musan cewa bayau ne zai dawo ba, sai zuwa jibi,
Kamar munafukai muka fito motar muna dan nonokewa ,
Duk da yagane nufin mu bai ce muna kowulakan ,
Salim ya kalla yace mai ya harama zuwa sallah kafin ata da jam,i,
Muna shiga gida har mun manta da zancen nafisa ashe ita tana nan tana ta hauka tun wucewar mu,
Akan dole sai an dauki mataki akan mu tunda munyi mata wulakan
Masifa take tayi yasa ginan gida jen su ba irin namu na Nigeria bane,
Balle wani yaji yadda take masifa ,saboda su ba halin su bane,
Ina dakina bayan mun idar da duk sallolin mu sai natashi ,ina cire kayan da sa ajikina ji kawai nayi ambankado min kofa da karfi
Najuyo don ganin kowaye yai min wanan irin shigar daki,
Allah yasa ban cire riga ba nadai cire dan kwali da su yan kunneya na,
Nafisace tsaye tana wani irin haki gyalenta a hannu ta rike shi don masifa,
Tana batun finciko ni taji anjata baya da karfi ko da ta waiga saitaga sheriff ne ,wanda dawo wanshi kenan daga masallaci , zai shigo yaga wulgawanta ,zuwa sashen mu,
Sanin halinta dayayi yasa shi biyo ta yaga ina zata,
Ganin da yayi dakina ta dosa yasa shi biyo ta har ciki, ganin yaje yeta yasa tafara
Ai ko sai tahaudura min ashar ,bakar Ashar,
Takara yo wa kaina gadan gadan, hakan yasa na boye bayan sheriff din wanda bakin ciki ya hashi yin ko yin magana
Ganin da yayi cewa bazata fita dakin ba shikuma mutum ne wanda baison fitina
Hannu na yaja zuwa waje, muka barta can dakin,
Aiko saita sa kuka wi wi, wai ya wulakanta ta saboda yar aiki,

Tundaga ranan sheriff ya hanani duk wani aiki da yashafe fan,nin nafisa tunda tace sai ta halakani,
Hakuri Shehi yaba shi so sai tare kara mai karfin gwaiwa, akan ya jure,
Wanan fitinar da NAFISA tayi yasa muka sake jiki ga fadan da muke tsan mani gurin she,

Koda yaushe Amal tana bani labarin Nigeria dakuma labarin yan makaran tar su da sukayi karatu tare,
Ina jin dadi wanan labari sosai ,
Idan tana bani sai in yi kwance in yi shiru ina saurare ta gama yanzu da banda wani aiki sosai a gida sai aikin ummi,
Can mukan zauna muyi ta hirar mu,
Har kusan lokacin shan ruwa sanan indan fito inyi aikina,
Aikin yanzu baida wani yawa kamar da iyakata kula da masu ayukan gidan,
Saikuma in dan zagaya inga abinda yadace ayi ma ma,aikata,

Azumi na Ashirin baba Shehi yai haramar komawa gida don sallah wurin sauran iyalin shi,
Shirye shiye sosai a,kayi mai ,
Ummi tatura mu munje munyi wa yan uwarta sayyaya sosai
Jin da nayi ance hjy tsohuwa guri guda take da su, baba shehi yasa naje nasiyo mata maganin ciwon kafa da kuma magani ciwon ido,
Naba baba shehi yakai mata cikon kayan da na hada naga Amal ta jefa wasika tace akaiwa hjy tsohuwa,
Ana gobe malam zai wuce nashiga dakin su inkai wa ummi fruit sald kafin ta kwanta
Sai na iske malam she da yaran shi Amal da Salim, yana basu wani dan abu suna lasawa,
Har na juya zan fita yace min yaki "yata sai na dawo nasamu gefe nadan tsuguna daidai saitin da Amal take yace min indawo
Ni abinda tabasu yadibo ya bani in lasa,
Na lasa yace min in miko mai hannuwa na na mika mai yakama hannu na dama ya murza min wani abu fari kamar takarda sai naga abin yashige min a jiki,
Inata juya hannu ko zan gashi banga abinba yabi lafiyan jiki,
Karshe yace min intashi in tafi Allah ya tsare masu mu mukace Ameen gabadayan mu,
Washegari malam shehi yawuce yabar mu da kewan shi sosai,
Dattijo mai dadin sha anni, dakuma fadin gaskiya,

Saura kwana biyar sallah da dare har na kwanta sheriff yace akirani a falo nasa may shi yace min gobe in shirya in raka Amal madina kuma ga goben zamu dawo,
Sanin da nayi tsakanin Makkah da madina akwai nisa sosai yasa nadaga kai na kalle shi sai yace inda bamu gama bada wuri zamu iya kwana har jibi in sun gama mudawo,
San mako mukayi tunda safe muka kana hanyar madina,
Amal ta dauka ai ba wani tafiya bane mai nisa sai taga har ana batun marance bamu isa ba, nan ta waigo inda nake ta kallon dogon dajin da ma,aiki manzon Allah SAW sukayi tafiya hijira saman rakumai daga makkah zuwa madina,
Gaskiya mu munzo cikin musulunci mai dadi dibafa a mota muke ta tafiya haka amma bamu kai ba,,,,,
Amal ce ke ce min fadima har yanzu nace mata saura kadan insha Allah,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
24/10/2017, 1:50:16 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣3⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP ND NASIBI GROUP🐎
🎁 *NASIBI WRITERS ASSOCIATION* 🎁
🎁N🎁W🎁A

Ku _yi Afuwa arayuwan ku
Kuyi sasauci ,arayuwa,ku
Ku yawaita murmushi da godiya ga dan uwan,
Sadaka na kariya sosai ga bawa ranan tsayuwa jiran hisabi,
Allah yasa mudace,

Yan huguma group ban taba mantawa da ku ban manta alherin ku gare ni,
Nagode Nagode Nagode

Almost true life story,,,

Gab da sallah la,asar muka shiga garin na madina garin da duk duniya babu inda takaita gaskiya da son jama,a garin mutanen kirki ga mutunci, garin da ba ruwan ko da sa ido ko hassada ga dan uwa,

Cikim larabci nai ma driver mu yusuf magana nace ya wuce damu direct mai kai gaisuwa mu kuma kwaso lada tunda
Mun makara nasan cewa baza su samu yin abinda yakawo su ba yau sai gobe,
Don haka goben ba,la,lai bane musa mu zuwa da wuri kafin mu wuce,
Saboda nasan cewa madina bakamar garin makkah bace gari da komai acikin natsuwa akeyin shi,
Al,umman garin madina daban suke da sauran mutanen garuruwan su maci kusa,
Karfe goma anrufe massalaci Annabin rahama ba,a bari kowa ya kwana acikin shi,
Bakamar masallacin makkah bane da wasu ma anan masaukin su yake,
Nan suke kwana suke komai,
Iyaka sai in anzo shara su dan kwashe kayan su su a,gyara wuri sai su dawi
A gaskiya koda banda wayo nasan cewa kasar saudiya kasa ce mai albarka da hakkuri da jama,a,
Duk yadda mutum yake suna hakkuri da shi indai har ibada kaje yi,
Ba irim mu takari masu zuwa da wani manufa ba na dan ban don tara dukiyar duniya,
Chapter 47 · 0% Book details