← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 139

Sashe 8

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan dogon jawabin mai gari yayi ,,,,, Sai duk jikin Gajiye yai sanyi.
Gaba daya an daureta da jijiyoyin jikin ta,,,,, Ko magana ta kasa yi sai gyara zama take yi.
Duk da sanyi da a,keyi ita zufa take yi kawai. Kafin mai gari yayi bayanin shi sai tace,,, A gaskiya mai gari nasan na cuci yar kulu,
Nai mata wayo na dauki yar diyar ta da sunan zuwa ganin gida wurina.
Gaskiyan al,amarin dai shine nakai yariyar kano wurin aiki ne ba wai sayar da ita nayi ba.
Wurin wata amiyata na,kaita ai,katau, a kano.
Kuma gaskiya anbani kudin aikinta na shekara na,cinye saboda hakane ma yasa ban dawo gida ba don gudun kada mu hadu da yar kulu .
Ta nakai nan duk sai wurin yadauki salati,,,,,,
Wasu ,suna tama Gajiye tir da Allah waddai da halin kwadai irin nata.
Saida mai gari yayi da gaske yasamu wurin yai shiru,,,,,,,,,
Aka natsu maigari yace ko Gajiye zata kai su malam sale da wasu mutum biyu inda Fadima take su dauko ta tace "eh zatakai su insha Allah
Saida gaskiya bata da kudin da zata biya hajiya mai,sharwali,
Maigari yace kada ta da,mu, shi,zai biya hajiya kudinta,,,,
Aka shirya yadda tafiyan zai kasance idan an,tashi.
Daga karshe Gajiye ta roki gafara inna yar kulu tana hawaye, tana rokon gafara,,,,,

Maigari ya hada masu tafiya zuwa kano wajen dauko fadima,,,
Tun karfe shidda na safe suka bar garin dogon daji zuwa kano,,,,,,,
Sun isa kano da karfe biyun rana ,,,,, saida sukaje sukaci abinci tukun kafin su wuce shagon hajiya,,,,,,
Koda sukaje shagon hajiya sai Gajiye taga wurin duk ya canza mata ,,,
Ta,isa wurin wata mace fara kakaura da tagani tana gyara wuta tai mata sallama
Matar ta ansa mata cikin hausanta da ala,mar harshen yare,,,,
Bayan sun , gaisa da matar, take tambayar hajiya mai,sharwali, mai wanan shagon
Sai matar tace gaskiya bata santa ba ma don ita sayen shagon tayi wurin dillalai,.
Aiko Gajiye ta daura hannu akai tafara kurma ihu tana fadin ta shiga uku ita Gajiye haihuwar mutum biyu ,,,,,
Ina mai sharwali ta, tafi da diyar mutane,,, ita dai wanan matar tace wlh bata sani ba don ita daga lagos tazo kano ta sai shago ita yar ghanace,,,,,
Gajiye sai ihu take kurmawa mutane nata kallonta ,,,,,,, a, haka mutane suka taru aka zagaye su don jin ba,asi.

Wakilin sarki yace aidama munsan karya kikeyi mutumiyar banza kawai kinzo ki sayar da yarinya kin gudu ki ce wai anan kika kawo ta,,,, Gajiye sai sharban kuka takeyi tana bidan agaji

Ana cikin haka saiga wani dan tsoho yazo yatambayi ba,asin abin da yafaru akagayamai komai yai shiru nawani dan lokaci.

Can yace gaskiya indai matar da yasani ne tana saida abinci a wanan shagon tasai da shago ta wuce saudiya dayaranta duka.
Yau kusan kwana uku ke,nan da tafiyanta. Kuma shago da gidan ta dashi akayi ciki su duk ta sayar tabar kasan,,,,,,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:11] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣5⃣
BY
🐎ZAINAB IDIRS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Hafsat Yusuf
MSS ILLYAS
Nerbilar
Mariya SB
Fatima Garba
Ina maku godiyan kulawa da ni da kuke na gode fatan alheri gare ku ko yaushe,,,,,,,,,

Almost true life story

(Labarin Fadima Takari)

Mun isa filin jirgin jidda lfy , muka bi layin bincike akai muna screening na shiga kasar da niyar zamu yi sati biyu muna ibada,,,,,,
Muna fitowa wajen sai, ga hajiya zinaro tare da wani bakin mutum sun zo daukar .
Tun a mota aka fara hiran harka zai yi kyau tunda babu wanda yasamu matsala daga cikin mu,,,,,,

Wani gida aka kai mu mukan sai kallo mukeyi munga larabawa da kuma yanayjn kasar tasu
Mundan zauna baifi minti goma ba aka dan bamu abinci bawai don mun koshi ba,,,,,, Rugaiyya ce tace min in,tashi muyi ramuwar sallah da bamuyi ba,,,,,

Muna cikin sallah sai ga hajiya Zinaro da wani sun shigo suna fadi, oya oya kowa takawo bizan ta za,a aje mata kafin mu koma don kada ya bace a hannu mu,
Jiki na rawa muka mika ma hajiya zinaro,,, sai kawai ta dawo ta gaban mu tace,,,,,
Ina son kowa ya saurare ni da kyau, tanu muna biza din tace kunga wanan , mukace eh tace to idan ba dashi ba bu batun komawa gida Nigeria sam,,,,
Saboda haka mun karbe na kowa cen ku ne sai kowan ku ya kawo muna kudin da muka biya masa aka hada wanan biza din kuma ya ba da ribi a sama,,,,,
Sanan zamu ba mutum abinshi ya koma gida ,,,,,,

