← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 139

Sashe 43

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Almustaphane tare da bakon saurayin nan mai suna Salim suna dauke da kwandon abinci, da abinsha, a hannayen su,
Nina karbi basket din hannu almustapha, nakai inda zan aje na aje,,,
Ahankali nadawo inda nake tsaye, nadan tsaya muna kallon ledar ruwan da ake kara, wa Ummi,
Almustapha gefen da nake yazo ya tsaya gab dani, ,,,
Shima kallon ruwan da ake kara wa Ummin yake yi cikin tausayawa,
Dan juyowa yayi daidai saitina ya ce min Aisha na can yau tana fitina wai sai ankawo ta gurina,
Murmushi nayi nace mai tunda tazo aibantaba dadewa waje hakaba, batare dani ba
Yace yau kan Yumma tasha rigima sosai
Ina dan murmushi don tuna Aisha da irin rigimar ta,
Ina,dan juyo sai ko muka yi ido hudu da Sheriff din mu,
Dake tsaye daidai saitin inda muke,
Hannu shi cikin aljihu yadan jingina da gina kadan,
Ashe idon shi na inda muke muna magana da mustaphan
Wani irin harara Ya watsa min,
Tare da wani irin mugun kallo na zaki gane kuren ki,
,bansan lokacin da na sada kaina kasa ba,
Don kallon ya firgita ni sosai,
Tunda ni bansan abinda nayi mai ba, yai min wanan kallon na kishi ga hankalin ki, da ni,
Shiko Almustapha sai kara fada min yadda Aisha ke fitinar yakeyi,,,
Duk nadan daga kaina sai mun hada ido dashi daga inda yake tsaye suna magana da shehi,
Ganin da tayi mustaphan ba daina yimin kus,kus din da mukeyi zai yiba saboda bai lura da sheriff din ba da kallon da yake muna,
Don baya yaba ma sheriff din,,,,
Daurewa kawai nakeyi ina yar dariya kasa kasa,
Muryan , sherrif naji gab da mu yana ce min naje muci abinci da Amal a waje
Kafin in yi wani yunkurin tashi wurin saina ji muryan shehi yana cewa kamar ruwan baya tafiya ko,
Da sauri ya juya zuwa inda ummi take kwance don ganin robar kara ruwan
Sai kawai naji duk banjin dadi saina dan shiga halin damuwa,
Saboda ban iya fassara laifin da nayi ake min wanan kalon warning din,,
Abinda ya kawar minda damur dana dan shiga shine,
Farkawan da Ummi tayi daga barcin da takeyi sanadiyar dan taba mata hannu da akayi,
yasa nadan saki jikina da sauri na naje gurin ta ka,fin kowa ya isa ciki
Sauri ina mata sannu da jikinta, Ruwa tace zata sha saina dan daga kaina nakali inda yake ina fada ma sheriff din bukatar ta wanda dama idon shi naga mahaifiyar nashi,
Shima gurin gadon ya iso, yadan duka daidai saitin kan ta yace mata tayi hakkuri, Ruwa ake kara mata tabari indan ruwan ya kare sai abata, tasha ruwan shan,,,
Cikin sanyin gwiwa ya Mike ya na tafiya yana ce min cikin larabci koda ruwan yakare kada in bata ruwan tasha don akwai tests din da za,azo aimata dan anjima kadan,
Barcin ne yakara daukanta mai nauyi duk ina tsaye, akanta sai likitocine keta zuwa da dawo kanta, suna aune aune don su gane ko may ye matsalar ta
Amal tana gefe zaune ita da salim cikin damuwa ganin irin wahalar da mahaifiyar nasu keyi,,,
Muna nan zaune mukaji takon takalma tun daga nisa kwas kwas sai duk hankalin mu yakai ga kofar shigowar don gani ko waye,
A,she Nafisa ce tashigo asibitin da marance lip,,,, cikin shigar wando da riga irin na yan Pakistan, take,
Ta yafa mayafin kayan ta rufe kanta da shi,,,
Tana shigowa ko wani gaisuwar kirki bata yi wa koda shehi datagai dattijo ba cikin mu balle su Amal dake tsaye gefe
Direct wurin gadon da ummi take kwance ta nufa,
Tadan dibata tana tabe baki kamar mai jin wani, bashi ,bashi
Ta dan jin tsaye,muma ba wanda yako kulata,
Ko minti goma batayi ba da zuwa tace zata wuce,,,
Har takai kofa tajuyo tana min tabayar ina habibi cikin turan ci,,,
Da larabci nace mata yana can gurin ansan result din test din da akayi, wa ummi,
Yafuto ni tayi da hannu alamar in kai ta inda yake,
Ba musu na dan gyara na nufi hanyar zuwa lab, da ita,
Dan tafiya mukayi maidan nisa sanan muka isa gurin, da yake,
Zaune yake saman kujerun da aka tanadawa mutane,
Saidai kan shi yana duke, ba wai kalon jama,a yakeyi ba,
Dagani jira yakeyi yaji an kira shi, kawai,
Muryana da yaji cikin lokacin da bai yi tsamani ji, ba yasa shi dagawa da sauri,
Yana dagowa saida idon shi yabani tsoro
Saboda Idon shi yayi jajir kamar wanda yai kuka,
Nikan nasan cewa ma kukan yayi ,don ko dazu dana kai mai wani takarda da aka bamu na iske shi zaune cikin mota shidaya yana kuka,
Ganina dayayi yasa shi yadan wayance, don kada in san cewa kuka yakeyi,,
Tausayi yabani saboda mahaifiya ai ba wasa bace,
Don gani nima kusan kulun da tunane inna nake wace nake ganin kamar ban kara ganin ta a duniyar nan,
Gashi tunda naga makwabcin mu ban kara ganin wani dan garin mu ba,
Balle ma yanzu da ban bara ban talan gumama atiti kida alhazai sun zo balle inga idon sani,,,,

