← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 139

Sashe 38

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina can dakina jiki ba kwari tunda anty na ta,tafi har na kwanta sai naji bana jin barci , duk da gajiyan dake jikina,
Don haka sau,kowa nayi daga kan gadon na zauna kasa,
Kanya gift din da aka bani na jawo ina fitar wa guda guda ina kalon su,
Duk kusan dogayen riguna ne har guda hudu nace a raina sai muraba nida Rugaiyya na
Sai kuma dikin shadda redmaid masu kya kusan guda uku suma nazabi guda nace biyu in bata tasa don tana son irin wanan kayan tun muna kano,,,
wani kwali da najawo waya ce mobile cellular mai shegen kyau, cikin kwalinta tare da tarkacen ta,,,
Aiko ina ganin wayan ban san lokacin da na ture komai na hau murna ba,
Koda banda wanda zan kira na dade ina sha,awar waya kodai photo na kalla kuma inyi game,
Jona ta nayi a wuta don ta samu caji,
Ganin wanan wayan yasa nakasa karasa kallon kayan da nakeyi,,
Nakoma saman gado na kwanta ina jiran wayan tayi caji,
Maganar da naji sheriff nayi da matar shi yafado min a rai na,
Allah sarki sheriff ai nice ka taimaka don ban manta irin taimakon da yaitamin can baya kafin ma inzo gidan shi,,,
Juyawa nakarayi ina Allah Allah gari yawaye in nuna ma Rugaiyya wayata,
Da haka barci barawo ya dauke ni,
Firgice natashi duk jikina yajike da zufa,
A c na kalla naga yana aiki, har nadan gyara kwanci sai mafarkin da nayi ya fado min a rai,
Gabana ne ya fadi dammmm,,,
Tiryan tiyar na fara tuna abinda nagani a mafalkin nawa,
Rugaiyya ce ke shiga cikin wani abu mai matakala kamar gidan sama tana murmushi tana min bye,bye,
Zubur na mike don wani zafi naji tundaga kafana har cikin kaina,
Bayi na fada nai wanka cikin daren nan nadauro al,wala nazu nayi nafila raka,a hudu,
Nan wurin na zauna har akai asuba
sam jikina bana jin dadin shi wlh,
Barci ya kara kwashe nan gurin da nai sallah asuba,,,
Wanan karon Aisha yar karama nagani ta kankamay ni ajikin ta,,, tana kuka,
Zubur natashi sai naga ashe har hasken rana yafito yau ban fita ba,
Cikin sauri nadan gyara jikina kodan make-up din danakan yi yau ban tsays yi ba,,,
Kitchen nanufa direct ina shiga sai naga yau mama mai abinci ce ita kadai tana aikin breakfasts taya ta nayi muna sauri don kada sheriff din mu yafito bamu gama aikin mu ba,,
Tun ina hakkuri har nakai ga magana nace ma mama yau babu wace tazo daga gidan hajiya wai ko lafiya
Ba,afi minti uku ba sai ga su sun shigo , daganin su suna cikin tashin hankali,
Ban kula sai cewa nayi aikin da muka sha jiya duk ya sa mu gajiya,
Nadauki kayan break din nafara kaiwa falo aiko na iske sheriff na saukowa daidai lokacin muka gaisa da shi sama,sama nakoma don in dauko sauran kayan
Abinda kune na yaji Sukaina na fadawa mama mai abinci yasani yanka wani irin ihu, daga inda nake,
Duk suka razana don basu san cewa har nadawo ba,
Yake jiki nayi nafadi ina ihu mai kunar zuciya,
Duk wanda ke gidan sauri take yi ya iso inda ihun nawa yafito,
Kusan ta,tare suka iso gurin,
Duk kan mu kuka muke yi har mama mai abinci,
Cikin tsawa Sheriff din ke tambayar mu abinda ya faru,
Sukaina ce tai karfin halin fada mai abinda yafaru da Rugaiyya jiya bayan tabar nan gida a hanyar ta na zuwa gida,,,
Shima ya shiga tashin hankali sosai wlh don baiji dadin ace ta sanadiyar shi hakan yafaru ba,
Inda na rakube jikin wani standing fridge ina kuka ya kalla,
Ya kau da kai don jin tausayi saboda ya tuna da labarin da Anty nawa taimai a madina lokacin da banda lafiya,
Nafisa duk da bata jin larabci tasan cewa wani abu munmuna ne yasamu Rugaiyyan,
Barin kitchen din yayi zuwa falo inda Nafisa itama ta rufa mai baya,
Da ya juyo ya ganta ya dakata, har ta iso yace mata, ke baki da tausayi ne abin kuka yasamay su , amatsayinki na mace yar uwan su baki tsayawa ki basu hakkuri,
Sai cewa tayi yo ni maizan masu tunda basa jin hausa basa jin turanci,
Ta kaici yakama shi yama rasa may zai ce mata, yaji sanyi,
Ga sautin kukana yana ji har inda yake tsaye, yana tayar mai da hankali,,,

