← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 139

Sashe 33

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakin da aka tanadar min na gidan nashiga , don indan gyara jikina,
Ina shiga batare da bata, lokaci ba, don dama duk nayi futub da kura gashi kuma na jika kaya na sama,
Cire bakan rigan da nasa sama na yi
Nakoma dagani sai dan wandon jens dark blue, na mata wata yar karaman riga pink mai guntun hannu ke jikina,,
Sai ribon mai kalar baki dana dan daure kaina dashi,
Nasamu wuri gefen gadon dake dakin na dan baza bakar rigan nawa don yadan bushe kafin in wuce,,
zaune nake ina kokarin cire takalman da ke kafa na, ahankali ya turo kofan hannu shi rike da tawul fari,
Ban san lokacin da na mike tsaye ba ina wage wage ko zan dan samu abinda na rufa ma jikina, alokacin ba komai adakin don ban barin kayana agidan kamar yadda sauran ma,aikata keyi,
Towel din ya jefo min tunda ya gane nufi na ,,
Shiko aganin shi baiga wani abin da har zan boye ajikina ba ,
Yar ficir dani kamar mage,
Juyawa yayi yabar dakin cikin sauri,
Shi dai tausayi wanan yariyar ke bashi a,rayuwan shi don koda baiji tarihina ba yakan tausaya min duk lokacin da muka hadu,
A dakin ta yasame ta tana kara gyara kwaliyar da akai mata a wurin akafar
Cikin dan dakikan lokaci ya kalle gyaran kan nata ya kauda idonshi tamkar baigani ba,,
Tasowa tayi tana wani rangwada ita adole tayi kwaliya ma miji,,
Tana batun rungumay shi yace cikin dakiyar fuska maynene haka pls,
Bana son irin wanan shashancin pls,
Sha shanci fa kace ,kana ,a matsayin mijina zakace min sha,shanci,
Nifa Ahmad bangane may kake nufi ba dani yau kusan satina uku kenan agidan nan
Amma ba wani nuna cewa ni matar kace, balle ,,,
Bata karasa maganar ta ba daidai lokacin nai sallama dakin dauke da cup din ruwan shayi mai tururi ,
Dai lokacin kuma wani sabon ruwa yakara gwaucewa kamar da bakin kwarya,,,
Shayin na gabatar mata ,wanda nasamu gundun mawar harara,
Bisa tebur din dake dakin na aje mata nafito abina,,,,
Dakina nakoma don naga yau abin ba dama,
Wajen window dakin na zuge glass din nadan tsaya, ina kallon ruwan
Wata zuciya kuma tana tuna min hajiyan mu dasu Aisha da umar ko yaya suke yau cikin wanan yanayin,sanyin
Danagaji da kallon ruwan baidauke ba sai kawai na kara cire rigana na fada bisa gadon mai wani katon bargo da laushi, nace barina dan huta kafin ruwan yadauke in,tafi gida,,,,
Har gari yai duhu ruwa ake ta tsulawa bakama hannun yaro,
Niko kwance nayi barci mai nauyi ne yai awon gaba dani,
inata barci abina don jin dadin wanan yanayin danayi,
Nadunkule wuri daya na,hada hannaye da kafana wuri daya na nadae, kamar wata yar mage,,,,
Kusan sau biyu ya shigowa dakin don ya ta dani daga barci,
Amma yana samuna dunkule ina ta sharar barci na, daganin yanayin da nake barcin yai min dadi,
Yasan cewa ko kadan bani da lokacin hutu balle har na barci don hakane ma koda yaga magrib ya kusa daidai lokacin da aka hana barcin marance yayi ,,
Sai yai niyar zuwa yata dani, saboda bai yarda wani ya shigo mai cikin gida har inda nake
Don ni dakina ya ta ciki ne inda kusan inda nasu yake,
Sabanin nasu rugaiyya dake can ta baya kadan inda hanyar kitchen yake,
Sanin da yayi cewa ina gidan yasa shi, zuwa kirana don in, tashi ,,,
Ganin ina ta barcin ne har yanzu yasa shi juyawa ya koma, yata tausaya min cikin zuciyar shi,
Shidai baisan dalili ba kawai yarinyar tana bashi tausayi so sai wlh,,,,,