Yana dagowa kan shi yagan mu tare da nafisa aiko sai naga yakara tamke fuskan shi tam
Kamar wanda aka aiko mai da mugun labari,,,
Ita sam bata damu ba sai wani dan kokarin shige mai da take batun yi,,,
Nikan wucewa nayi don nakoma dakin da ummi ke kwance,
Don kada su bidi wani abu ban kusa,

Gida zamu koma don saboda asibiti majinyata basu kwana aciki,saidai mai jiya kawai da nurse's,
Saidai gaskiya shi shehi yace sam bazai koma ba zai tsaya asibitin, tare da ummi ne,,
Saida Sheriff yadan yi shige da fita aka bar shehin ya kwana, agurin nata,

Mu hudu ne a cikin motar a hanyar mu ta komawa gida
Sheriff ke jan motar duk da dare yayi sosai,amma baka gane wa saboda hasken da garin keda shi ko ina,
Zakaga duk hasken fitilo ne ya haske ko ina a garin jama,a kuma basu daukewa har galin Allah yawaye,
A hankali yake jan motar bakajin komai sai sanyin A C kawai dake ta aiki amotar , kirar Jeep baka, wulk,
Murya a raunane yadan juya gefen da salim yake ya na magana, dashi,,,
Yace, yanzu salim kun san cewa ummi batada lafiya kuka barta har ciwo yacita haka ba wanda ya kirani a waya, ya fada min,
Yanzu saboda Allah kunyi min adalci ke nan,
May ye amfanin samun da nayi a,duniya,
Har, da za,ace wai mahafiyata tana dauke da ciwon yunwa ulcer da hawan jini har yai mata mugun kamu, haka ban sani ba,
Amal ce ta katse mai maganar shi tace wlh yayan mu Kada kaga laifin mu
koda mun ce zamu fada ma sai ummi tace batayafe mu fada ma ba,
Wai kada mutayar ma da hankali, tunda kana iya kokarinka akan mu bai kamata mu dinga sama wasu wahala ba hakana,,
Wai zai zama kamar rokon ka muka yi ,
Salim ya karbe zancen da cewa ai ni koda yaushe nikan ce ma ummi sai na fada ma, tunda mutane zasu ga kamar cewa ka kasa kula da lalurar mu ne bawai daga ummin bane,,,
Ya ci gaba da fadin,,
Aiko wanan kiran da Shehi yai ma bada son ranta bane saida yaga ta rikice shine yadaga waya yakiraka,
Tsuki yayi yana mai kada kan shi cikin bacin rai,
,azuciyar shi kuma, yana tunane kawaici irin na mahaifiyar na,shi har yai yawa, watan ita dai haka Allah yai mata rayuwar ta cikin sanyin hali,
Hmmm Allah guda gari bambam ,,,,,Wai hausa ne sukeyi haka wanda sai da kyat nagane may suke cewa,
Get muka shiga ,muna paker motar mu mukafito,
batare da Amal ta tsaya ba tai niyar wucewa cikin gida abinta don duk a,gajiye take,
Niko lokacin na dauko basket din da aka kai muna abinci da rana ga flasks din ruwan tea da nake kokarin dauka wa cikin motar da hannu na guda,,,
Wani wawan tsawa ya,daka mata ta,tsaya wuri guda cak,
Tare da yi mata masifa, wanda ita dai duk iya saninta dashi baitaba yi mata hakan ba,,
Kayan dake hannu na yace mata ta tayani kwasa zuwa ciki,
Flasks din ta karba a hannu na ba shiri, jiki a sanyaye,
Shi kuma salim ya kwaso sauran kayan da muka kwaso daga asibitin,yashiga dasu,
Bin mu yayi da ido yana tausaya min irin wahalar da nasha yau,
Shin wai ita wanan yarinyar haka zuciyan ta yake ne,
Don dai gaskiya inbadon yasan ni tun ban karasa kai haka ba da sai yace kila don asani nakeyi wani abu,
Amma shi duk abinda zanyi sai yaga na tsakani da Allah ne babu kissa aciki,
Tsaki yaja lokacin da yake kokarin rufe motar,
Da ya tuna da Nafisa,
Wace ta nuna mai halin ko in kula, ga mahaifiyar shi,
Shi yarasa ita kowace irin mutunce mara tunane da lissafi,
Ace ankawo mahaifiyar shi asibiti daga Nigeria
Amma wai har ta biyo shi asibiti tana request din kudi a wurin shi,,,
Ita bata da aiki sai dai yawan tambayar shi kudi da bukata
Kuma sai yau yakara sanin halinta sosai don,ganin halin ko in kula da ta nuna mai akan ciwon mahaifiyar shi,,,
Da wanan tunanen ya shiga cikin gidan,,,,
Chapter 43 · 0% Book details