← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 139

Sashe 56

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ahakana mika dinga karatun ba kama hannun yaro,
Muna samun kula sosai ga sauran yan uwan mu dalibai don ganin da suke muna cikin shigar mutunci koyaushe,
Sannu sannu na fara fice a department din mu kowa yasan da ni,, koya malami yakoyar dani insha Allah zan hadace shi akaina,
Wanan kokarin yasa nadan fara fice sosai ga kawaye na,
Mun hadu da yan Nigeria can da dama , suma sunzo karatune kawai,
Akwai wata Salimat yar kano damukr yawan hadewa wurin karatun mu da ita,
Saidai ayadda na fahinta ita matar aure ce, don ba yarinya bace,
Dafarko salimat bata kulani amma ganin da tayi inada kwazo sosai yasa ta dan sake jiki dani,
Hakan yasamo asaline watarana da akai muna test bata zo ba sai na kokarta nai mata,
Kafin in mata saida nasha wuya aranan don da kyat nasamu information nata,
Bata shigo school ba sai bayan kwana biyu ,Ashe bata da lafiya newai kuma tarasa wanda zata aiko,
Abin mamaki saida akazo rabon test din sai taga ai har da ita kuma abu guda muka samu,
Ina can gefe ban ko kali gefen da take ba na,
Ina karatuna sai ganin ta nayi gaba ta dafa fan table din dake gabana tana mai yi min sallama,
Ahankali nadago kai na kalle ta ina mai ansa mata sallamata
Sai take ce min tazo ne taimin godiya don tasan cewa duk wanda ke wanan ajin na computer science ba wanda zai iya taimaka mata bayan ni,
Naso in boye mata cewa bani bace nai mata amma ina sai tace min,
Ba yauba ina lura dake kina da hakkuri da sanin yakamata,
Nimatar aure ce mijina ya hanani hulda dakowa don gudun gurbatar tarbiya,
Shiyasa kikaga ban kula kowa acinkin wanan department din na mu
Don gudun saba ma Kama train da tadauka kafin tazo, amma inyi hakkuri zatayi wa mijin ta bayani komai gamay dani
Tundaga wanan lokacin muka yi sabo da salimat sosai,
Inda nagane cewa ita kadai ke zaune a gidan ta, karatu yakawo ta madina ,
Mijin ta yana Nigeria da zama,,salimat tana da kishiya a Nigeria wace nake gani kamar yar kasuwa ce tana kano to Dubai,
Nafahinci hakane indan suna waya da mijin in ta tambaye shi yara da maman su sai yace ai ta tafi dubai. Koyace ai tadawo rana kaza,

