← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 139

Sashe 129

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
9⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,

Allah yakawo mu gida lafiya cikin dare muma shigarin makkah,
Mun samu maman Umar a gida tai muna taro na musan man,
Sai murna take yi daganin mun dawo tare da yar ta lafiya,
Ba karamin chanji nagani ba a gidan amma dayake nasan halin sheriff, da son abubuwan zamani dan shi bai jin zafin sayen abin rayuwa a gidan shi,
Sai dai may azuciya wani irin kallo nake wa gidan sai kace yau na fara zuwa ciki,
Ina tuna cewa a wanan gidan ne fa nasamu cikin da zankira da rabo,
Murmushi kawai nayi azuciya dan nasan ba,a wasa da ikon Allah,
Dakina na aini hi na shiga da niyar zama kasan cewa nasan cewa sama na Aziza ne da Sheriff,
Ina tsaye a tsakiyar dakin ina kallon yadda maman Umar ta gyara min shi, tas,
Sai naji an banko kofar dakin da karfi, cikin firgita nadan waiga dan gani kowa ye haka,
Sheriff ne nagani a tsaye yana min wani irin kallon mamaki ,
A hankali ya karaso har inda na ke, tsaye,,cikin fuskan mamaki yake ce min, sai bangaki adaki ba shiyasa daman nasa rai cewa kina nan,
To may kuma zaki anan din, don naga kayan ki nan,
Saida na kai zaune bakin gadona ina kokarin gyara, wani dan kit din yan kunen da na cire a kune na,
Nace cikin sanyi murya Sheriff ina zan kai kayan nawa to,
Ina ce nan ne dama dakina a gidan, ko,
Yar murmushi yace a da ke nan ko Fatima, yanzu kema kin san cewa kin wuce zama a kasa saida sama ko dan kici gaba da kula da Sheriff din ki kamar yadda kika saba ko,
Murmushi nayi nace aiko anan zan dinga kuka da shi fiye da tsamanin shi,
Wani irin laulausar murmushi ya sake , yace umurni na bayar bawai fa shawara nazo bayar wa ba,
Sai kawai yajuya da niyar barin dakin bayan shi na bi da kallo dai dai lokacin shi ma ya juyo gareni,
Yace min mariya ta dawo wanan dakin ita da Aisha su gwagwa su zauna dakin da Amal ta fita, dan nasan cewa baza su yarda araba masu daki ba,
Kai kawai na kada mai ina son ince mai idan Aziza tazo fa yaya zanyi zan kara barin dakin ne kamar yadda tai min a madina,
Kamar yasan tunane na sai yace ko kina ganin a halin yanzu akwai wata matar da zata zo nan tace ki bata daki har ki yarda ki bata kamar yadda kikayi a baya,
Murmushi nayi don tuno da wanan lokacin da yake magana, don ni kadai nasan irin kukan da nasha a wanan lokacin
Ga ciki ajikina ga tashin hankalin Aziza,da tasani agaba saboda hauka,
Murmushi nakara yi na Allah nagode ma da baka sa na biye ma aziza ba, muka dinga hauka alokacin,
Tashi nayi na nufi kofar daki dan in diba su gwago in masu bayanin inda zasu zauna
Suna tare da maman umar anata labarin abin da ya shafi cikin garin makkah da kewayenta,
A cikin larabci nai mata bayani nakuma bukace ta data kai su gwago su yi umurah zuwa gobe idan mun huta,
Tare da mariya muka hau sama don ganin dakin da aka umurceni in koma ciki,
Dakin na nan a gyare kamar kulun sai kamshi ke tashi cikin shi, tankar a kwai mutun adakin,
Wardrobe na fara zuwa na bude dan inga komay ke cikun shi,
Kayane ciki na mata birjit sababi fil a sheke ko ina dasu,
Gurin dressing mirrow na nufa abin mamaki kayan shafa ne irin na mata babune kawai babu agurin,
Mamakin yaushe akai wanan abin ya kamani sosai ,dan dai a,gaskiya abin yabani mamaki so sai,
Itako mariya sai santin dakin takeyi tana cewa kai anty fafima shine har kika iya barin nan kika gudo zuwa gida,
Cikin mamaki na kalleta nace lailai ma mariya da sauran ki,.
Anfada maki cewa akwai inda yakai gida dadina agurin duk wani dan halak,
Da taimakon ta muka sa komai inda yakamata daga cikin dan abin da mukazo da shi,
Su gwago duk mamaki da imani yakashe zukatan su,