Muryan mama mai abinci ne naji tana cewa inda za,aga cikin shugaban nin mu na takari ai masu magana wata kila akwai yadda za,ayi sufitar da ita,
Jin hakan yasa hajiya laila ta fado min a rai,
Batare da bata lokaci ba na koma daki na na shirya cikin bakaken kaya irin namu nadauko takalmana Tommy nasa nadan gyara fuskana kadan jakata nadauka,
Nafita cikin sauri taxi natare nace akaini Masfala, by pass,,,
Tafiyan minti kusan hamsi yakai mu maspalan naba mai taxi kudi
Gidan hjy laila na nufa kai tsaye nasa may ta tana shirin fita, wai zata SHARMANSOOR gidan wata aminiyar ta batada lafiya,
Kallo daya taimin tasan ba lafiya,
Cikin tashin hankali take tambayana may yafaru,
Ina kuka nafada mata abinda duk yafaru da Rugaiyyan
Itama hankalinta yatashi sosai wlh,
Tashi mukayi zuwa gidan wani Alhj Aliyu bandi shugaban matasa na wanan erea din
Bayan bayani da mukai mai ne ya nisa yafara fadin akwai kudi ko da zasu bi sugani ko za,aiya fitar dasu,
Nace ma hjy laila duk kudin namu na wurin Rugaiyya dashi ta wuce,
Kassh yace yawani dafe kan shi, yace ashe ba zancen bi kenan
Kusan wuri uku mukaje amma zancen shine akwai kudi,
Daga karshe dayake hjy laila bata iya cin amana ba sai tace min in kyale su mudawo gida,
Gidan ta muka koma tai ta min nasiha ta kwantar minda hankali,
Muna nan zaune kafin in tafi mukaji ana sallama da hjy laila mun dauka ma ko maganar Rugaiyya ce aka samu wani labari
Da saurin mu muka fito shugaban matasan takari na uguwar da mukafara zuwa wurin shine yazo,
Yan dan wani sosa kai yana gyara yar falmaran da ya aza saman nalabiyan,
Hajiya tace mai Alhj bandy lafiya dai ko sai yace a,a dama nazo inji cewa ita wanan din a ina take da zama,
Kai haji bandy walahi kafita idona,
Kaida keda mata uku a ina zaka sa wanan din
Haba hjy kada muyi haka dake fa tace mai har hiya da haka ma sai muyi,
Inajin haka na banka mai wata irin hara na wuce cikin gidan hajiya,
Ban wani dade ba nai sallama da hajiya laila mata mai mutunci da karan ci
Taimin alkawarin zata zo gidan hajiyan mu don jin bayanin may ake ciki.

Koda na isa gidan hajiyan mu a tsorace na samay su ita da umar da Aisha,
Suna gani na duk sukayo kaina suna kuka,
Tausayin su ne ya kamani har cikin raina tundai hajiya kuka takeyi kamar wace akaiwa mutuwa mai karfi,
Saida naga maran ce yayi nace zan koma gida saboda yanayin hanya,nai ma hjy alkawrin zandawo badadewa ba,,,,,,,,,
Ashe can gida kuma hankalisu duk ya tashi saboda rashin gani na da basuyi ba, din fita nayi batare da na fada ma kowa ba,
Ina shigowa gida nagan su hankali a tashe duk sunyi tsaye cirko cirko a wajen gidan
Fadawa nayi a jikin Yumma ina kuka mai kona zuciya cikin sauti mai ban tausayu
Dafani naji anyi a hankali nadan waiga sai naga sheriff din mu tsaye bayana handkerchief ya miko cikin dakiyar murya yace min kukan ya isa
A hankali nadan tsagaita kukan nawa, Almustapha yace ma abude masu yumma dakin ma,aikatn dake ta baya su zauna ciki kafin ansan abin yi,
Ina ji haka cikin kuka nace hjy da su Umar fa,
Wurin wa za abarsu,
Da Yumma suka tafi dashi hargidan namu sun samu har sun rufe gida ta kwan kwasa musu dakyat suga bude masu bayan muryan ta da sukaji
komi da muke bukata yumma ta ta dauko muna
bawani abinda zai iya nuna shedar cewa mun yi zama, agida koda anzo bincike,,
Sam bansan cewa anje dauko hajiya ba dasu umar,
Gani Aisha kawai nayi ta rugumay ni tabaya,
Wani irin dadi naji dana gansu tare da mu,
Ashe ko mungode Allah mun gode ma sheriff din mu,
Don cikin dare yan samay suka kawo muna farmaki don suna zaton cewa ba rugaiyya bace kawai a shiyan,
Koda suka shiga gidan namu ba kowa sai yan tarkacen mu na aiki,
Basu gane komai sukatafi don sun san cewa ko sun tanbayi mutanen uguwar ba su gane komai,

Tunda akasa su,a ajirgi kasar, Niger jirginya je ya sauke,
Dayake ita tana da kudi tab ga jikin ta sai bata samu matsala ba sosai,
Motar zuwa Nigeria ta shi ga sai kano,
Da wayon ta tabar gida don haka bata sha wani wahala ba wurin gane gidan su,,
Mahaifiyar ta na daka a soron gidan su taji sallama
Tana waigawa sai taga wata yar gayu kamar Rukaiya amma dai wanan din tana da haske
Zuwa tayi da gudu ta rugumay mahaifiyar nata tana fadin
Ashe da rabon zan kara ganin ku ,
Nan ,da nan gida yacika da jama,a yan zuwa gani bakuwar makka,.
Kamar yadda takari kan dawo aimasu rade radin sun je yawon duniya ne hakane yafaru ga Rukaiya
Zancen ya bazu dan kauyen nasu Rukaiya tadawo daga yawon takari da tabi wata hajiya mai kudi saudiya,
Tadawo bata da komai, sai hakorin makka da tasa a bakinta,
Ita dai komai batace ba don yanzu ba lokacin bayani bane,
Saida komai ya lafa bayan kwana biyu cikin dare ta zauna da yan uwanta tai masu bayanin irin rayuwan da tayi a makka,
Tabasu labarin abinda hajiya tai muna da kuma yadda ta baro mu can,,,
Chapter 38 · 0% Book details