Wani irin ihu naji Yumma tayi cikin kuka tana fadin don Allah hajiya kuyi hakuri ku maida mu gida don Allah kada ku bar mu anan
Ke rupe muna baki kinji inji katon mutumin da suke tare da Zinaro yace ma Yumma,,,,,,
Sauran ma kuka naga suna yi nidai ina tsaye ina kallon su ido wuri, wuri dani

Daga nan aka kwashe mu lokacin dare ya fara zuwa wani wuri madan nisa saman wani dutse gidan yake dan karami daganin ginan kasan na da ne,,,, kuma na tallakawa ne ,,,, muna fita motan hajiya Zinaro ta karbi kayan su goron da muka zo da shi tace ma hajiya sai ta dawo zataji yadda za,ayi,,,,,,,,,

Tunda hajiya Zinaro ta aje mu bata leko mu ba , ga yunwa ga matsi ya ishe mu,,,,,,
Hajiyan mu ta dan shiga damuwa rashin ganin dawo wan Zinaro,
Wacce ta tafi da dan kudin da hajiya ta kulla zamu je mu ja jari da shi,,,,
Wata makwabciyar gidan da muke Laila yar katsina itace ta dan tai maka muna da abin da zamu ci,,,,,,
Data,ga la,lai zinaro ba zata dawo ba kuma da alama ta yaudari hajiyan mu ne,,,,,, Sai hajiya Lai,la bata nuna ma hajiya ai yaudaran ta akayi ba sai ta ba hajiya shawaran mai zai hana mu fara bidan kudi tunda muna da yawa ,,,,,,,
Shawaran matar hajiyan mu ta dauka,,, mata ita taima hajiya hanyoyi kakala don mu fara sana,a a jidda,,,,,

Aiki aka samo muna a gida jen larabawa don mu samu abin kula da kan mu,,,,
Gidan wasu turawa nasamu aka kaini inda zan dinga kula ma matar da yaron ta na goye gaskiya na ji dadin aiki a gidan saboda da turanci muke magana
Ita kuma antyna Rugaiyya goge goge a ka samo mata a wani ma,aikata,,,,, saidai Hajiya Laila tace aikin ba mai dadewa bane zamu bari mu koma Riyahd ne,,, saboda can anfi samun kudi,,,,,

Uwar dakina Rita ba laifi gaskiya iyakata daukan yaro in,dan mashi wasa sai ku ma da dare indan nane dinshi ta tafi gida ne nake aikin
Amma ina samun kulawa sosai daga wurin Ritan,,,,,
Ina yarinta sosai alokacin don haka ban damu da komai na duniya ba,,,,,
A lokacin da zamu fara aiki an muna huduba cewa ba ga albashi kawai zamu dogara ba,,,, zamu dan rika hadawa da , dabara samun kudi bawai muce sai abinda aka bamu ba,,,,,

Yan uwana kowa na na,shi aikin daidai sun fara sabawa da aikin bidan kudi,,,,
Ranan lahadi da mutanen gidan mu zasu je wurin ibadan su sai suka sauke ni gida wurin hajiya kafin su dawo,,,,
Nasamu hajiyan mu bata jin dadin jikinta dan abinda aka bani in kawo mata ,,,,,,,, Da kyat ta iya dagawa donta gani ko may ye acikin katon ledar da nashigo dashi,,,,
Duk hajiya sai naga tabani tausayi sosai ,,, amai tafara yi can kuma sai gudawa,,,,,
Nakama ta na kaita ban daki na gyara mata jiki,,, tea mai kauri na hada mata daga cikin kayan tea da aka bani inzo dashi daga gidan aikina,,,
Hajiya bata dade da kwantawa ba sai barci yadauke ta,,,
Natashi nadan gyara mata dan tsukaken dakin namu,,,, daidai naga ma gyara Rugaiyya tadawo daga wurin aikinta,,,
Munyi murnan ganin junan mu sosai da Rugaiyya ta rungumay ni tana hawaye,,,
Sai nasa hannu na nashare mata nace kai anty kibar kuka mana ,,, tace Fadima aidole inyi kuka tunda bansan ranan da zamu bar wanan kasar zuwa gida ba,,, nace mata ai babu komai
Mundan jima muna hira tana tanbayana lbr inda nake aiki daku ma yadda nake zama dasu,,,,,
Tace fadima don Allah duk ritsi kada ki yarda ki zubar da mutum cinki na diya mace,,,,,, ki kama darajan kanki don Allah
har zuwa lokacin da Allah zai kawo muna mafita nace to,,,,,
Iyayen gida na suka dawo suka,zo suka daukeni muka koma gida,,,

Kamar yadda akace aikin wata biyu zuwa uku zamuyi haka din ne kuwa
Saidai ni abin yayi min daidai don dai uwayen dakina ma sungama contract din su zasu koma garin su,,,,
Kayan afani masu yawa nasamu wurin su
Nakawo ma hajiya ta sayar muka hada yan kudin mu muka kulla sai birnin Riyadh,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/3, 19:15] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
1⃣6⃣
BY

🐎ZAINAB IDIRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Muna godiya ga ubangijib mu sarki Allah da ya nuna muna wanan lokaci mai albarka , Allah ya bamu damana mai albarka ,,,,,,,,
Jinjina gareku yan huguma group , musan man Anty hasfsat yusuf da anty mariya sb sai mai group din safiya Abdullahi huguma ,,,

Almost true life story,,,,,,,

GARIN RIYADH
Chapter 8 · 0% Book details