← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 139

Sashe 3

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Inna yar kulu zaune a dakinta cikin dare bayan ta idar da sallah dare kamar yadda tasaba, Tana kai kukanta ga Allah akan Allah yasa wanan tafiyan da za,ayi yazama mata alheri,
Allah kuma tsare mata yaranta aduk inda suka shiga.
Duk wanan addu,an da takeyi a cinkin zuciyar ta takeyin shi, ,,
Shin wai ma wazata tura wanan tafiyan cikin hafsat da fadima .
Duk iya tunanen ta takasa tantance wacce zata bari a,tafi da ita,,,,,,,,
Washegari karfe takwas na safe sai ga Gajiye acinkin shirinta na,tafiya,,, A,zuciyanta tana fadin ai,tunda malam sale ya yarda bazan kara kwana ko guda ba kada in,zo in samu matsalar tafiya,,, Don ita ga haukanta duk yaran biyu zata tafi dasu saboda samun banza.
Da sallama tashigo yar kulu ta, tare ta da mutunci, Saidai acan cikin zuciyar ta addu,atakeyi ,,,,,,
Bayan sun gaisa cikin gimama juna,,,,, Sai yar Gajiye tace tau ina fatan yaran sun shirya ko ?
Innna dake shirin mikewa ta dauko mata koko tadakata tace yaran kuma ,"eh mana inji Gajiye bada hafsat da fadima zamu ba ,,,,,,,, habadai Gajiye idan na,bakisu dukka nidawa zan zauna au baga Maryam da DATTIJO ba,,,,, a,a gaskiya hakan bazai yiba , ai,ko mutun gudan dazan baki kawai dai don kece an riga anzama daya
Duk da ran Gajiye ya baci amma sai tadake tanuna ai ba komai ko hakan ma ai, ta gode tunda an,yaba da ita har anbata,,,,,,,, Saidai acikin zuciyar ta fada takeyi,,,, yo ga matsiyaciya nizaki kulla ma tsiya inga samu inga rashi haba wanan wata irin shu,umar mace, ce
Muskudawa tayi tare da gyara zama dan taji dawa zata tafi,,,
Juyowa inna tayi daidai lokacin tai ajiyan zuciya gami da cewa,,,,,,, Ban riga na gama shawaran ko dawa zaki tafi ba tukun ,,,, au mutafi da hafsat ma tunda itace babba.
A,aa gaskiya hakan zaiyi wuya donkin ga itace maidan wayo daga cikin su. Kinga ko zaiyi wuya inbari tayi nisa dani . Duk da yake fadima itace kusan ke taimakawa hasfsat din, kinsan abu ga tallakka ai sai a hankali.
Acikin zuciyar gajiye tace duk kigama tsiyar ki sai naci riba dake,,,
Inna abu yasha mata kai tara wace zata tura birni,,,,,,,,Caraf fadima da ke da saurin wayo da fahinta tace inna nizani abar hafsat dasu maryam
Aiko inna taji dadin hakan don dama tana shakar zuwan hafsat, Saboda shiru shirunta yai yawa za,a iya cuta mata batare da ta dauki wani mataki ba.
Fadima duk da yarinyace amma ta gane cewa inna batason zuwar hafsat din don ko cikin dare , da ta, farka taji inna na,maganar ,,,,,,,
Duk zancen da inna tayi cikin dare fadima naji ,,, A ,hakanan ta kwanta zuciyar ta fam da tunane tana fadin,,,,, Kiyi hakkuri inna tunda kin riga kinyi alkawari ,, nayi alkawarin ni fadima nizanje koda kuwa zuwan nada illar kamar yadda zuciyar ki ke fada maki ,,,, kuma gashi kinyi alkawari baki son fasawa,,,, kada Gajiye taga rashin cika alkawarin ki.
Kuka inna tasaka tana fadin Allah yaimaki,albarka fadima ,,,saboda ta fahinci fadima tagane manufar ta.
Kiyi hakkuri zan maki addua ,,, Sanan kuma ina son jan hankalinki duk da nasan tarbiyan da nayi maku, amma dai inason kisan yanzu birni zaki ba kauye ba ,,,,Don Allah ki kula ki kauda kai ga abin duniya ba ruwanki da abin mutane kiyi abinda yakaiki watau zumunci ki kulada rayuwar kamar kina a gabana,,,Don Allah ki kiyaye ki kare mutuncin ki,,, Sannan nasan ki da rawan kai to ki rage don Allah,,,, Allah yayi maki albarka yakare minke daga duk wani abinki ya azurta min ku da ilimi mai amfani ,,, Zancigaba da yi maki adduan alheri har randa akadawo min dake ,, Allah ya kaiku lfy
Da kyar ta kai maganar ta da kuka a fuskanta.
Gajiye ta mike tsaye tana fadin haba yar kulu sai kace wani guri zata haka.,,,,, aiki kwatar da hankalinki fadima gida zata.
Hmmm Gajiye aikin san danyau saida fada ,,, tau hakane kuma
Gajiye tace ina kayanta akadauko wasu yan tsumakara da duk basufi huduba acikin wata tsohuwar leda bage baka aka bata
Kuka fadima keyi ta kankamay yan uwanta tana kuka kamar bazasu kara haduwa ba,,,Gajiye tace haba fadima ki yi hakkuri daina kuka ba wai dadewa zakiyi ba ai idan zan dawo tare zamu dawo, ba wai an rabu ne gaba daya ba . Wanan kuka haka ai sai yasaki ciwon kai.
Gurin inna takoma ta kara riketa tana fadin inna ki yafe min dan Allah ,,,, ita ma inna fadi takeyi cikin kuka baki man komai ba fadima Allah ya kai ku lfy.
A waje suka tarar da,su Ramatu da wasu yan uwan gajiye suna jiran fitowar su,
Haba shiru haka inji Ramatu ai mundauka kun fasa zuwa yaune,,,,
A,a ,a haba dai mun dai tsaya adan kintsa ne kinsan rabuwar da da mahaifi da wuya tun dai irin wanan da ba,a taba zuwa ko ina ba.
A haka suka samu motar da zata kaisu sokoto nan bakin hanya ,,, Ana daga masu hannnu fadima ma tana daga masu hannu tana kuka har saida ta daina ganin su,,,,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
[10/3, 16:34] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

Girmamawa Gareku masoyana👏👏,👏
ANTY Mariya SB
Hafsat yusuf
Safiya mai Huguna
Fatima Garba Teema luv
Maman Rufaida
Maman Ihsan
Anty Amal.
Nagode maku sosai,,,,

( FARKO )
Chapter 3 · 0% Book details