Arazane na mike akan gadon gami da salati , nazaune atsakiyan gadon kafana lankwashe cikin na juna,,
Nadan lunshe idona kadan don barcin bai sakeni ba,,,,
Azatona magaruba bai mayi ba tukun, yanayin dai garin ne haka, nadan kara lumshe idona daga zaune,
Idona yana rufen naji kamshin turaren shariff din wanda yakara dawo wa daniyar yatasheni daga barcin,,,
Jinkamshi yasani saurin bude idona saidai banyi sa,a ba yariga ya wuce ko tunda ya leko tagan ni a zaune,,,,.
Kallo nakaiwa agogon bangon dakin zubar na sauko kasa don ina gizo,,, idona ke min ba wai takwas saura nadare,,,, agogon ya nuna,
Bayi, nafada nadauro alwala na gabatar da sallah a gagauce,,,,
Ina idar wa natashi na nufi hanyar cikin gida don indiba abinda gidan keciki ,,,,,,
Don koni dan karen yunwa nake ji don harda kugi cikina keyi,
Ina tafe duk su hajiya nake tunane ko yaya suke can ko may zasu ci tunda ba girki takeyi ba,,,
A dining nasamay sherriff din zaune yana cin abincin shi daya,,,
Haka kawai ganin shi yasa kirjina bugawa don na tuna da fadan da yai muna dazu,
Yanzu gashi don jin dadi da samun,wuri na zo nayi kwance inata sharar baci kamar wace Abadan bata da aikin yi,,
Cikin girmamawa na gaishe shi,,,,
Amma maimakon ya ansa min sai dago wanan yadaurarren idanun nashi ya watso min, wanda kulun yakale ni dasu ban iya gane komai acikin su,
Shima tambayana yayi kinci abinci kine,
Batare dana bashi ansa ba
nace madan bata fito bane, sai kawai na nufi hanyar zuwa dakin ta, nashiga da sallamata,
Zaune take cikin wata yar rigar barci wanda yake dan iya nuna surar ta waje,
Dan damtsen hannuta yadan wani murde kamar na matashi kato,,,
Kanta duk da an gyara shi wai yau yawani yi tsirma tsirma dashi dayake guntun gashi gareta,
Waya takeyi, har na juya kamar in wuce sai na hago cup din dana kawo mata shayi dazu saina nufi inda yake indauko,
Jin maganar da tajeyi awayan yasani faduwan gaba duk na,riki ,
Saida nayu kokarin saita kaina, don kada tasan cewa ina jin hausa,, don ita duk dauka takeyi, banjin hausa ko dan turanci sai larabci kawai
Abinda naji tana fadi shiya tayar min da hankali sosai hankali,sosai
Cikin rashin damuwa da inajinta tacigaba da fadin,
Wlh duk da auren dukiya nai mai salwa yanzu ina son Ahmad,
Kafin in fara yaudarshi sai na dan more rayuwata dashi,
Hmmm zancan kawai hjy ke yi, kina tsan manin cewa zai ta bani kudine a haukace,
Ganin da tayi nadauki cup din kamar zan fita taimin alama da hannu cewa wai in dakata har ta gama wayan,,,
Cigaba tayi da maganar ta, Salwa don dai baki ganshi bane shiyasa kike cewa hakan
Yo nima dana fara ganin shi ai,saida na manta da plans din mu,
Takare karshen zance da cewa ai dole inbi a,hankali don in Daddy yagane plan din hjy duk mun mutu Salwa,,,
To sai kin kirani din,,, takashe wayan tana kallon inda nake tsaye
Niko alokacin duk nagama rudewa kokarin saita kana kawai nayi,,,
Yadda naga ta dan zuba min ido yasa nadan tsargu,
Saidai kuma naji tayi dan tsaki tace, waima ko taya zan ma wanan mara hausan magana fahince ni,,,,,,
A,lamatai min kawo mata abin sha jiki ba kwari nabar daki nata,,,
Hankalina a,tashe anya kuwa ba munafuntar Sheriff wanan matar keyi ba, au har ma shakukeyi inji wata zuciya tace min hakana keda yanzu kikaji komai ,
agaban ki fa akai maganar komai kina ji ba labari aka baki ba ji kijayi,,,
To inko hakane gaskiya akwai aiki ja agabana
Wurin wasu kujeru dake tsakiyan coredon gidan na isa na zauna gami da buga tagumi, don dai inji dadin tunane, don gaskiya dole in taimaka ma Sheriff nima saboda shima yataimaka min a rayuwat, lokaci da dama,
Minti goma tsakani na tashi na shiga dakin
Wanan karon bisa gado take kwance tayi daidai da ita saman gado da alama akai abinda take tunane,
Dakatawa na danyi na kare mata kallon tsab sai naji wani tsanar ta ya shiga zuciyana,
A sanyaye na karasa gareta na aje mata dan tiren da na hado mata abin shan sama wani dan stol .
Juya nafito dakin nabar mata cike da tsanar ta,a raina,
Tausayin Sheriff din naji ya kaman,,,
a gaskiya dole ne indan taimaka mashi batare da sanin saba,
Ajiyan zuciya nasaukar daidai lokacin da nagama tunane mafita,,,

