← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 139

Sashe 123

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban tsanmani arai na cewa hjy umma zata zo abuja ba saiga ta tare da yayan malam Abu driver ne yakawo,su, Hjy Umma mutumiyar kirki macen da tasan ciwon kanta ga kuma riko ga addini, Tazo ma yara da kayan sawa masu kyau da sai kuma ni da tazo wa da irin din yan Senegal din shaddace taci kwaliya har kasa, dogon riga, Da ga ita har yaranta sunyi mamakin ganin irin gidan da nake ciki a matsayin gidan mijina,. Dan sam basu zaci cewa arkin Sheriff yakai can ba murmushina yi masu dan nasan cewa basu san kowa ye sheriff ba, Da Allah zai kai su saudiya da sun tabbatar wa kan su ba sai na fada da bakina ba, Basu zauna suka fara gudanar da al,amarin buki, Awa daya tsakani Salimat ta iso tare da sisters din ta su uku, Nayi murna kwarai da zuwan su,Salimat, Don zuwan na,su ,yai muna amfani sosai, saboda sun hade da su hjy umma suna ta arranging din abinda za,aiwa baki, Sai zuwa dare Antyna Rugaiyya ta iso uwar gaiyyar aiki, Dan ko Rugaiyya ta nuna mi ita ita din ce a gareni, Tazo min da duk wani kayan snacks da ake yi a gurin buki tankar yadda al,adun mu na kasar sokoto yake, Duk wani abinda uwa ko ya zataiwa yar ta shi Rugaiyya ta hado min , Mota guda suka ciko da kayan gara, irin yadda ala,adar mu ta hausa take, Ban samu bakin da zan mata godiya ba don abin ya wuce lissafina, Sai zuwa dare sai ga mutanen dogon daji sun iso, mota biyu na mata guda na maza, Kawai sai naji aiduk na rude ban iya ai,watar da komai Salimat da Anty Rugaiyyane sukai kasafin guri sauke kowani bako yadda ya kamata, Maza yan dogon daji mun kai su boys Quarters, Mata kuma sai duk aka rabasu a sauran dakunar gidan, Nida Salimat da Safiya da sister ta muka koma dagin sheriff sai mukabar hjy umma da Rugaiyya da hafsi dakina, A gaskiya ban taba zaton haka ba sam a rayuta ashe jama,a dadi gare su, Duk yadda dangi na suke yan kauye a cikin mu sai naji kawai hankalina yafi karkata gare su, don komai su nake fara sa akawai, ko,aimasu, Ban bada wani kafan da za,araina min yan uwa ba sam, Sai cikin dare so,sai mutanen Maiduguri suka iso ,hurjanjan duk sun gaji, Sam bamu san da zuwan su ba alokacin sai dai ganin su mukayi, kawai, Da gudu Amal tazo ta rungumay ni cikin missing din juna muka dan dade a hakan, Can kuma sai naji ta ture ni baya kadan ta canza fuskanta , Cikin larabci ta fara zazagami ruwan bala,i akan gudun danayi na basu, Inda take ce min wai na guda batare da na fadawa Ummi matsalata ba kuma ma na raina da Ummi ne aida ban rainata ba da ban gudo na barsu a cikin tashin hankali ba, Shiru nayi kawai sai yar murmushin da nake mata, Suko yan uwan su da basu san ni ba sai kokarin zuwa sugan ni suke yi, Nan da nan falon ya kaure da larabci tsakanin Salimat da Amal da Anty Rugaiyya sai ni dake dan jefa masu baki Hjy umma tace wa safiya kin gani ko keda nacewa kitafi saudiya karatu kika ce min ke bazaki ba yai maki lokal, Tace yanzu dan Allah hakan bai baki sha,awa ba sai kawai duk mukasa dariya, Nan Amal tace ai karatun saudiya nada amfani so sai wlh musan mam ma ga matasan mu mata, don duk wani akidar alheri da ake so uwata samu har ta tarbiyartar da yaran ta dole tasamo shi a can koda ko batayi niyan koyon hakan ba Don al,adun su kawai zaisa mutun yaje koyi dasu har ya dauki halayyan su ya dinga yi, Ta ce ai rashin sani ne kesa iyayen tura ditan su karatu har kasa shen turawa bayan ga inda ya kamata iyayye sika yaran su don koyi da sunna ma,aiki SAW,,, Wata daga cikin yan maiduguri baidai yarinya bace kamar mu ta cabe zancen da cewa ai mu mun ga faidar hakan so sai ba sai an fada muna ba, Don ko mai wanan gidan da muka taru don shi abin musaline kawai, Dan yan uwan shi da aka fara turawa kasan turawa karatu akwai daga cikin su wanda har yau baiko leko kasan nan ba, Gudan ma da yazo wani lokaci da kitso fa yazo muna har kauyen mu dashi, shiko guda da baturiya yazo ganin gida sai kuma akidar sa wando a sabule shi ta baya wai duk cikin wayewa ne, Shiko Amadu don hassada akasa a lokacin wai akaishi karatu saudiya saboda wai basu da karfin ilimi kamar kasar turai, To kin san abin Allah sai gashi shi wanda Allah ya nufa ya take daga cikin su, Su yanzu suna can ba wanda yasan ma halin da suke a ciki, Garama da da Abba ke zuwa dibasu wani lokaci har yadan tsawata masu akace duk da uwar su na boye wa duniya sherin su, batasan cewa ba,a boye magana ba anzu, To yanzu ma Abba girma ya kamashi ba ko,ina yake