← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 139

Sashe 17

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tundaga wanan lokacin muka samu kan mu cikin wani mawuyacin hali,,,
Bamu da komai na anfani Ali ya wawashe mu kaf ,yayi tafiyar shi abin shi,,,
Idan mutum yaje gurin aiki dan abincin da yaci sai mu rago ma hajiya mukawo mata,itama taci
Gashi yanzu ba lokacin azumi bane ko aikin hajji balle mu samu aikin yi,,,

Da, taimakon hjy Laila mutumiyar kirki muka dan samu dan abincin ci muka aje agida muna maneji dashi.

Tun wanan lokacin hajiyan mu ta dan fara ciwo kadan kadan gashi bata da kudin zuwa asibiti a auna ta,,,,,
San,nu sannu ciwo nata mata karfi ajikinta,,
Sai gashi harta kai wasu daga cikin mu yanzu basajin tsoron hajiya sam,,, sai abinda sukaga dama sukeyi kawai,,,
Tunda naga ciwon yana batun kada hajiya takaik kwance sosai ,,,,, batare da sanin antyna Rugaiyya ba na debi kudin mu da muke tarawa nakai hajiya asibiti,,, Aka auna ta akace tana dauke da cutar hawan jini,,,,

Nasayo mata magani da dan abincin da yadace muka dawo gida yinin ranar banje gurin aikina ba, inata hidima da hajiyan mu,,,,,,
Duk wanan abin da nake mata sai ido take bina dashi saboda bata da bakin magana amma ina ganin hawaye masu zafi na yawan fitowa a idonta,

Washe gari koda naje gurin aikina sai na iske ashe masu gidan suna gari tun jiya wai,,,
Ance idan nazo inzo in,karbi sauran kudin ranakun danayi aiki in wuce,,,,,,
Wani falo ne akace min in shiga ina jefa kafana wani sanyi da kamshi kamar kamfanin gidan turaren Al,Rahaf nashiga ,,,
Sanyin A,C da kuma TV bango suna ta aikin su,,,, acikin falon ,,, duk yadda zanyi lbrn falon ban iya fadin ,,abinda ke cikin shi duka,,,
Zaune may shi yake ya ba kofar baya ,amma kan shi na duke yana latsar laptop din dake gaban shi,,,, dagani hankalinshi na kan abinda yake browsing,,,
Duk karan da tv keyi ana ta wasan tseren rakumma sai ihu ke tashi,,,,
Nima da na shigo hankalina yana ga TV ina kallon wani dan yalalon balarabe yana kokarin wuce sauran samar rakumin shi,,,
Aiko bansan lokacin da nakama tafen hannu naba ina fadin yisauri yisauri,,,
Cikin sauri ya waigo tareda mike wa tsaye lokaci guda ido waje yana nuna ni,,,
Niko a lokacin ina kokarin kara tafa hannu na saboda murnan star dina zai ci,,,
Hannu da ban tafa ba kenan ,, Saboda gani Ahamad tsaye agabana wanda ayanzu duk inda naganshi zan iya she,dashi,,,,
Nakama ja baya a,hankali a,hankali har kusa kai karshen kofan cikin tsawa yace min may yakawo gidan shi,,,
Gidan shi na nuna gidan da yatsa nace la,la,la ainan gidan aikina ne ni,,,
Al,mustapha Al,mustapha ,,,, cikin sauri may shi yashigo falon mai kama da fadar wata masarauta,,,,
Ni Ahamad yanuna ma mai sunan Al,mustapha,,
Yanatanbayar shi may kawo ni gidan shi har aka bani pass na shigo mai falo,,,
Yace mai ai nice wacce ke kula da tsuntsayen gida da banzo aikiba jiya
Yakara nuna ni yace ita wanan din
Hannu ya nuna min alamar inbar falon,,,
gudu gudu na fita cikin falon sim,sim dani.

Ina zaune in jiran aban kudi na in wuce sai naga Ahamad yafito cikin shiga ta matasan larabawan zamani ,,,, Sai, kam,shi ke tashi,,,ya zo ya wuce tagaba,na batare da ko ya kalli da nake ba
Wurin harabar aje motocin gidan ya nufi wata mai kama da kifi kusan ko yaushe nazo gidan nakan ta kallon motocin ,,,,saboda suna burgeni,
Kamar walkiya ya harba motar shi yabar haraban gidan ,, nabi shi da ido kawai ,,,,,ina fadi a,cikin zuciyata dama nice awanan motar
Naji ace min intashi incigaba da aikina anfasa sallamata,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 08:20] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
2⃣9⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Duk wanda baiji tsoron Allah ba to tabbas zai ji tsoron abinda Allah ya halitta,,,,,
Allah bamu ikon bauta mashi da tsarkaken zuciya,,,,,,

Ina godiya gadukkan masoyana na Allah barmu tare cikin mutunci da kaunar junan mu,,,

Almost true life story,,,,,,

Nishi takeyi guda guda daga kwance ,,, yayin da kowar mu ke sauri fita zuwa wurin aikin shi,,,
Har na shirya zan fita sai na tuna cewa hajiya bata karya ba tun jiya ina ganin bataci komai ba,,,
Dole na kwabe rolling dina nacire bakaken kayan da na sa,a,saman na zauna dagani sai wani dan wando jeans sky colour da riga fara,mai dan hannu iya gwiwar hannu.
Wanka na fara yi mata sai kuma na gyara gurin kwanciyar ta dafa mata abinci mara nauyi ,,,