Karatun da mukeyi bai hana mu yin ibadar mu ba, don kusan kulun muna zuwa sallah a haram , saidai ba kowani lokaci ba,
Amma sallar ranan jumma,a bata wuce mu sam,
Saboda itace ranan weekend muna zama tun safe har dare acan
Ranan alhamis mukan taya maman umar gyaran gida da sauran aiki gida da ya kamata
Idan mundawo wani lokaci mukan dan zauna da maman Umar mudanyi hira kokuma in koya ma su Umar da Aisha karatu,,,
Kusan watan mu guda a madina, Sheriff din mu yazo ziyar mu, tare da ummi da hajiyan mu,
Munji dadin wanan ziyar so sai don ji mukayi kamar mun kai shekara bamu gansuba,
Koda suka iso bani gida mun fita dani da Aisha, munje wurin gyaran kai ,
Wurin baida wani nisa da gidan mu sosai don haka da kafa muka tako dazamu dawo,
Waje nasamu sheriff shida,Almustapha, yana waya a,lokacin,
Tunda na bude gida zan shigo idon shi ke akaina, nima ganin da nai masu na bazata yasani mamaki,
Cikin fara,a na isa gurin su ina masu sannu da zuwa,
Kamar yadda yake ansa min a dakile yau din ma hakane,
Cikin zuciyar shi kuma sai mamaki yakeyi, may yarinyar ga ke ci haka tawai wanan girman cikin lokaci guda,
Anyako madai tana karatun kuwa kodai jin dadinta kawai takeyi abinta sai kuma wata zuciya tace mata a,a ina bayazatayi hakana ba don yasan ni da kokari sosai,
Balle ma yasancewa ina son karatu sosai arayuwa na,
Muryan mustapha ce takatse mai tunanen shi inda mustaphan ke ce min ina mukafito haka,
Nikuma ina washe bakin murnan ganin shi,nace mai ai,nafito can wurin gyaran kaine, nida Aishan
Azuciyar shi yace badai tsafta ba kan wanan yarinyar akawai kulada kai,
Ciko na shiga inda yabi bayana da kallo da sauri ya kauda kanshi don gudun yin sabo,
Saboda wani irin mugun girma yaga nayi mai lokaci guda, saida gaban shi yafadi,
Inashiga cikin gida, kuma nai arba da ummi da hajiyar mu zaune a falon mu,
Da dan ihu na, naRugumay su ina murna,na daidai lokacin shima sheriff ya shigo cikin gidan
Saida nagama murna na san nan natuna cewa, aiba abasu komai ba na dan motsa baki,
Da sauri na shiga na hado masu kayan sanyi a ture tare da dan fruit ,
Ummi tace aidama nace diyata bata gidan ne tunda naga ko ruwan sha ba,abamu ba balle,
Ina dariya ina tsiyaya mata a cup nace mata murnan ganin ku ne ya hanna ta baku ai,
Sheriff na zaune yayi kicin,kicin da fuskan shi,na iso da cup da lemon zan zuba mai,
Agaban shi na dan tsugun na gab dashi sai kamshin, turaren na da ke hawa mai kai,
Yana min wani irin kallon mamaki a fakaice,
Bayan nadan tsiyaya mai ne nadan dago kaina a hankali nace mai ga lemu na yasha
Hannu yadaga min kawai alarmar godiya,
Natashi a hannakali cikin tafiyar da ni ban masan cewa ina yin irinta ba, nabar gurinshi
wurin mustapha nanupa don shima in tsiyaya mai,
Ban karasa kawai wurin mustaphan ba naji karan cup din da na zuba ma sheriff lemo ya fadi,
Cikin sauri na aje cup da gwangwanin lemo agaban mustapha na juyo wurin sheriff da sauri,
Lemon ya zube a kasa har yadan taba mai rigan shi kadan,
Ruwan da ke gefe na bude nadan zuba mai daidai inda lemon yataba mai riga,
Cikin rudewa na cire gyalen da na yane fusaka na dashi na fara goge mai wurin,
Kaina da akai ma gyara sai kamshi ke tashi ya dan tsira ma ido
Yana kallon yadda gashina ya kwanta lub bakikirin da shi,
Ga kamshin mangashin dana turare na ya rude wurin ,,,
Idonshi yadan rintse kadan gabanshi nata faduwa,
Don shifa gani yake wanan kamar ba fadimar yar takarin da ya sani bace,
Saboda canzawan nawa yayi yawa cikin dan lokaci guda haka,
Idonshi yadan kara lumshewa yana mai dan maida nufashi, a hankaki ta yadda ba mai iya ganewa,
Cikin kidima naje da sauri nadauko moper na goge kasan , Sai faman yi mai sannu nakeyi,.
Saida na gama gogewa san nan hankalina yadawao daidai
Ko da na daga kai in kara yi mai sannu sai naga idon shi a lunshi sainadauka ko ranshi ne ya baci ,
Cikin sanyin murya nace mai dan Allah yayi hakkuri ba san zai zube mai ajiki ba ,,
Idon shi yabude wanda naga kwayar idon shi yai ma jajir ,saida naji tsoro,.
Hannu yadaga min alamari is ok,
Chapter 56 · 0% Book details