zuwa ba,, Allah ya kyau,ta inji hjy umma takarasa zancen dashi tana fadin Allah yasa iyayye su gane su daina tura diyan su kasa shen da babu akidar addinin musulunci acikin ta Kowa ya ansa mata da Ameen, a lokaci guda saboda duk jikin mu yayi sanyi ga bayanin ta, dan sai a lokacin nadan fahinci cewa ashe hjy mama hassada takeyi da Sheriff , Shiyasa yan uwan shi basu kaunar ci gaban shi sam, Nace inko hakane gaskiya akwai aiki so sai nan gaba dan dai dole a sheriff's yasamu support dan kara mai karfin gwiwa, saboda yasa su aran shi, , Sai daga bayane nake jin cewa ita wanan matar mai magana diyar dan uwar Abbane, Kakansu guda da sheriff hjy tsohuwa itace ta haifi mahaifinta, Ke nan ba karami zumunci ke tsakanin su da shi ba don haka na sa araina cewa zan ja ta ajiki sosai , Saboda duk abinda mace zatayi ya kasance taja koda mutun guda ne daga cikin dagin mijinta ajiki so sai wanan zai sa yan uwan miji so so mutun kodan dole, Kamar yadda wa su baruwan su da dangin mazan su kan su kawai suka sani da yan uwan su, Duk yadda miji ke kyautata masu su basu damu da nashi yan uwan ba, Tundaga waban lokacin na dinga kafa,kafa da ita dan kusan duk abinda za,ayi sai ince akira hjy falmata, Hakan yasa ta tun ba,akai ko ina ba tafara yabona agaban yan uwan su , Washegari aka radawa yara suna a babban masallacin dake cikin maitama suna,tare da kwararo madu addu,a, Kusan duk wanda yazo sallah asuba aranan ya sheda wanan abin don sun koma gida dauke da gift da su malam Basiru da Bashir suka tsaya daga kofa suka bayar as a sadaka, Yara sunci sunan, hjy mama, da kuma Abba lawal zannah, Sheriff da kanshi yasa shehi yai masu huduba da wanan sunan Saboda hjy mamatasan cewa ita uwace a gurin shi ko yau she, Agida kan bukin suna akayi sosai kamar yadda mata ke taruwa yan uwa da abokan arziki ayi , Dagani har yaran kwaliya kawai muke ta dan dasawa wanda mai photo da kuma video ke tadaukar kowa gurin, Yan company din su dake nan Nigerian Mobile sun yi kokari sosai don sun shirya wata liyafa taban girma ga shugaban nasu, Wanda dama jama a bsdu sanshi ba sosai sai a wanan lokacin, aka waye shi tunda ba Nigeria yake shigowa ba sosai, Mariyata tayi mugun kyau cikin yan kwanaki kadan din da mukayi da barin kauye dan tare da safiya suka fita inda takai saloon akai masu gyara na musn man, Abdull kanin mu hafsi tazo da shi kayan yan kati na ma,a suka fita da salim yasaya mashi su kalakala masu kyau, dakudin shi, Nai magana akancewa zan bashi kudin yace min ina ruwa na ko nafishi son shi ne ? nai shiru naja bakina, Walima suka shirya wanda suka gaiyato mashuriyar malamar na mai ma mata wa,azi, watau malama Zuwaira, tare da wasu sairan malamai mata biyu, Da musalin karfe hudu na marance za,ai wanan walimar, Sai musalin karfe biyun rana lokacin ina cikin shigar wani material green colour ,mai tsada wanda tun a saudiya da nake da ciki salimat tasani muka siya don wanan ranan taba mijinta yazo dashi Nigeria adika min,a kano, Wasu matane sukayi sallama a falon su hudu daganin su kasan cewa kosassun matane don shigan su kawai yawadatar ga may ganin su, Ga wani kamshi duk ya kaure gidan, da suka shigo da shi kowace taci ta koshi, Duk wanda ke falon ba su san ko suwaye ba, Kasancewar mu duk muna sama, Hjy umma ce zaune tare da Rugaiyya suna fasalin abinci hatta anty falmata bata san su ba, Gurin zama hjy umma ta basu cikin mutunci tasa akawo masu abin tabawa , Cikin wani irin murya da sauti irin na yan duniya wata daga cikin su ta dakatar da wace umma ta turo dauko abincin, Text naji ya shigo min alokacin kamar kada indauki wayar sai dai na mika hannu na nadauka dan inga ko text mai amfani ne gareni, Salim ne dake waje zaune cikin taron mazan dake kofa ya hango shigowar su gidan alokacin da kyat ya iya sheda ta, ma, Abinda ya turo min shine ga, Aziza ta shigo maki gida sai ki san yadda zaku tare su, Gabana yai dam, cikin mamaki na furta afili na ce Azazi kuma by now, Da sauribkowa ya kalloni cikin mamaki dan jin abinda nace a bakina, Cikin kidima Salimat tace tana ina ? nace masu cikin murya mai rau,ni tana falon kasa wai, Amal tace barin fita kafin ta fara wa mutane iskanci, A,falo kuma su Aziza da hindu suna can sun fara yiwa mutane iskanci ko, Cikin ya tsunar fuska suke wa mutane magana,wai a kawo masu jarirai su gani dan dama su shi yakawo su ai, Amal daga step tana saukowa ta basu ansa tace Akan wani hujja za a,dauko maku, jarirai haka kawai kai tsaye, Aike kinfi kowa sanin cewa ina
Chapter 123 · 0% Book details