Nidake fita da shidda na safe sai gani yau har kusan goma na safe ,,, koda na iso na samu an min duk aikina ,,,
Al,mustapha yace may yasa yanzu nake makara ne,,, nafada mai ummi na ce bata da lfy ,,, ina dan kula da ita ne kafin inzo amma zan gyara,,,,
Tunda naga cewa zan samu matsala a wurin aikina sai nake tashi tun karfe hudu na asuba in yi duk wani abinda ya dace ,,, saboda gudun makara,
Tun lokacin ban kara ganin Ahamad ba ,,, koda yake ma ko tazo ba sani zamuyi ba tunda ina can gurin abokan hirana tsuntsaye yini nakeyi ina masu watsin abinci,,,

Yau ko da nadawo gida na samu Rugaiyya ta dawo take fada min cewa gidan da take aiki sundawo daga tafiyar da sukayi,,,,
Nan muka hadu tare da ita muka gyara hajiyan mu ,, nadan fito da ita kofar gidan mu don ta dan kara warware wa,,,
Da alamar taji dadin hakan don yau harda yar hira munyi da ita,, awajen
Matsala guda ce take min complain kafarta takeji yana mata nauyi sosai,,,
Tundaga rana nake dan yawatawa da ita acikin uguwar mu duk da yake saman dutse muke,,,

Kofar kitchen din su yake kallo daga bakin kofar shiga falon su,,, duk wani motsi da takeyi idon shi na a,kanta wanan abin ya fara isan ta gaskiya ibadon wanan aikin yazama kamar na dole ba da tabar masu gidan su,,,
Duk lokacin da maigidan yake a gida matsalar da take fuskanta kenan ,,
Idan sun hada ido wani lokaci har lasan lebon shi yakeyi kamar maye,,,
Azuciyar ta tace ka boye matar ka ko kuda baya ganin ta amma ni ka hanani shakat da wanan mugun kallon

Cikin dare suna kwance da matar shi tace mashi maigida nasan duk halin da kake ciki da yar aikin mu ,,, babu matsala zan kawo maka ita har nan gidan tadawo da ,kai na,,,, ni nasan kufi sha,awan wa,"yan nan matan fiye da mu matan ku,,,

Tundaga wanan ranan matar ta fara rarashin anty na Rugaiyya tana wani haba haba da ita,
Abinci lafiyaye ake bata tana ci sai kuma sutura masu dan kyau da aka sayo mata,

Tundaga ranan da aka sai mata wa,yan nakayan sawar masu kyau antyna tafara shiga damuwa saboda tana yawan tsorata da mugun kallon da maigidan ke mata yana shafar gemay shi yana lunshe ido,,,,,
Tundaga ranan tadawo gida cikin damuwa,,, tana shigowa ta jefo min ledar kayan da aka sai mata ajiki tana kokarin cire yar bakar rigar da muke sawa sama,,, Don wanan kowa yasan al,adan larabawa ne, bayan sungama kwaliyan ciki dole akwai bakar riga da hijjab ko gyale da zaka rufe fuskan ka dashi takalmi kuma mun fi sa flat cover,,,,
To muma TAKARI ,, haka mu tamu shigar saidai lokacin umurah da aikin hajji wasu sukan dan yi dressing din kasar su,,,,
Ledar nabida kallo ina fadin may ke cikin wanan ledar yar uwa, nakai dibana zuwa gareta don jin ansa,, yo kibude mana ki gani,, kayane masu kyau dogayen riguna da yan kayan unders aciki rigunan kala hudune,,,
Daga ina daga uwar daki na matar hamza Abdallah,,
Nakalla nakara juya kayan nace gaskiya suna da kyau, halan sun samu wani alheri ne haka,, ta waigo tadan debeni dadai lokacin tana cire kayan kan,ta,,, azuciyar ta, tace ansa may zan baki maryam da sauranki nasan bazaki fahince ni ba,,,
Kawai sai ta wuce dakin hajiya don ta gaida ita,,,,
Tanunawa hajiya kayan ,takuma bata dan abin sa ma bakin da tazo mata dashi,,,
Dakin nashigo na zauna gefen gadon hajiya nace mata,,,,,
Gaskiya hajiya yakamata ki fara fita hakana koda Haram ne ki dan dinga zuwa kina dawafi , zaifi maki wanan zaman , agida kulun .
Zama wuri guda zai ta kara maki bakin cikine arayuwar don babu ranar da wanan damur zata barki in bakibar tuna wa ba,,,,
Rugaiyya tace ai na fada mata ba yau ba saboda naga tadan ji saukin jikin nata ai
Saida hajiya ta gyara zaman ta kadan tace insha Allah zan gwada zuwa ,,, kuma nagode maku sosai da kulawar da kuke bani ,,,, ayadda na dinga cuta maku amma sam baku gujeni,,, sai ma kara shigata jiki da ku,keyi,,,,
Amma sai gashi Sukaina da mari sun fi karfina don suna ganin banda komai yanzu,,,,
Takare maganar ta ta tana share kwalla,
Dama tunda bata da lafiya nadawo dakinta da kwana saboda dare,,,
Chapter 17 · 0% Book details