Wai ace a wanan kasar nazo tundaga dogon daji yar karama da ni nai rayuwa a cikin ta batare da iyayyena ba,
Matan maigari mama tace gaskiya rashin sanin yanan kasar yasa har wasu yan sheri sukayi saurin zarga wa wanan yariyar sheri,
Gwago tace ni wallahi har kunya nake ji idan an tuna wanan maganar,
Saboda alokacin idona ya rufe sai nake ganin maganar su tumba itace gaskiya kamar yawon bariki ne kawai yariyar tazo yi,
Tabata muna sunan zuri,a don duk wanda zaiyi magana cewa zai yi ai iyalen gidan mu ne,
Amma tun wani rana da tazo gidan mu yini a hiran su da kawun ta nagane cewa tana da aure duk yadda akayi
Saboda duk bayanin ta acikin natsuwa taiwa malam shi,
Mama tace kedai bari agaskiya zato zunubi ne sosai wallahi,
Suna cikin wanan hiran sai ga sheriff yace ai sai su fito za akai su suyi umurah,
Don ba kyau mutum yazo garin makkah har ya kwana batare da yayi umurah ba indai har farkon zuwan mutum ne,
Fitar su gabada a lokaci guda yasa nagane cewa zaman su a tare da ni yana da matukar amfani,
Don ni kadai na dinga lalurar yaran kafin su dawo,
Gaba daya tun fitar su gidan ina sama tare da yaran , duk na rude na rasa yaya zan yi dawainiyar su ni kadai,
Azatona tare da sheriff suka tafi yin dawafin, ashe shi har yatafi yayi ko yadawo,
Dakin yashigo daure yake da bath robe, zaune ya samay ni ina kokarin sawa Abba permpers ga kuma ummi tana ta tsala ihu daga kwance,
Cikin sauri ya dauko yarinyar ya rungumay ta a jikin shi,
Sai kuma ya koma kallon wanda nake sawa permpers din shima ya fara kuka ,
Wata irin ajiyar zuciya yayi don har cikin ran shi na bashi tausayi don yar karama dani ya zanyi rainon yara biyu alokaci guda
Duk da kwazon da yasan ni da shi lokacin ina yarinya so sai,
A hankali yazo inda nake zaune rugumay da yaron a hannu na ya hada mu gaba daya ya rungumay,
Kuka na fashe da shi kawai, batare da ya bani hakkuri ba yana nan rike dani har nadan ba kaina hakkuri,
Yace min Fatima cikin murya mai rauni, baki godewa Allah bake nan ko,
Allah mai kyauta da kari shine yai maki wanan baiwar a lokaci guda,
Kina son ki nuna mai cewa baki gode bane ko kuwa,
Yadan kara mannani ajikin shi yace nasan ki da kwazo sosai na san cewa zaki iya wanan dawainiyar
Amma kuma nasan cewa a yanzu baki saba da wanan harkan ba yana daga cikin hikimar da nayi don zuwa da su gwago har zuwa lokacin da zaki dan saba da lalurar su,
Yakare zancen yana mai ce min kikara daurewa, ki kula da yaranki,
Kiyi kokari cewa duk wani bukatar mu nida yaran mu kin kokarta kin muna shi,
Idan kin muna haka, ki kingama muna kimai don mun zama yan gata agareki,
Jin kalaman shi yasa nadan murmusa, kamar banice mai kuka ba yanzu,
A hankali na ce baku da matsala daga yau insha Allah,
Yace to ki rikeni amana nida yarana pls,
Rugumay shi nayi nace in sha Allah zaka samay ni mai rikon ku amana,
Yadan mike ya lakuto min fuska yace to koke fa ,
A, hankali na ce nagode da wanan fadakarwan,
Yace ni dai zan gode maki nida kika yi wa wanan kyautar
Kin mayar min da gida na kamar yadda kowani magidan ci ke bukatar gidan shi ya koma,
Kin ingata min rayuwana kullun acikin godiyar ubangina, nake da ya zanto na mallake ki amatsayin mata ta uwar diyana abin alfaharina ako yau,she,
Dariya maganar shi tabani daidai lokacin na aje yaron dake a hannu na tafi daniyar in karbi yarinyar da tai barci a hannu mahaifinta,
Ji nayi kawai ya nemo bakina ya manne da nashi, wuri daya,
Can wata duniya muka tsinci kan mu cikinta, irin duniyar nan mai mantas da mutum inda yake,
Saida ya gaji dan kanshi ya sake ni ya juya da sauri yabar dakin namu,
Bayan shi nabi da kallo yana mai bani tausayi don hakkurin shi bai sa ka gane damuwar shi,
Chapter 129 · 0% Book details