Dole wanan ranan agidan muka kwana, saboda dare yayi ba damar mu fita waje,,,
Tunda safe dana tashi bayan mun kanmala komai,
Naje gun mama mai abinci na fada mata cewa, zanje gida indiba yaran nan biyu,
Batare da nafada makowa ba na gidan n sulale naitafiya na,

Motar shi yadauka don zai je yadan zagayo wurin aikin su dake cikin gari ,,,,
Har yadan fara tafiya sai ya lura da wani leda a,gefen kujera, daukowa yayi yadiba sai ya mayar inda yaga ledar, aje,
Har Saida yaje yadawo inda zashi ne yadauko ledan ya shiga dashi cikin gida,
Dakin shi yashiga da ledar ya aje, batare da yayi cigiyar mai ledar ba,
Falo yadawo don yadan huta, saidai yana zama sai yaga ai kamar yadda yabar falon dazu da safe haka yakara samun shi,,,
Wayan intercom yadauka yana son kirana
Yayi kira kusan sau uku amma ban,dauka
A fusace ya fito falon yana kokarin yaga ankira ni, saidai an fada mai fita zuwa gida amma nace bazan da de ba zan dawo, yan zun nan,,
Ranshi bace yakira almustapha yai mai kaca kaca kan sakaci da aikin da nakeyi,..

Agidan mu kuwa gaskiya nasamu hajiya ta kula da yaran don ta basu abinci kuma tai masu wanka,
Suna gani na suka yo kaina da murna suna nuna farin cikin su na gani na da,sukayi,,,,,,,,,
Jawo su nayi a jikina ina farin ciki da ganin su,
Saida muka gama yar hiran mu naje gurin hajiya muja gaisa na fada mata cewa ruwan samane ya hanamu dawo jiya,
Tace min ai,gara da muka tsaya can don da munce zamu biyo hanya za,a iya kama mu a,lokacin,
Nadan kai wani lokaci a gidan tare da hajiya da yaran inda na dan kara gyara wuri,
San nan mukayi sallama na koma cikin sauri don sai yanzu nafarga d lokacin da muke ciki,
Tabas nasan cewa na bata lokaci sosai a gida tare dasu hajiya,
Chapter 33 · 0% Book details