← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 139

Sashe 84

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Su biyu ne, zaune a bayan motar ita Hindu wacce ta dade rabon da tashigo kasar saudiya
Tafi zama can Dubai suyi harkokin su ,saboda can ne world businesses center,
A hankali hindu tai ajiyan zuciya tace kina kokari Aziza nasan cewa in ba don wanan habibin naki ba da babu abinda zaisa ki irin wanan tafiyar haka mai nisa,
Saida tadan yatsine baki kadan sannan tare bari kedai a,gaskiya koni wani lokaci ina yawan mamakin kaina,
Duk nabi na su,su ce akan wanan bawan Allah,
Idan wani yace min zan iya tsaya in bata lokacina ga wani da namiji irin haka, ada wlh zance karyane,
Hira ce sosai sukai tayi tsakanin su gamay da auren Ahmad da Aziza tayi,
Sai gab da sallah magrib suka iso madina daga birnin Riyadh,
Cikin farin ciki kowa ke taron su, ana masu sannu da zuwa,
A hankali na, sauko daga saman gadona da Amal ta ce min ai sun iso,
Na, dan gyara rolling din kai, rigar da nasa rashin sani yasa ni sashi don ban zaci cewa yana nuna cikin nawa ba,.
Saboda yadan matse ni kadan kasancewar yanzu duk wani sura nawa yafito ,
Irin yadda mai sabon shigar ciki kanyi kyau, tana,haske haka na koma,
Falon nashigo cikin natsuwa, nake tafiya, sallaman da nayi a falon shi ya maida hankalisu gare ni,
Duk kan su sunga baiyanar cikina adai,dai wanan lokacin,
Aziza tamike tsaye don mamaki ta tako har inda nake ta riko min hannu,
Sam takasa boye farincikin da take ciki, ta ma manta cewa abin siri ne,
Sai tafara dan ta,taba min jiki cikin mamaki, tana ce wa iye fadima wanan kyawo haka
Gaskiya abin yayi kyau sosai,
Shigowar Sheriff kenan cikin falon don shima yadade baya gida tunda safe yafita sai yanzu yadawo,
Amal da ke gefe tai wani dan guntun tsaki wanda yasa kowa ya kallota,
Sheriff shigowa dakin idon shi akaina ya sauka,
Sai kuma ya kula da irin rikon da Aziza tai min,
Cikin hikima naga ya dauke mata hankali don ta sake,
Juyawa tayi wurin shi babu ko kunyar UMMI da ke falon tawani kama sunbantarshi,
Ina ganin haka najuya don in koma dakina sai UMMI tace min
Fadima zo nan ki zauna mana karki koma daki ki kwanta ,
Badon naso zaman falon ba na koma kusa da ummi na zauna,
Saida komai yadan lafa ne, kowa na sa harkan gaban shi
Aziza tazo har dakina ita da Hindu, suna shigowa
Aziza da sauri ta karaso har inda nake, ta janyo ni zuwa jikinta ta rungume tace fadima,
Kingama min komai aruyuwana tunda kin sama min abin faricikina da kuma alfahari,
Kin gusar min da duk wani bakin ciki da tashin hankalin da dagin miji zasu iya kumsa min nan gaba ,,
Saikuma ta juya inda Hindu take tsaye tana fuskantar ta, tace,
Hindu Duk wani barazan nan da zai taso nan gaba ina mai tabbatar maki cewa zan iya jurewa intun kareshi ga ko waye,
Saboda abinda nake nema nasa mu ko,
Suka dan tafa gami dayin dan shewa,,
Ashe duk wanan zancen da Aziza keyi a idon sheriff din mune bata sani ba,,
Maganar ta doke har cikin ranshi,
Jiyayi kamar yai magana a wanan lokacin,
Saidai kawai yadake yace bari yaga iya gudun su tukun,
Ina tsaye daga inda nake idona ya ci,ciko da kwalla, mamaki su da kuma tausayin kaina ya kama,ni,
Lalai mutum ba kyau wallahi ji yadda Aziza taita lalashi na akan in taimaka mata amma tun yanzu har ta fara ikirarin cewa zata iya fuskantar kowa akan wanan case din,
Hmmm mutum,
Saida suka gama shewan su ta waigo taganshi tsaye, a kofar daki ya zubo mata ido,kawai, sai basar da ita ya nuna mata cewa baiji komai da take fadi ba,
Cikin halin ko in kula yake ce masu may kuka samu haka kukasa fadima a gaba kuna murna,
Sai taji kamar ta fada mai komai a wanan lokacin don duk abinda zaiyi ayita
Sai kuma ta tuna cewa ai a kasar saidiya suke,
Yanzu ana iya sa ajefe su ko a rataye su bari kawai idan ta koma ta sanar dashi ko da tawaye ne,
Yafi,mata alheri lokacin cikin ya kara girma sosai ta yadda baza,a iya zubar, wa ba,, idan har an gane plan din ta,
Chapter 84 · 0% Book details